Ƴan sama-jannati sun kama hanyar zuwa duniyar wata
Asalin hoton, NASA
- Marubuci, Pallab Ghosh
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Science Correspondent
- Marubuci, Alison Francis
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Senior Science Journalist
- Lokacin karatu: Minti 6
Hukumar binciken sararin samaniya ta Amurka (Nasa) ta tura ƴan sama-jannati a karon farko cikin shekara 50 zuwa duniyar wata, a ranar ɗaya ga watan Afrilun 2026.
Tafiyar, wadda aka yi wa laƙabi da Artemis II a turance, za ta ɗauki kimanin kwana 10, inda ƴan sama-jannatin za su je wuri mafi nisa fiye da kowane bil'adama a tarihi.
Tawagar ƴan sama-jannatin hudu ba za su sauka a kan duniya wata ba, sai dai za su yi zagaye a kusa da watan, inda za su duba yiwuwar share fagen yadda ɗan'adam zai sake sauka a kan duniya, karon farko tun bayan shekarun 1960 da kuma 1970.
Me ya sa aka jinkirta tafiyar?
An ɗan samu tangardar na'ura na ƴan awanni, wanda hakan ya sa aka ɗan jinkirta kafin harba kumbon.
Matsalar da aka samu ita ce ta na'urar da za ta lalata kumbon idan ya kauce daga kan falakinsa, da kuma na batirin tsayar da harba kumbon idan an samu tangarɗa, wanda shi ne aka tsara zai kawar da sunduƙin da ƴan sama jannatin suke ciki zuwa wuri mai aminci idan tangarɗa ta faru a lokacin harba kumbon.
Amma an samu nasarar warware tangarɗar ba tare da ɓata lokaci mai tsawo ba.
Bayar harba kumbon an dan samu tangarɗar sadarwa na ƙanƙanin lokaci, inda masu kula da tafiyar kumbon a doron ƙasa suka kasa yin magana da ƴan sama-jannati da ke cikin kumbon, sai kuma tangarɗar da aka samu da ban-ɗakin cikin kumbon, amma tuni an maganace matsalolin.
An fasa yunƙurin da aka yi na gwajin harba kumbon a cikin watan Fabarairu da kuma Maris sanadiyyar tsiyayar mai da aka samu jikin kumbon.
A lokacin da ake tsara tafiya, wajibi ne masana su yi la'akari da yanayi da kuma tsayawa har sai wata yana a daidai inda ake buƙata a kan falaki.
Me ya faru a lokacin harba kumbon?
Ƴan sama-jannatin sun kama hanya ne da ƙarfe 11:35 na dare agogon Birtaniya a ranar Laraba 1 ga watan Afrilun 2026.
Mutanen da suka taru domin kallo sun ɓarke da shewa a wajen cibiyar nazarin sararin samaniya ta Kennedy Space Center.
Masu kallo sun ga yadda injuna biyu da suka taimaka wajen tashin kumbon suka rabu da jikinsa bayan da ya kai gudun kilomita 16,100 cikin awa ɗaya a sararin samaniya.
Kumbon ya hau kan falaki ne lokacin da ya rasta layin 'Karman' wanda shi ne kan iyaka tsakanin sararin samaniyar duniyar bil'adama da kuma sauran sararin subuhana.
Mene ne ƴan sama-jannatin za su yi a lokacin tafiyar??
Ƴan sama-jannati huɗu da ke yin wannan tafiya ta Artemis II - Reid Weisman, da Victor Glover, da Christina Koch da kuma Jeremy Hansen - sun kasance cikin wannan tawaga ta farko da za ta yi irin wannan balaguro.
Hansen, wanda ke aiki da hukumar binciken sararin samaniya ta Canada ya zama mutum na farko ɗan ƙasar Canada da zai yi balaguro zuwa duniyar wata.
A lokacin balaguron, matafiyan za su gwada yadda za a iya sarrafa sunduƙin da suke ciki mai suna Orion da kansu, domin gwada yadda za a iya amfani da shi domin sauka a duniyar wata cikin tafiye-tafiyen da za a yi zuwa duniyar wata a nan gaba.
