Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Yadda sulhu da ƴanbindiga ya janyo rikici tsakanin ƙauyukan Zamfara
Sulhu da wasu al'ummomi ke yi tsakaninsu da ƴanbindiga a Jihar Zamfara da ke Arewa maso yammacin Najeriya ya haifar da wani sabon rikici tsakanin al'ummar wasu kauyuka biyu a yankin ƙaramar hukumar Kauran Namoda, lamarin da har ya kai ga rasa rai.
Saɓanin ya kai ga ƙauyukan da ke makwabtaka da juna sun shata iyaka tsakaninsu tare da yi wa juna barazanar kisa, sakamakon yadda ɗaya ɓangaren ke zargin ɗaya da zama mafakar ɓarayin daji.
Rikicin ya shafi ƙauyukan Madira da kuma ƙauyen Yankaba masu maƙwabtaka da juna, a ƙaramar hukumar Kauran Namoda da ke jihar Zamfara.
Mazauna ƙauyen Madira dai sun yi zargin cewa an kashe masu mutane saboda sun yi sulhu da ƴanbindiga.
Su kuma al'ummar ƙauyen Yankaba suka yi zargin cewa ana tsallakowa daga Madira ana kashe mutanensu.
Wannan dambarwa dai ta janyo yanke alaka tsakanin ƙauyukan biyu maƙwabtan juna.
Wata mata da aka kashe ɗan uwanta a rikicin ta shaidawa BBC yadda aka tare ƴan uwanta nata biyu a Yankaba lokacin da suke kan hanyar su ta komawa Madira daga Kauran Namoda, lamarin da ya yi sanadiyyar mutuwar ɗaya daga cikin su, ɗayan kuma ke kwance a asibiti inda ya ke jinyar ciwon da aaka ji mashi.
''Suna hanya sai mutanen garin Yankaba suka rufe su da duka, sai ɗayan ya ruga da gudu, kuma suka bi shi suka harbe shi kuma suka sassare shi, suka kashe shi. Shi ma wannan da yake asibiti sun harbe shi a ciki, shi ma sun barshi a matsayin gawa ne.'' in ji matar.
Ta kuma roƙi gwamnatin tarayya da ta jihar Zamfara su shiga lamarin domin kawo ƙarshen rikicin.
Shi ma maigarin Madira, Alhaji Bala, ya ce sanadiyyar sulhu da ƴanbindiga, sai mutanen Yankaba suka ɗauka cewa mutanen Madira sun zama abokan gabar su, ''Saboda haka ko mutumin Madira suka gani, to abin da suke ganin ya fi, sai su kashe shi.''
Ya yi bayanin cewa rikicin ya taso ne bayan an yi faɗa tsakanin mutanen Yankaba da ƴanbindiga a bakin gulbi, lamarin da ya kai ga kisan mutum biyu dag cikin mutanen garin.
''su kuma mutanen Madira sun zo wucewa kawai sai jama'ar Yankaba suka far masu...ga mutanen Madira nan, ga mutanen Madira nan!'' in ji Alhaji Bala.
Ya ce tuntuni a matsayin su na jagorori suka shaidawa mutanen Yankaba cewa idan akwai wanda suke ganin cewa yana da hannu a ayyukan ƴanbindiga, daga cikin ƴan Madira, to su bayyana shi domin samun hanyar magance matsalar.
Ya yi bayanin cewa sun kai maganar har gaban sarki, kuma ya shiga tsakani inda ya nemi su zauna lafiya da juna.
Daga nasu ɓangaren mazauna ƙauyen Yankaba sun yi bayanin yadda ake ciki, kamar yadda wani mazaunin ƙauyen ya shaidawa BBC ''su (Ƴan Madiga) sun yi sulhu da su ne, mu kuma ɓarayin sun nemi a yi sulhu da su, amma mu ƴan nan garin ba su yarda ba,''
Ya ƙara da cewa an ja layi a tsakani ''ta yadda ɗan can baya zuwa nan, ɗan nan kuma baya zuwa can''
''To kuma sai ya zamo ƴan wancan garin sai sun bi ta hanyar garinmu sannan su shiga nasu garin, lamarin da ya janyo rikici.
Jihar Zamfara ta daɗe tana fama da matsalar ƴan fashin daji masu kashewa da satar mutane, kuma duk ƙoƙarin da jami'an tsaro ke cewa suna yi, ƴanbindiga na tilasta wa mutanen ƙauyukan yin sulhu da su kafin su samu walwala ta zuwa gonaki da kasuwa.
'Ba za mu yi sulhu da ƴanbindiga ba'
Daga cikin manyan abubuwan da suka daɗe suna jan hankali a jihar Zamfara akwai batun sulhu da ƴanbindiga a jihar.
Gwamnan jihar Dauda Lawan ya daɗe yana cewa zai iya yin sulhu da ƴanbindiga da ke addabar jihar ne kawai idan har sun ajiye makamansu.
Batun yin sulhu da ƴanbindiga lamari ne da ke haifar da zazzafar muhawara a Najeriya, bayan shafe sama da shekara 10 ana fama da ayyukan ƴan fashin daji a arewa maso yammacin Najeriya, lamarin da ya yi sanadiyyar rasa dubban rayuka da tarwatsa al'umma da durƙusar da ilimi da kasuwanci.
A wata hirarsa da BBC, Gwamna Dauda ya bayyana cewa "Akwai da yawa waɗanda aka cutar da su, wasu an kashe iyayensu wasu matansu, saboda haka sai a duba me za a yi masu saboda sun rasa dukiyarsu, ba wai kullum a riƙa fitfita ƴanbindiga ba," in ji Dauda.
Ya ƙara da cewa sai ƴanbindigar sun daina kashe mutane kuma sun ajiye makamansu sannan za a iya yin sulhu da su.
A baya dai, Gwamnan jihar Zamfara Dauda Lawal Dare ya sha nanata cewa har abada ba zai yi sulhu da ƴan fashin daji ba.
Yayin zantawarsa da BBC gwamnan ya ce ya ɗauki wannan matsaya ce ganin cewa a bayan an sha yin sulhu da 'yan bindigar, amma ba sa mutunta alƙawurran da aka yi da su a baya.