Miyagun makaman da Amurka ke amfani da su wajen kai wa Iran hari

Lokacin karatu: Minti 4

Amurka ta fara kai wa Iran hare-hare ne tare da taimakon Isra'ila a ranar 28 ga watan Fabrairun 2026, abin da ya sake buɗe sabon babi na zaman fargaba a Gabas ta Tsakiya.

Samamen ya haɗa da amfani da makamai na zamani masu ƙarfi da kuma cin dogon zango da za su iya kai hari ko'ina.

A cikin sa'o'i 48 na farko, an kai hari ne ta hanyar amfani da manyan jiragen sojin sama, ciki har da jiragen yaƙi, da makamai masu linzami masu dogon zango da kuma na'urori masu tattara bayanan sirri.

Wannan ya nuna irin shirin da Amurka ta daɗe tana yi, kafin ƙaddamar da hari.

Rahotanni daga majiyoyin soji sun nuna cewa an fara tsara yadda za a kai harin ne a watan Janairun wannan shekara, wanda ya haɗa da rarraba kaya, ƙarfafa sansanonin soji da ke Gabas ta Tsakiya, da kuma aika jiragen ruwa da jiragen sama na yaƙi.

Ana ganin haɗin kai tsakanin Amurka da Isra'ila ya ƙaru a wannan yaƙi, inda kowane ɓangare ke kai hari kan muhimman wurare a cikin Iran.

A wannan maƙala, mun duba wasu manyan makamai da ake amfani da su wajen kai waɗannan hare-hare, wanda ke nuna yadda yaƙe-yaƙe na baya-bayan nan ke ƙara dogaro da fasahar zamani.

Jiragen yaƙin zamani na B-2 bomber

Ɗaya daga cikin muhimman makamai da ake amfani da su a wannan yaƙi wajen kai hare-hare shi ne jirgin yaƙi na B-2 Spirit. Wannan jirgi na cikin cigaban fasaha a ɓangaren sojin saman Amurka, inda yake iya kauce wa abokan gaba wajen gano shi.

Kamfanin Northrop Grumman ne ya ƙera B-2 Spirit, kuma an tsara shi ne wajen kai hare-hare na musamman kan shingayen da ke da matukar tsaro, kamar cibiyoyin nukiliya da kuma wurin adana makamai.

A wannan yaƙi, wannan jirgi ya yi tafiyar sama da sa'a 30 daga Amurka zuwa Iran, inda ya kai hari kan muhimman wurare. Damar da suke da ita na yin tafiya mai nisa ba tare da sun sha mai ba, shi ya saka za su iya kai wa ko'ina a duniya.

Jirgin zai iya ɗaukar manyan bama-bamai, ciki har da na'uin bam ɗin da za su iya far wa wuraren ɓuya na karkashin ƙasa. Wannan ya sa ya zama makami mai muhimmanci wajen far wa wuraren da ke matukar tsaro.

Amfani da jirgin B-2 Spirit ya nuna yadda Amurka ta dogara da fasahar zamani wajen tabbatar da cewa ta kai hari cikin nasara ba tare da an gane da wuri ba.

Makamai masu linzami na Tomahawk

Ƙari a kan jiragen yaƙi, Amurka ta yi kuma tana ci gaba da amfani da makaman linzami masu cin dogon zango na Tomahawk, waɗanda ake harba wa daga cikin jiragen ruwan yaƙi na kuma na karkashin ruwa.

Waɗannan makaman linzami na iya tafiya mai nisa da kuma afka wa shinge daidai yadda aka tsara, ta hanyar amfani da na'urorin sa ido na zamani.

A hare-haren da aka kai wa Iran, an yi amfani da Tomahawksn wajen far wa shingayen soji masu muhimmanci, musamman a lokacin farko na fara yaƙin.

Muhimmancin makaman shi ne ana iya harba su daga wuri mai nisa ba tare da sun lahanta matukin jiragen ba, abin da ke rage barazana ga masu harba su.

Amfani da Tomahawks na nuni da irin dabarun Amurka na yin amfani da hare-hare daga nesa wajen raunana tsaron Iran, kafin shiga sararin samaniyarta kai-tsaye.

Jirage marasa matuƙa na MQ-9

Jirgi mara matuki na MQ-9 yana ɗaya daga cikin makamai masu muhimmanci a yaƙin zamani, inda ake amfani da shi wajen bincike da kuma kai hari a lokaci guda.

Jirgin na iya tsayawa a sama na tsawon sama da sa'a 27, yana karɓar bayanan soji masu muhimmanci da kuma kai hari idan buƙatar hakan ta taso.

A lokacin far wa Iran, an yi amfani da MQ-9 domin bibiyar shige da ficen sojojin Iran ɗin da kuma afka wa shingaye da ƙarfi.

Jirgin yana iya ɗaukar makaman linzami da wasu makamai, abin da ke ba shi damar kai hari cikin gaggawa ba tare da yin gargaɗi ba.

Amfani da wannan jirgi ya kawo wani sauyi na yadda Amurka ke kai hari da fasahar zamani ba tare da taimakon ɗan'adam ba, kuma hakan ya taka rawar gani wajen kai wa Iran hare-hare.

Sauran makamai da Amurka ta yi amfani da su kan Iran

Ba ya ga waɗannan manyan makamai, Amurka ta kuma yi amfani da jiragenm yaƙi daban-daban kamar F-15, F-16, F-18, F-35, da kuma A-10, waɗanda suka kai hare-hare ta sama da kuma kare dakarunta.

Haka kuma, an yi amfani da tsarin tsaro na THAAD wajen kakkaɓe makaman linzamin Iran, yayin da aka yi amfani da jirgin EA-18 wajen lalata hanyoyin sadarwa da kuma na'urorin gano makamai da aka harba.

Samamen ya haɗa amfani da tsarin makaman linzami na HIMARS, jirage masu bincike kamar P-8, da kuma jiragen ruwa na yaƙi irinsu USS Abraham Lincoln da USS Gerald R. Ford, waɗanda ke taimakawa wajen kai hare-hare daga ruwa.