Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Abubuwan da APC ke fatan cimmawa a taronta na ƙasa
Ƴaƴan jam'iyyar APC mai mulkin Najeriya na ci gaba da tururuwa zuwa Abuja, babban birnin ƙasar, domin halartar babban taronta na ƙasa da ake shirin gudanarwa tsakanin ranar Juma'a 27 zuwa Asabar 28 ga watan Maris na 2026.
Ana sa ran shugaban ƙasar Bola Tinubu da mataimakinsa da muƙarraban gwamnatinsa da ma gwamnonin jam'iyyar 32 ne za su halarci taron jam'iyyar.
Baya ga waɗannan ana sa ran shugabanninin jam'iyyar na shiyya-shiyya da na jihohi da ƙananan hukumomi da aka zaɓa a baya-bayan nan ne za su halarci babban taron, wanda za a zabi sabbin shugabannin jam'iyyar a matakin ƙasa.
Wakilai daga sassan ƙasar daban-daban fiye da 8,000 ne ake sa ran za su halarci taron.
Wannan ne karo na takwas da jam'iyyar ke gudanar da babban taronta na ƙasa tun bayan kafuwarta a shekarar 2013.
Me taron ke son cimmawa?
BBC ta tattauna da Mallam Bala Ibrahim, daraktan yaɗa labarai na jam'iyyar, wanda ya bayyana abubuwan da APC ke son cimmawa a taron nata.
Ya ce akwai abubuwa muhimmai da taron zai mayar da hankali a kai da suka haɗa da waiwaye kan manufofin jam'iyyar.
''Sannan za a yi waiwaye kan matsalolin da aka samu a shekarun da suka gabata, da yadda aka tunkari matsalolin domin shawo kansu'', in ji shi.
Ya kuma ce za a yi nazarin ƙalubalen da jam'iyyar ba ta iya shawo kansu ba domin sanin yadda za a tunkare su.
Zaɓen sabbin shugabanni
Darakta yaɗa labaran jam'iyyar ya ce babban abin da zai ɗauki hankali a taron shi ne zaɓen sabbin shugabannin jam'iyyar da za su ja ragamarta nan da shekara hudu masu zuwa.
Tun bayan saukar Sanata Abdullahi Adamu daga shugabancin APC a watan Yulin 2023, jam'iyyar ke amfani da shugabannin riƙo a matsayin jagorrinta.
Da fari ta naɗa Abdullahi Umar Ganduje a matsayin shugaba riƙo a farkon watan Agustan 2023, kafin ya sauka a watan yunin 2025 saboda dalilai na rashin lafiya, kamar yadda ya bayyana.
Bayan saukar Ganduje ana naɗa Ali Bukar Dalori matsayin shugaban riƙa, kafin sanar da Farfesa Yilwatda Nentawa a matsayin shugaban riƙo shi ma.
Nazarin alƙawuran da APC ta ɗauka a baya
Kakakin jam'iyyar ya kuma shaida wa BBC cewa taron na yau zai kuma yi nazarin alƙawuran da jam'iyyar ta ɗauka na warware wa ƴan ƙasa matsalolinsu.
''Za a duba a gani ko jam'iyyar ta samu nasarar warware wa ƴan ƙasa matsalolin da ta yi alƙawarin magance musu'', in ji shi.
Ya kuma ƙara da cewa taron zai yi nazarin tafiyar da jam'iyyar ta yi a cikin gwamnati, domin tabbatar da cewa tafiyar ta yi daidai da manufofin jam'iyyar.
Amfani da maslaha wajen zaɓen shugabanni
Jam'iyyar ta tabbatar da cewa za ta fara amfani da masalaha wajen zaɓen sabbin shugabannin nata.
A cewar Bala Ibrahim APC ƙarƙashin jagorancin shugaban ƙasar Bola Tinubu na fara la'akari ne da hanyar masalaha a kowane mataki.
''Idan za a iya samun masalaha to ba sai an je ga jefa ƙuri'a ba, da har a wasu lokuta zai kai ga samun hagaga ba'', kamar yadda ya yi ƙarin haske.
To amma ya ce a wurin da masalahar ta gagara jam'iyyar za ta yi amfani da hanyar ƙuri'a domin zaɓar sabbin shugabannin.
Su wane ne manyan ƴantakara?
Tuni dai jam'iyyar APC ta sanar da keɓe wa kudancin ƙasar takarar shugabancin ƙasar a shekarar 2027.
Don haka bisa ga tsarin jam'iyyar shugaban jam'iyyar zai fito ne daga yankin arewacin ƙasar.
Kuma bisa ga rabon muƙaman jam'iyyar shiyyar arewa tsa tsakiyar ƙasar ne aka ware wa muƙamin shugaban jam'iyyar.
Tuni dai kwamitin tantance ƴantakara ya tantance shugaban riƙon jam'iyyar na yanzu, Farfesa Yilwatda Nentawe domin tsayawa takarar shugabancin jam'iyyar.
Haka ma wasu rahotonni na ambato sakataren gwamnatin tarayya, Sanata Gorge Akume da tsohon gwamnan Nasarawa, Sanata Tanko Almakura a matsayin waɗanda ke sha'awar muƙamin.
Ana sa ran duk wanda aka zaɓa a matsayin sabon shugaban jam'iyyar zai riƙe ta har nan da shekara huɗu masu zuwa, in dai ba wata matsala ta taso ba.
Yadda APC ta samu gagarumin rinjaye a siyasar Najeriya
Jam'iyyar APC ta kasance kan gaba a tarihin siyasar Najeriya da ta samu gagarumin rinjaye.
Yanzu haka jam'iyyar ce ke mulki a jihohi 32 cikin jihohin ƙasar 36.
Gwamnonin jam'iyyun adawa da dama ne suka sauya sheƙe daga jam'iyyunsu domin komawa cikin jam'iyyar, musammam tsakanin shekarar 2025 zuwa 2026.
Gwamna na baya-bayan nan da ya koma jam'iyyar shi na Zamfara, Dauda Lawal, wanda ya fice daga PDP.
Haka kuma jam'iyyar ta APC na da gagarumin rinjaye a majalisar dattawa da ta wakilan ƙasar, ta yadda za ta iya zartar da da muhimman ƙudurorin da take buƙata.
Tsoffin shugabannin jam'iyyar
- Chief Bisi Akande - (2013–2014).
- Chief John Odigie-Oyegun - (2014- 2018)
- Comrade Adams Oshiomhole - (2018 - 2020)
- Mai Mala Buni - (2020-2022)
- Abdullahi Adamu (2022 - 2023)
- Abdullahi Ganduje - (2023 - 2025)
- Farfesa Yilwatda Nentawe ( 2025 zuwa yanzu)