Yadda APC ta zaɓi shugabanninta ta hanyar maslaha

Lokacin karatu: Minti 2

Jam'iyyar APC mai Mulki a Najeriya ta kammala babban taron ta karo na takwas, inda aka zaɓi shugabanta na riƙo Nentawe Yilwatda domin ci gaba da jan ragamar shugabancin ta.

Taron ya kuma zaɓi Surajudeen Basiru a matsayin sakataren jam'iyyar na ƙasa.

Wakilai daga sassan Najeriya ne suka amince da sabon wa'adin shugabancin jam'iyyar, ta hanyar amfani da tsarin maslaha ba tare wata jayayya ba.

Yadda shugaban kwamitin tsara babban taron jam'iyyar APC na ƙasa, kuma tsohon gwamnan jihar Katsina Aminu Bello Masari ya sanar da amincewa da sabon wa'adin shugabancin jam'iyyar kenan, a yayin taron da aka yi jiya da dare.

Da wannan sanarwa dai, da kuma amincewa da kama aiki daga shugabannin suka yi, jam'iyyar APC ta ci gajiyar hanyar maslaha wajen miƙa ragamar shugabancinta ga waɗanda za su jagorance ta zuwa zaɓen 2027.

Taron wanda ya gudana a dandalin Eagle Square a birnin Abuja, ya tara duk wani mai faɗa a ji, a cikin gidan jam'iyyar APC a Najeriya, ciki harda shugaba Tinubu da mataimakinsa Kashim Shettima, da gwamnoni da ƴan majalisu da kuma sauran masu ruwa da tsaki.

Mohammed Idris, shi ne ministan yaɗa labaran Najeriya, kuma ya ce taro ya tafi yadda aka tsara.

Shugaba Tinubu ya yi amfani da taron wajen tabbatar wa ƴan Najeriya cewa yana sane da ƙorafin su game da hanyar da ya ɗauka domin kawo gyara.

Ya ce "Mun sani cewa sake gina Najeriya zai buƙaci ƙarfin hali, da haƙuri, da kuma yanke shawara ɗaukar matakai masu wahala. Amma kuma muna sane cewa babu wata ƙasa da za ta ci gaba ta hanyar ɓoyewa kai gaskiya. Dole ne mu kaucewa yaudarar kanmu, dole mu gina gagarumar ƙasa ga jikokinmu kafin zuwan su, dole ne tubalin wannan gini ya zamo mai ƙarfi kuma na musamman wanda zai jure ƙalubalen zamani."

Shuagaban Najeriyan ya ce ko a yanzu, a bayyane take cewa gwamnatin APC ta kama hanya madaidaiciya don kai ƙasar ga gaci.

Su ma wasu daga cikin mambobin jam'iyyar APC da suka halarci taron sun bayyana gamsuwa da yadda abubuwa suka kasance.

Jam'iyyar APC dai ta ce wakilai fiye da dubu takwas ne daga sassan Najeriya suka halarci wannan taro, kuma ta jaddada matsayar ta cewa ta shirya fafatawa a kowane matakin zaɓe ba tare da wata fargaba ba.

Kammala wannan taro cikin nasara dai wani ƙalubale ne ga jam'iyyun adawa a Najeriya, waɗanda su ma ake jiran ganin yadda nasu tarukn za su kasance, musamman yadda suke ta shan alwashin kawar da gwamnatin APCn, duk da jan hankalin da masana harkokin siyasa ke yi cewa su ma akwai ɓaraka a cikin gidajen su.