Makaman linzamin Iran sun faɗa tsakiyar Isra'ila
Wasu makaman Iran masu linzami sun faɗa yankin Beit Shemesh da ke tsakiyar Isra'ila.
Hare-haren sun haifar da wani wawagegen rami a wurin da lamarin ya faru, inda suka lalata gine-gine da motoci da kuma kayan jami'an agajin gaggawa da ke wurin.
‘Yan sandan Isra’ila sun ce faɗuwar makaman a kusa da tsaunin Judean da ke kusa da Birnin Kudus ya raunata mutane 12.
Jami'ai da masu sa kai na ci gaba da aiki a wurin.
Jaridar Times ta Isra'ila bayar da rahoton cewa, rundunar sojin saman ƙasar za ta binciki gazawar na'urar kakkaɓo makaman ƙasar wajen kakkaɓo waɗannan makaman.
A wani labarin kuma rundunar sojin Isra'ilar ta ce tana ƙoƙoƙarin kakkaɓo wasu makaman linzami da Iran ta tarba cikin ƙasar.