Za kuma su gwada yadda sunduƙin zai iya taimaka wa ɗan'adam ya rayu cikin sukuni a duniyar wata a nan gaba.
Bugu da ƙari ƴan sama-jannatin za su gwada kayan kiwon lafiya da suka tafi da su, kuma za su turo bayanai da hotuna daga sararin samaniya zuwa duniyarmu.
A lokacin dawowa duniya, ƴan sama-jannatin za su gamu da gargada lokacin da suke shigowa samaniyar duniyar bil'adama, inda a ƙarshe sunduƙin da suke ciki zai faɗa cikin tekun Pacific ta gaɓar ƙasar Amurka.
Ko ƴan sama-jannatin za su sauka a kan wata?
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
A'a. Wannan tafiyar ta gwaji ce da kuma shiri gabanin balaguron Artemis na IV da ake sa ran bil'adama zai sauka a duniyar wata, wadda aka tsara yi a shekara ta 2028.
Gabanin tafiyar Artemis IV, hukumar binciken sararin samaniya ta Amurka za ta gudanar da wata tafiyar ta gwaji da aka yi wa taken Artemis III a shekara ta 2027 domin gwada yadda sunduƙin Orion zai iya sauka a kan wata, sannan kuma a yi gwajin sabuwar rigar ƴan sama-jannati da ake sa ran za a yi amfani da ita.
Nasa ta zaɓi kumbo na kamfanoni biyu da za a yi amfani da su domin balaguron biyu da ke tafe: wato kumbon Starship na kamfanin SpaceX da kuma kumbon Blue Origin na kamfanin attajiri Jeff Bezos.
Kafin lokacin tafiyar ne hukumar Nasa za ta tantance kumbon da za a yi amfani da shi domin kowace tafiya.
Idan lokacin tafiyar Artemis IV ya zo, ƴan sama-jannati za su sauka ne a ɓarayin kudancin duniyar wata.
Bayan haka ne kuma ake sa ran ƙara tura wani kumbon zuwa wata a cikin shekarar ta 2028, wanda aka yi wa laƙabi da tafiyar Artemis na biyar, domin samar da abubuwan da za su taimaka wa bil'adama ya yi rayuwa a duniyar wata.
Yaushe ne lokaci na ƙarshe da ɗan'adam ya je duniyar wata?
Lokaci na ƙarshe da bil'adama ya je duniyar wata shi ne tafiyar kumbo Apollo 17, wanda ya sauka kan wata a cikin watan Disamban 1972, sannan ya dawo duniyarmu.
A tarihin ɗan'adam, mutum 24 ne jimilla suka taɓa zuwa duniyar wata, kuma mutum 12 ne suka yi tafiya a doron duniyar ta wata, an yi amfani da kumbo Apollo ne wajen yin dukkanin tafiye-tafiyen.
A cikin shekarun 1960 ne Amurka ta tura kumbon nata, domin ganin ta sha gaban Tarayyar Soviet.
Asalin hoton, NASA, ESA
Ko akwai wasu ƙashen da ke shirin zuwa wata?
Akwai ƙasashe da dama da ke yunƙurin ganin sun tura mutanensu zuwa duniyar wata cikin shekarun 2030.
Ana sa ran ƴan sama-jannati na nahiyar Turai za su shiga balaguron da ake yi na Artemis a nan gaba, tuni Japan ta samu kujera a cikin tafiye-tafiyen na gaba.
China kuma tana ƙera nata kumbon, inda take sa ran tura ƴan sama-jannati waɗanda za su sauka kan wata a cikin shekara ta 2030.
Rasha na ci gaba da yin nata shirin na tura mutanenta zuwa wata, inda take sa ran za ta gina wani ƙaramin sansani a kan wata tsakanin shekarar 2030 zuwa 2035.
Sai dai akwai yiwuwar takunkuman da aka ƙaƙaba wa ƙasar da ƙarancin kuɗi su yi mata karan-tsaye wajen cimma manufar tata kamar yadda ta tsara.
Ita ma ƙasar Indiya na sa ran wata rana za ta tura mutanenta zuwa kan watan.
Babban Labari
Labarai na musamman
Labaran da suka fi shahara
Babu karin bayanai