Lewandowski da wasu fitattun ƴan wasan da ba za su je Gasar Kofin Duniya ba

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Robert Lewandowski ya ci ƙwallaye sama da 700 a matakin kulob da kuma ƙasarsa
    • Marubuci, Michael Emons
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Sport journalist
  • Lokacin karatu: Minti 5

Ɗaya daga cikin ƴan wasan gaba mafi shahara a duniyar kwallon kafa a tsawon shekara 15 da suka wuce - ɗan ƙasar Poland Robert Lewandowski - yana cikin manyan taurarin kwallon kafa da ba za su je gasar kofin duniya ba da za a yi a Canada, Amurka da kuma Mexico a wannan shekara.

Ɗan wasan mai shekara 37 da ke buga wa ƙungiyar Barcelona, wanda ya zura kwallaye 89 wa ƙasarsa, ya kasa taimaka mata zuwa gasar kofin duniya bayan da suka yi rashin nasara a hannun Sweden da ci 3-2 a birnin Stockholm ranar Talata, a wasan karshe na neman gurbin xuwa gasar.

Lewandowski, wanda ya lashe gasar Bundesliga ta Jamus har sau goma - biyu da Borussia Dortmund sai kuma guda takwas a jere da Bayern Munich, kafin cin La Liga biyu da Barca - za a iya cewa ya buga wasansa na karshe a matakin ƙasa.

Mun yi duba kan ƴan wasa shida waɗanda su ma suka gaza tsallakewa zuwa gasar ta kofin duniya.

Gianluigi Donnarumma (Man City da Italiya)

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Italy ta kasa zuwa gasar kofin duniya karo na uku kenan a jere yanzu

Gianluigi Donnarumma ya kasance mai tsaron raga mafi kwazo a gasar Premier a bana tun bayan komawa Manchester City daga Paris St-Germain kan fam miliyan 26 a watan Satumba, bayan taimakawa ƙungiyar ta Faransa lashe gasar Champions League a bara.

Duk da kasancewa ɗan wasan da ya fi haskawa lokacin da Italiya ta lashe gasar Euro 2020, yanzu ƙasarsa ta gaza zuwa gasar kofin duniya bayan rashin nasara da ci 4-1 a hannun Bosnia-Herzegovina a bugun fenariti ranar Talata.

Serhou Guirassy (Dortmund da Guinea)

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Serhou Guirassy shi ne na huɗu a yawan cin kwallaye a gasar Bundesliga a bana

Serhou Guirassy ya assasa kansa a matsayin ɗaya daga cikin ƴan wasan gaba mafi hazaka a duniyar kwallon kafa, inda ya zura kwallaye 62 a Bundesliga a cikin kakar wasanni uku da suka gabata, sannan babu ɗan wasan da ya ci kwallo sama da 13 wanda ya zura a gasar Champions League na kakar 2024-25.

Sai dai, ba zai samu damar zuwa gasar kofin duniya ba saboda ƙasarsa ta Guineata fita tun a zagayen farko na neman gurbi a ɓangaren Afirka, inda suka kare a matsayi na huɗu a rukuninsu, nasara huɗu kacal da kuma canjaras guda uku a cikin wasanni goma.

Khvicha Kvaratskhelia (PSG da Georgia)

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Georgia ta lashe wasa ɗaya kawai cikin wasanni shida da ta buga na neman gurbin zuwa kofin duniya - ci 3-0 da ta yi kan Bulgaria a gida

Khvicha Kvaratskhelia ya taimakawa Paris St-Germain zama zakarun Turai a bara, inda ya zura kwallo a wasan karshe da suka doke Inter Milan 5-0.

Ya kuma zo na 12 cikin jerin ƴan wasan da suka fi haskawa na kyautar Ballon d'Or.

Sai dai Georgia ba ta taɓuka wani abin kirki ba a wasannin neman gurbin zuwa gasar kofin duniya, saboda maki uku kaɗai suka samu a cikin rukunin da ya kunshi Spain, Turkiyya da kuma Bulgaria.

Lewandowski (Barcelona da Poland)

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Robert Lewandowski zai kai shekara 41 lokacin da za a sake buga gasar kofin duniya a 2030

Lewandowski ya jagoranci Poland zuwa gasar kofin duniya ta 2018 a Rasha, sai dai bai zura ko da kwallo ɗaya ba inda ƙasarsa ta kare a karshen teburin rukuninsu.

Ya samu haskawa a gasar kofin duniya da aka yi a Qatar a 2022, inda ya zura kwallo biyu har da kai Poland zagayen ƴan 16, kafin Faransa ta doke su.

Ya ci kwallaye hu,du a wasan rukuni na neman gurbin zuwa gasar kofin duniya na 2026, inda ƙasarsa ta kare a kasan Netherlands wadda ta fi ta da maki uku - kafin su yi rashin nasara a hannun Sweden ranar Talata.

Victor Osimhen (Galatasaray da Najeriya)

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Victor Osimhen ya zura kwallaye 26 a ƙungiya da kuma ƙasarsa a bana

Victor Osimhen ta taimakaa Napoli lashe Serie A a 2023 kafin ya koma Galatasaray, inda ya zura kwallaye 26 a cikin wasanni 30, abin da ya ba su nasarar lashe gasar Turkiyya a bara.

Najeriya ta yi canjaras biyar a cikin wasanni 10 na neman gurbin zuwa kofin duniya, inda ta kare maki ɗaya kasan Afirka ta Kudu, sai dai sun samu dama ta biyu a wasan neman gurbi da ya biyo.

Najeriya ta yi rashin nasara a hannun Kongo a bugun fenariti wanda aka buga bayan sauya Osimhen, abin da ya sa ƙasar ta kasa zuwa gasar kofin duniya.

Dominik Szoboszlai (Liverpool da Hungary)

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Dominik Szoboszlai ya ci wa Liverpool kwallaye 12 a kakar bana

Ɗan wasan tsakiyar Liverpool da Hungary Dominik Szoboszlai yana haskawa sosai a bana kuma ya ci kwallaye masu kayatarwa da ban sha'awa.

Sai dai ba zai samu damar zuwa gasar kofin duniya ba bayan da ƙasarsa ta sha kashi a hannun Jamhuriyar Ireland da ci 3-2.

Ƴan wasan fili 11 da ba za su je Gasar Kofin Duniya ba

Sauran ƴan wasa

Ana sa ran gasar kofin duniyar da za a yi a watan Yuni da Yuli za ta ƙayatar sosai.

Sauran ƴan wasan da ba za su je gasar ba sun haɗa da mai tsaron raga

  • Jan Oblak (Atletico Madrid da Slovenia).
  • Milos Kerkez (Liverpool da Hungary).
  • Nikola Milenkovic (Nottingham Forest da Serbia)
  • Willi Orban (RB Leipzig da Hungary).
  • Ola Aina (Nottingham Forest da Nigeria).
  • Sandro Tonali (Newcastle da Italiya)
  • Bryan Mbeumo (Manchester United da Kamaru).