Gareth Bale ya yi retiya daga kwallon kafa

Gareth Bale
Bayanan hoto, Gareth Bale

 

Kyaftin dan Wales Gareth Bale ya sanar da yin ritaya daga buga kwallon kafa yana da shekara 33. Dan wasan wanda ya taka rawar gani ta sanar da  haka ne a shafukan sada zumunta.

Shi ne dan wasan da fi rike mukamin kyaftin ga kasarsa a wasannin 111 kuma ya sanar da haka ne a shafukan sada zumunta.

Bale, wanda ya lashe gasar zakarun Turai sau biyar tare da Real Madrid, za a iya cewa shi ne dan wasan kwallon kafa daya fi shahara daga yankin Wales.

"Bayan  na yi nazari sosai, ina son na sanar da yin murabus nan take daga wasan kwallon kafa a wata kungiya da kuma kasa da kasa," In ji  Bale .

"Ina farin ciki matuka da na cimma burinna na buga wasan da nake kauna ."

Bale wanda haifaffen Cardiff ne ya taka leda a Southampton da  Tottenham Hotspur da kuma Real Madrid kafin ya koma kungiyar Los Angeles FC ta Amurka

Shi ne  ya kasance gwanin kasarsa yayin da suka kai ga gasar cin kofin nahiyar Turai a 2016 da 2020 kafin ya jagoranci Wales a gasar cin kofin duniya  a Qatar a 2022 a karon farko tun bayan 1958