Gasar ninƙaya da mai sayar da kayan tarihi cikin hotunan Afirka

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, A ranar Litinin aka gudanar da baje kolin zane-zane a birnin Abidjan na kasar Ivory Coast

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, Wata Ƙungiya na wasa a dandalin convention na birnin Abidjan

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Ranar Laraba wasu jama`a sun gudanar da zanga-zangar ƙarin kuɗin haraji a Nairobi babban birnin kasar Kenya

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Wani mutum zaune kusa da motar da aka kunnawa wuta yayin zanga-zangar da jagoran adawa Raila Odinga ya kira

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Wani daga cikin masu zanga-zangar yana tserewa daga hayaƙi mai sa hawaye, bayan mutuwar mutane shida ranar Laraba

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, Murnar dawowar matasan da suka halarci bikin gargajiya na Elim ranar Asabar a kasar Afirka ta Kudu

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, Akalla matasa 68,000 ne suka halarci bikin a lardin Limpopo

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Likita yana duba idon maras lafiya a Abuja baban birnin Tarayyar Najeriya

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Mai sayar da kayan tarihi a birnin Luxor na kasar Masar

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, Tsananin zafi a Arewacin Afirka a ranar Laraba ya sanya wani yaro ninƙaya a Kogin Nilu

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Nadine Barsoum ƴar kasar Masar a lokacin gasar wasannin ruwa karo na 20 ranar Juma`a a Japan

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, Ƴar wasan Najeriya Michelle Alozie ta ziyarci filin wasa na Rectangular Stadium a Australia yayin gasar wasan ƙwallon ƙafa ta mata