Wane ne Sarki Sulaimanu, Sarkin Kano na farko a tarihi?
Asalin hoton, INSTAGRAM/Maikatanga Photography
Sarki Sulaimanu shi ne sarki na 44, amma shi ne sarki na farko a cikin sarakunan Fulɓe.
Lokacin da aka yi jihadi aka kori Sarki Alwali an naɗa Sulaimanu ne a matsayin Sarki na ɗaya a daular Fulani.
Gabanin naɗa shi, shi ne limamin manyan gidajen da suka haɗu suka yi jihadi. Kuma mafi karancin shekaru a cikinsu.
Ya yi sarautar Kano a tsakanin shekarar 1807 zuwa shekarar 1819 miladiyya kafin Allah ya kawo ƙarshen mulkinsa.
Sarki ne malamin addinin Musulunci, wanda masana tarihi suka bayyana cewa yana da sauƙin kai da amana da girmama mutane musamman ɗaliban ilimi da almajirai.
Tarihi ya nuna cewa mutanen gari sun ji daɗin rayuwa a zamaninsa kuma an samu rayuwa da zamantakewa mai kyau.
A zamaninsa an fifita ilimin addinin musulunci sosai, sannan mutane sun kasance suna ƙoƙarin bin dokokin shari'a da ya gindaya na gudanar da harkokin mulki da sarauta.
Masarautar Kano tana cikin manyan masarautu a ƙasar Hausa a yammacin Afirka, kuma tarihi ya nuna tsohuwar masarauta ce da aka kafa shekaru aru-aru.
Masarautar ta taimaka wajen bunƙasa garin Kano da Arewa da ma Najeriya baki ɗaya.
Yada wakilan Kano suka ƙi amincewa da sarauta
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Dr Raliya Zubairu Ahmad ta sashen nazarin tarihi a kwalejin ilimi ta Sa'adatu Rimi da ke, ta ce Sarki Sulaimanu ya zama sarki ne bisa ƙaddarawar Allah, kuma cikin sauƙi da lalama.
"Bai gada ba, ba naɗa kansa ya yi ba, kuma ba zaɓarsa aka yi ba. Wato abin da ya faru lokacin da Fulɓe suka ci Kano da yaƙi, sai shugabanninsu suka yi shawarar zuwa su sanar da Shehu Usman Ɗanfodiyo abin da ake ciki domin ya naɗa musu shugaba kamar yadda ake yi a kowane gari da Fulɓe suka yi jihadi."
Masaniyar tarihin ta ƙara da cewa wakilai ne suka tafi wajen Shehu Usman Ɗanfodio, amma a ƙarƙashin jagorancin jagorori guda biyar:
- Tawagar Yolawa a ƙarƙashin Malam Jibo da Goshi
- Jagoran Danejawa Malam Ɗanzabuwa wanda shi ne shugabansu baki ɗaya
- Malam Jamo shugaban Sullaɓawa
- Malam Dabon Dambazau, shugaban Dambazawa
- Malam Bakatin, shugaban Joɓawa
Dr Raliya ta ce waɗannan ne jagororin da suka jagoranci wasu gidaje da mutane zuwa wajen Shehu Usman Ɗanfodio.
"Suna hanyar tafiya ne Allah ya yi wa Malam Ɗanzabuwa rasuwa a garin Badau da ke yankin Bichi. Da ya rasu sai shugabanci ya koma hannun Malam Jamo, jagoran Sulluɓawa, wanda kuma ya kasance yaya ne wajen Sarki Ibrahim Dabo."
"Limaminku, sarkinku"
Masaniyar tarihin ta ƙara da cewa da wakilan suka isa ne sai suka haɗu da Sheikh Muhammad Bello a birnin Gada.
"A nan suka gabatar da kansu suka bayyana masa sun samu nasara a Kano suna so a naɗa musu shugaba."
Raliya Zubairu ta ce bayan sun gabatar da kansu sai Sheikh Muhammadu Bello ya ce tunda dai Malam Jamo ne ya gabatar da jawabi a madadinsu, kawai ya zama Sarkin Kano ya koma ya cigaba da sarauta.
"Amma sai ya ƙi amsa, sai Muhammad Bello ya ce Dabon Dambazau ya zama sarki, shi ma ya ƙi amincewa. Haka ya zagaya dukansu, kowa ya ca ba ya son sarauta," in ji ta.
A cewar Dr Raliya, a lokacin ne Muhammad Bello ya tambaye su wane ne suka bari a gida yake jagorantar al'umma.
"A nan ne suka faɗa masa cewa sun bar garin ne a hannun wani mai suna Malam Sulaimanu. Shi ne yake limanci."
