Dalilai huɗu da suka sa tattaunawar Iran da Amurka ke cikin ƙila-wa-ƙala
Asalin hoton, AFP via Getty Images
Makomar tattaunawar Iran da Amurka ta shiga cikin rashin tabbas yayin da lokacin da aka kebe na tsagaita wuta ke daf daƙkarewa. Abin da ya sa ake gani a yanzu ba wai rashin cimma matsayar diflomasiyya ba ce kaɗai, har ma da kalamai masu zafi da tsauri tsakanin ɓangarori, barazana da kuma bayanai masu cin karo da juna daga dukkan ɓangarori.
A cewar rahotanni da dama, babu tabbas cewa Iran za ta shiga tattaunawar da aka tsara za a yi wanda Pakistan ke shiga tsakani. Yayin da wasu majiyoyi ke bayyana cewa Iran na duba yiwuwar shiga tattaunawa, wasu kuwa sun ce ƙasar za ta iya janye wa watakila saboda yanayin da ake ciki.
A ɗaya gefe, lamarin yana ci gaba da zama mai tsarkakiya bayan da rahotanni suka ce mataimakin shugaban Amurka wanda ke jagorantar tawagar tattaunawar, JD Vance, bai ma je Pakistan ba watakila saboda rashin tabbas da ake da shi kan tattaunawar.
A nan, tattaunawar za ta iya kawo fatan cimma matsayar diflomasiyya ko kuma barazanar komawa fagen daga.
Ga wasu dalilai huɗu da suka tattaunawar ke cikin kila-wa-kala.
1) Kalaman nasara da barazana
Shugaban Amurka Donald Trump ya wallafa a shafinsa na Truth Social cewa Amurka "na samun nasara a yaƙi da Iran kuma da gagarumin rinjaye" inda ya ƙara da cewa "abubuwa na tafiya yadda ake so" da kuma cewa sojojin Amurka "sun yi gagarumin aiki".
Masana sun ce waɗannan kalamai sun ƙara matsin lambar siyasa ce kawai maimakon samar da hanyar tattaunawa. Maimakon amfani da kalaman sulhu, an yi amfani da kalaman "yaƙi" abin da ya ƙara dagula al'amura.
A ɗaya gefen, Iran ta mayar da martani da kakkausar murya, inda ta ce ba za ta amince da tattaunawa cikin barazana ba, lamarin da ke nuna cewa ɓangarorin biyu ba sa kan turba ɗaya.
2) Ƙwace jirgin ruwan Iran
Asalin hoton, Getty Images
Hankula sun ƙara tashi bayan da sojojin Amurka suka ƙwace wani jirgin dakon kaya na Iran wanda ya nufi tashar jirgin ruwa ta Bandar Abbas. Lamarin ya faru ne bayan da jirgin ruwan ya yi kokarin tsallake shingen da Amurka ta saka.
Amurka ta fitar da wasu hotuna da bidiyo waɗanda suka nuna lokacin da dakarun ƙasar suka ƙwace jirgin, lamari da ake gani na ci gaba da ɗaukar matakin soji duk da ana cikin tsagaita wuta.
Iran ta mayar da martani cikin fushi, inda ta yi gargaɗin cewa a shirye take ta yi komai. Daga bisani ta mayar da martani ta hanyar far wsa jiragen ruwan yaƙin Amurka.
Iran tana kallon hakan kamar almara, 'muna tattaunawa, ka ƙwace jirgin ruwan mu'. Wannan batu ya ƙara janyo fargaba da kuma rage yarda tsakanin ɓangarorin biyu.
3) Rabuwar kai a Iran kan tattaunawa
Rahotanni daga cikin Iran sun bayyana irin rabuwar kai kan yiwuwar shiga tattaunawa. Wasu majiyoyin diflomasiyya sun ce Tehran na ci gaba da "yin nazar sosai" kan yiwuwar shiga tattaunawa, tare da duba sharuɗa da ke ƙasa.
Sai dai, kalamai daga manyan jagororin ƙasar sun yi tsauri. Kakakin majalisar dokokin Iran Mohammad Baqer Qalibaf ya ce Iran "ba za ta amince da tattaunawa karkashin barazana ba," inda ya ƙara da cewa ƙasar na shirin ƙara nuna ƙarfinta a fagen daga a cikin makonni biyu da suka wuce.
Sai dai, daga baya Pakistan ta ce tana magana da manyan jagororin Iran, inda suke nuna alamun shiga tattaunawa, wanda ake sa ran yi a yau Talata.
Kalamai daban-daban da ke fita sun nuna ƙarara cewa babu wani zaɓi daga wajen Iran kan cewa ko a ci gaba da tattaunawa ko kuma akasin haka. Kuma wannan shi ma wani dalili da ke jawo cikas a tattaunawar.
4) Gaza warware tsoffin matsaloli
Duk da irin ci gaba da ake samu, batun da ake rikici a kai bai sauya ba. Batun shirin nukiliyar Iran da kuma mashigar Hormuz su ne abubuwa da ke kan gaba a rikicin, inda kowane ɓangare ya hau kujerar naki.
Amurka- na kallon shirin nukiliyar Iran a matsayin barazana ga tsaron ƙasa da ƙasa, yayin da Iran na kallon shirin a matsayin ƴancin kirkiro da abubuwan fasaha.
Wannan bambanci tsakanin ɓangarorin ya wanzu na tsawon shekaru da dama kuma har yanzu ba a warware shi baki ɗaya ba.
Hakan na nufin cewa ko da babu wani sabon tashin hankali da aka samu, tattaunawa za ta yi wuya. Ƙaruwar sabbin matsaloli sun saka lamarin zama mai wahalar warware wa.
Babban Labari
Labarai na musamman
Labaran da suka fi shahara
Babu karin bayanai