Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Ko sulhun da Pantami ya yi wa El-Rufai da Uba Sani zai ɗore?
Ƴan Najeriya na ci gaba da tafka muhawara musamman a shafukan sada zumunta game da sulhu da fitaccen malamin Addinin Musulunci Sheikh Ali Isa Pantami ya yi wa El-Rufai da Uba Sani.
Al'amarin ya ɗauki hankalin mutane da dama musamman waɗanda ke bibiyar abubuwan da suka shiga tsakanin tsohon gwamna da gwamnan jihar na yanzu.
Mutanen biyu dai sun jima ba sa ga maciji da juna, sakamakon rashin jituwa da ta shiga tsakaninsu, jim kaɗan bayan saukar El-Rufai daga mulkin jihar Kaduna.
Malamin ya yi musu sulhu ne a lokacin jana'izar mahaifiyar El-Rufai, Hajiya Umma ranar Lahadi a Abuja.
Jana'aizar ta samu halartar fitattun ƴansiyasar Najeriya, ciki har da waɗanda ke takun-saƙa da tsohon gwamnan.
Hajiya Umma El-Rufai ta rasu ne ranar Juma'a bayan fama da jinya a birnin Alƙahira da ke Masar.
Dattijuwar ta rasu ne a daidai lokacin da El-Rufai ke tsare a hannun hukumar ICPC mai yaƙi da almundahanar kuɗaɗe, wani abu da ya ƙara ɗaukar hankalin yan ƙasar da dama.
Sai dai hukumar ta sake shi jim kaɗan bayan ɓullar labarin rasuwar mahaifiyar tasa.
Yadda Pantami ya yi musu sulhu
Kasancewar mutanen biyu sun jima da samun rashin jituwa tsakaninsu, Sheikh Pantami ya yi amfani da damarsu a wurin jana'izar wajen yi musu sulhun a bainar jama'a.
Jim kaɗan bayan binne gawar a maƙabarta, bayan mutane sun fara gaisawa, sai malamin ya fara yin nasiha ga mahalarta janazar, wadda daga baya ta riƙiɗe ta koma sulhu tsakanin El-Rufai da Uba Sani, waɗanda ke tsaye kusa da juna, shi kuwa malamin na tsakiyarsu.
Ya fara da batun haɗin kai tsakanin al'ummar musulmai, yana mai cewa ya kamata musulmai su riƙa ganin alkairan juna.
"Mu tuna da alkairan juna fiye da sharrin juna, mu sani abin da haɗa mu, ya fi abin da raba mu yawa'',
Ya ci gaba da cewa ''mu sani da ni da kai duk abin da muke so ba wanda zai ba mu shi sai Allah, ba kuma wanda zai iya hana mu sai Allah''.
Daga nan sai ya kama hannun Uba Sani - da ke ɗaya ɓarin nasa, ya kuma kama na El-Rufai da ke ɗaya gefen - ya ce musu ku yafi juna.
Ya sanya suku suka gaisa da juna ''don Allah a yafe wa juna, a kama hannun juna, gaba ta fi baya baya yawa, a yafe wa juna Allah ya yafe mana gaba ɗaya, sai ya kalli El-Rufai ya ce your Excellency an yafe ko''.
Sai El-Rufai ya ɗaga kai alamun ya amince, sai Sheikh Pantami ya ce ''yawwa an yafe wa juna'', sai mutanen da ke wurin suka yi kabbara.
Ko Sulhun zai ɗore?
Tun bayan yin wannan sulhu mutane suka riƙa tafka muhawara kan ko sulhun zai ɗore, ganin yanayin da lokaci da kuma wurin da aka yi shi.
Dr Kabiru Danladi Lawanti, Malami a Sashen Koyar da Aikin Jarida na Jami'ar Ahmadu Bello da ke Zariya ya ce baya ganin wannan sulhu zai ɗore sabod a cewar wannan ba ma sulhu ba ne.
''Wannan ba sulhu ba ne, abin da Sheikh Pantami ya yi shi ne kawai ya sa Uba sani da El-Rufai sun gaisa, amma ba sulhu ba'', in ji malamin jami'ar.
''Abin da ya yi shi muke kira 'Photo Of', wato ya sanya sun gaisa, an kuma ɗauka a wayoyi an dora a shafukan sada zumunta'', in ji mai koyar da aikin jaridar.
