Wace jam'iyya Kwankwaso zai koma bayan fitarsa daga NNPP?

Lokacin karatu: Minti 4

Tun bayan da tsohon gwamnan jihar Kano, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya sanar da ficewa daga jam'iyyarsa ta NNPP, masana da masu bibiyar siyasa ke ci gaba da hasashen jam'iyyar da zai koma.

Cikin sanarwar ficewar ta sa, Sanata Kwanwaso ya ce matakin ya zama tilas ne la'akari da yanayin siyasar Najeriya ke ciki ''wanda ke bukatar haɗin kai''.

''Matakin ya zama tilas domin haɗa kai da wasu jam'iyyun don kawo wa ƙasarmu sauyi nagari'', kamar yadda Kwankwason ya bayyana.

Tuni dai masana da masu sharhin siyasa suka fara bayayna hasashensu na inda Kankwason zai koma.

Wace jam'iyyar zai shiga?

Dr Kabiru Sufi masanin kimiyyar siyasa ya bayyana cewar ''zaɓin da ya rage wa Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso manyan jam'yyun ne guda biyu, kuma tun da ya nuna cewar ba shi da sha'awar shiga jam'iyya mai mulki ta APC, don haka akwai hasashen zai koma jam'iyyar hamayya ta ADC kenan'' .

Ya ƙara da cewa a halin yanzu batu ake na haɗuwa don a tunkari jam'iyya mai mulki.

''Duk da ana ganin za su iya fuskantar ƙalubalen yin takara a tsakanin su, amma da wuya bai koma ADC ba'', in ji shi.

Yayin bukukuwan sallah dai an ga Peter Obi da Seyi Makinde da Seriake Dickson daga mabanbantan jam'iyyu sun kai wa Kwankwaso ziyara a gidansa da ke Kano.

''Hakan na nufin wataƙila su jiga-jigan jam'iyyar hamayya suna da shirin ɗinkewa kuma ko da an yi zaɓe za su iya haƙura da wanda ya yi nasara'', kamar yadda ya yi ƙarin haske.

Wane tasiri Kwankwaso zai yi a ADC?

Yayin da jam'iyyar ƙawancen ƴan hamayya ta ADC ke ci gaba da samun karɓuwa daga wasu ƴansiyasar ƙasar ana ganin zuwan Kwankwaso zai yi matuƙar tasiri ga jam'iyyar.

Dr Kabiru Sufi ya ce tasirin da zai yi shi ne zai iya kawo ɗimbin ƙuri'un da ake ganin akwai a jihar Kano.

Jihar Kano ce kan gaba a yawan samar da ƙuri'u a zaɓen shugaban ƙasa a Najeriya.

''Kuma mafi yawan ƙuri'un da ake samu daga a zaɓukan shugaban ƙasa da suka gabata, Kwankwaso da na matuƙar tasiri wajen samar da su'', kmar yadda ya bayyana.

A zaɓen 2023 da ya gabata Kwankwaso - wanda ya tsaya takarar shugaban ƙasa a NNPP ya samu fiye da ƙuri' miliyan guda daga jihar, wadda tafi kowa yawan al'umma.

Don haka ne Dr Kabiru Sufi ya ce tasirin da zuwansa ADC zai yi wa jam'iyyar shi ne samun ƙuri'un Kano, ''kada ta yi sakaci da jam'iyya mai mulki ta kwashe su''.

Masanin siyasar ya ci gaba da cewa da wannan ake ganin Kwankwaso da Nasir El Rufa'i za su iya bayar da gudummawa daga Arewa maso Yamma.

Me ya sa ba zai shiga APC ba?

An dai jima ana alaƙanta Kwankwaso da komawa jam'iyyar APC mai mulki tun kafin rantsar da gwamnatin Tinubu.

A wata ganawa da Kwankwaso ya yi a Tinubun a Faransa gabanin rantsar da shi a 2023 da alƙawarin da ya yi na aiki da ƴan adawa, ya sa aka riƙa tunanin zai shiga ƙunshin gwamnatin idan an rantsar da ita.

Haka aka riƙa wannan hasashe a tsawon shekara uku da gwamnatin Tinubu ta kwashe amma har yanzu Kwankwason bai shiga APC ba.

Ficewarsa daga NNPP ya sabunta wannan zargi, to amma Dr Sufi ya ce ko kaɗan Kwankwanso ba zai shiga APC ba.

Ko a sanarwarsa ta ficewa daga NNPP kwankwaso ya ce zai koma wata jam'iyya ce da za ta ba shi damar kawo sauyi a siyasar Najeriya.

''Ba na tunanin zai shiga APC a wannan gaɓa, saboda abubuwan da suka faru a baya-bayan nan'', in ji shi.

Masanin siyasar ya ci gaba da cewa ana ganin rashin daidaitawa da gwamnan Kano na daga cikin dalilan da za su hana Kwankwaso shiga jam'iyya mai mulki.

''Inda a ce sun tafi tare zai fi armashi amma kuma sai bayan gwamna ya tafi shi kuma Kwankwaso ya shiga APCn daga baya shigar ba za ta yi kwarjinin siyasa ba'', in ji shi.

Kwankwanso a siyasar Najeriya

Tsohon gwamnan jihar Kanon, Rabi'u Musa Kwankwaso na ɗaya daga cikin ƴan siyasa a arewacin Najeriya da suka daɗe suna tasiri, musamman saboda yadda ya shiga zuciyar matasa.

Ana dai ganin tun bayan Malam Aminu Kano ba a sake samun wani ɗan siyasa ba da ya fito da wani tsari na siyasa a arewa da ya saka wa suna, kuma yake da mabiya na ga-ni-kashe-ni, sai Kwankwason.

Kwankwaso ne jagoran aƙidar siyasa mai suna ɗarikar Kwankwasiyya da mabiyanta ke saka jar hula.

Bayan kammala wa'adinsa ne ya tsayar da mataimakinsa, Abdullahi Umar Ganduje, wanda ba a daɗe ba, suka samu saɓani aka raba-gari.

Wannan ya sa a lokacin da Ganduje yake neman wa'adi na biyu, Kwankwaso ya tsayar da Abba Kabir Yusuf a zaɓen 2019, amma Ganduje ya kayar da shi bayan an yi zaɓen cike gurbi a garin Gama.

Har ila yau, Kwankwaso ya tsayar da gwamnan Kano mai-ci, Abba Kabir Yusuf inda ya kayar da ɗantakarar gwamna mai barin gado, Nasiru Yusuf Gawuna na jam'iyyar APC mau mulkin jihar a lokacin.