"Shi ne ya ce musu ga tuta su kai masa ya zama sarki. Sai suka faɗa masa cewa ai yaro ne. Sai Muhammad Bello ya amsa su cewa 'Imamukum, amirukum' wato limaminku ne shugabanku. Tunda dai shi ne yake limanci, shi ne zai zama sarkinku."
Ta ƙara da cewa haka aka yi kuwa, suka kai masa tuta suka bayyana masa cewa shi ne Sarkin Kano.
Sai dai ta ƙara da cewa akwai wani ƙaulin na da masana tarihi suke alaƙantawa da yadda Sarki Sulaimanu ya zama sarki.
"Hujja ta biyu ta bayyana cewa an tsinci wasiƙa a aljihun Malam Ɗanzabuwa, wanda shi ne shugaban tafiyar na farko yana ba Ɗanfodio shawara cewa idan tafiyar ta tabbata, a naɗa Malam Sulaimanu sarki," in ji ta, sai dai ta ƙara da cewa wannan hujjar ba ta da ƙarfi sosai.
"Na ajiye Kano, na ɗau rafi"
Asalin hoton, M T Safana
Dr Raliya ta ce Sarki Sulaimanu ya sha wahalar mulkin Kano, bai ji daɗin mulkin ba kamar sauran sarakuna, saboda a cewarta abubuwa sun zo masa ba shiri ba tsammani.
"Bai zata zai zama sarki ba, bai iya irin sarautar ba kuma bai shirya ba. Duk tarbiyarsa ta amjiranci ce da malanta. Bai taɓa tunanin zama sarki ba. Karatu yake yi da rubutu da sauran ɗabi'un almajirai. Sai kwatsam aka ce masa shi ne sarki, ga kuma ƙuruciya."
"Da ya zama sarki sai ya ƙi shiga gidan sarakuna. Wasu ƴan'uwansu ne suka ce kar ya shiga gidan sarauta saboda suna fargabar zai iya zama tamkar irin waɗanda suka yaƙa, kuma matsalar da suka kawar za ta dawo," in ji ta.
Ta ce wannan ne ya sa a farkon lokacinsa ya zama tamkar babu sarki a Kano, saboda wasu ba sa masa wannan kallon.
Masaniyar tarihin ta ce daga baya ne wani ya ba shi shawarar cewa matuƙar yana so ya samu karɓuwa a sarautar, to lallai ya koma Gidan Rumfa, da aka saba da ita a matsayin gidan sarauta.
"Wannan ne ya sa ya aika saƙo wajen Shehu Usman Ɗanfodio yana neman shawarar yadda zai yi. Shi ne sai Ɗanfodio ya ce masa ya koma gidan sarautar, sannan ya aika masa wuƙa da takobi, ya ce masa duk wanda ya yi masa wargi ya sare masa kai," in ji Dr Raliya.
Masaniyar ta ce duk da kasancewarsa a gidan sarkin, idan ana fadaci Sarki Sulaimanu sai ya zauna a ƙasa ba a karagar mulki ba, inda ta ƙara da cewa yakan hau karagar kawai idan zai yi shari'a.
"Kuma komai zai yi tare da almajirai yake yi, suna bayyana albarkacin bakinsu. Haka ake yi a fada kuma, ana zaune kowa na wani aikin. Wasu na saƙar riga, wasu ta tabarma da sauransu."
Dr Raliya ta ce shi ma sarkin da an gama zama, "sai ya tashi ya tafi rafi ya je noma. Shi ya sa yakan ce 'na ajiye Kano na ɗauki Rafi."
Ta ƙara da cewa Malam Abdullahi Gwandu ya je Kano, inda ya rubuta littafi mai suna "Diya'ul hukkam" kuma littafin ya taimaka wa Sulaimanu sosai wajen gudanar da harkokin mulki.
Gwagwarmaya
Dr Raliya ta ce kasancewar Sarki Sulaimanu mutum ne mai sauƙin kai da son zaman lafiya, sai ya kasance bai yi yaƙi ba sosai.
Sai dai ta bayyana cewa ya sha fama da matsalolin cikin gida da faɗa tashi tun a tsakanin mutane na kusa da shi.
"Su jagororin Fulɓen da suke karɓo tuta daga baya sun fara jin haushin me ya sa ba suk karɓi sarautar ba. Suna ganin ba ya ƙoƙari sosai, suna tunanin da su ne, da za su fi shsi ƙoƙari," in ji ta.
Masaniyar tarihin ta ce jagororin Sulluɓawa da Yolawa ne suka ba shi haɗin kai sosai har ta Allah ta yi.
Babban Labari
Labarai na musamman
Labaran da suka fi shahara
Babu karin bayanai