Don haka ya ce ''wannan abun ina mai tabbatar maka nan kwana uku ya wuce''.
Ya ƙara da cewa ba wannan wuri ya kamata a taso da maganar sulhu ba, kasancewar El-Rufai na cikin yanayin alahinin rashin mahaifiya.
"Shi kuma Uba Sani ya zo wurin ne a matsayinsa na Uba ga al'ummar jihar Kaduna, don haka ya je wurin ne a matsayin wakilin jihar Kaduna, don haka janaza ake yi ba sulhu ba'', in ji shi.
Ya ci gaba da cewa abin da ya kamata Sheikh Pantami ya yi shi ne ya kira su wani wuri daban, domin yi musu sulhu in hakan yake so, amma ba wannan wuri ba.
Wasu mutane da dama na ganin wannan dama ce da Pantami ya samu na haɗuwar mutanen wuri guda, kasancewar da wuya su iya samun kansu a wuri guda a wannan lokaci.
To amma Dr Lawanti ya ce matsayin Sheikh Pantami ya kai ya kira duka mutanen biyu duk wurin da yake so, ko Abuja ko Gombe domin yi musu sulhu.
''Sheikh Pantami babban malami ne da ake darajawa a ƙasar nan, tsohon ministan kuma stohon shugaban NITDA don haka ina ganin matsayinsa ya kai ya kira su duk wurin da yake so kuma za su je'', in ji shi.
Me ya shiga tsakanin El-Rufai da Uba Sani?
Mutanen biyu waɗanda a baya aminan juna ne a fagen siyasa, sun fara samun saɓani ne tun bayan sauyin gwamnati da kuma takun-saka da ta kunno kai bayan da Uba Sani ya hau kan kujerar gwamna.
Daga lokacin ne aka fara bijiro da batun binciken gwamnatin El-Rufa'i kan yadda gwamnatinsa ta kashe kuɗi a zamaninta.
Rashin jituwar tasu ta ƙara fitowa fili ne a 2025 lokacin wata hira da Uba Sani da ya yi gidan talbijin na TVC, hirar da ba ta yi wa El-Rufai daɗi ba.
A cikin hirar an tambayi Uba Sani kan mene ne ra'ayinsa kan batun masu neman yin haɗaka domin kifar da gwamnatin Tinubu.
Sai ya ce "zance na gaskiya shi ne, wasu mutane," ciki har da magabacinsa "na fitowa suna suka kan abubuwan da ba gaskiya ba".
A cewarsa waɗannan masu sukar ba sa ɗaukar su da wani muhimmanci saboda sun fahimci duk wannan fafutikar ta kashin-kai ce ba wai tausayin al'umma ba.
"Ai galibinsu sun yi mulkin shekara takwas kuma ba a ga wani abu na arziki ko rawar ganin da suka taka ba'', in ji shi.
Ya ci gaba da cewa "mutanen da ke ta bibiyar Tinubu ne a baya, amma saboda sun rasa samun shiga ko dama sai a koma suka''.
Waɗannan kalamai da Uba Sani ya ke yi wasu na ganin tamkar gugar-zana ce ga magabacinsa Malam Nasir El-Rufa'i.
Sai dai ba a jima da wannan hira ba El-Rufai ya mayar da martani a shafinsa na X, inda a ciki ya tabbatar da cewa ba sa jituwa da Uba Sani.
Domin kuwa a cikin saƙon nasa ya rubuta cewa, "a duk lokacin da na ga wannan gwamna ya fito yana ɓaɓatu da baza rashin basira da abin kunya, sai na shiga mamaki ya aka yi haka.
"Amma babu komai kuma wannan tayar da jijiyoyin wuya da Uba Sani ke yi saboda kuɗaɗen da gwamnatin Tinubu ta bai wa Kaduna na naira biliyan 150 a cikin watanni 18 ne, sai a fito a yi bayyani yadda aka yi da kuɗaɗen.
"An dage ana kare Asiwaju saboda kudaden da aka samu, Asiwaju ya ci riba, a kanka. Mutanen Kaduna za su yi hukunci a lokacin da ya dace a inda kuma ya dace."
Wanna martani da tsohon gwamnan ya mayar da ya ja hankalin al'umma tare da haifar da muhawara a shafukan sada zumunta.