Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassana duniya, Asabar 28/03/2026

Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassana duniya, Asabar 28/03/2026

Taƙaitattu

Rahoto kai-tsaye

Abdullahi Bello Diginza

  1. Makaman linzamin Iran sun faɗa tsakiyar Isra'ila

    bayan hari

    Asalin hoton, Getty Images

    Wasu makaman Iran masu linzami sun faɗa yankin Beit Shemesh da ke tsakiyar Isra'ila.

    Hare-haren sun haifar da wani wawagegen rami a wurin da lamarin ya faru, inda suka lalata gine-gine da motoci da kuma kayan jami'an agajin gaggawa da ke wurin.

    ‘Yan sandan Isra’ila sun ce faɗuwar makaman a kusa da tsaunin Judean da ke kusa da Birnin Kudus ya raunata mutane 12.

    Jami'ai da masu sa kai na ci gaba da aiki a wurin.

    Jaridar Times ta Isra'ila bayar da rahoton cewa, rundunar sojin saman ƙasar za ta binciki gazawar na'urar kakkaɓo makaman ƙasar wajen kakkaɓo waɗannan makaman.

    A wani labarin kuma rundunar sojin Isra'ilar ta ce tana ƙoƙoƙarin kakkaɓo wasu makaman linzami da Iran ta tarba cikin ƙasar.

    bayan hari

    Asalin hoton, Reuters

  2. Mun kakkaɓo makaman linzami 20 da jirage marasa matuƙa 37 - UAE

    Ma'aikatar tsaron ƙasar Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa ta ce ta kakkaɓpo jirage marasa matuƙa 37 da makamai masu linzami 20.

    Ƙasar ta ce tun bayan fara yaƙin Iran ta kakkaɓo makaman linzami fiye da 40 da jirage marasa matuƙa fiye da 1,800 da Iran ta harba mata.

    A cewar ma'aikatar tsaron ƙasar, hare-haren sun haddasa mutuwar 11 ciki har da jami'an sojin ƙasar biyu da wani farar hula ɗan Moroco da ke yi wa sojojin ƙasar aikin kwantiragi.

    Iran na kai hare-hare kan makwaɓtan ƙasashe a matsayin martanin hare-haren da Amurka ke kai musu.

  3. Rasha ke bai wa Iran bayanan sirri kan sansanonin sojin Amurka - Zelensky

    Zelensky

    Asalin hoton, Getty Images

    Shugaban Ukraine Volodymyr Zelensky ya zargi Rasha da taimaka wa Iran da bayanan sirri kan hare-haren da take kai wa sansanonin sojin Amurka a yankin Gabas ta Tsakiya da ma harin da ta kai sansanin haɗin gwiwar Amurka da Birtaniya da ke Diego Garcia

    Yayain da yake zantawa da manema labarai, Mista Zelensky ya karanta wani abu daga wayarsa, wanda ya yi iƙirarin cewa rahoton bayanan sirri ne da ke cewa tauraron ɗan'adam Rasha na leƙen asiri kan sansanonin sojin Amurka a Gabas ta Tsakiya da na Diego Garcia.

    Zelensky ya ce waɗannan bayanan sirrin ne ake bai wa Iran waanda kje taimaka mata wajen hare-haren da take kai wa.

    A wani labarin kuma Ukraine ta ƙulla ƙawancen tsaro da Qatar domin musayar fasahar jirage masara matuƙa.

  4. Tsagin Wike na PDP zai gudanar da babban taronsa na ƙasa a ranar Lahadi

    Wike

    Asalin hoton, others

    Babban jam'iyyar hamayyar Najeriya PDP tsagin Nyesom Wike zai gudanar da babban taronsa na ƙasa a ranakun Lahadi da Litinin.

    Jam'iyyar PDP - wadda ke fama da rikice-rikicen cikin gida - na ƙoƙarin ɗinke ɓarakarta da ƙwatar mulki a hannun APC mai mulki.

    Yuni dai tsagin Kabiru Tanimu Turaki na jam'iyyar ya garzaya kotun Kolin ƙasar da nufin dakatar da hukuncin da ya kwace masa iko da jam'iyyar.

    Ministan Abuja, Nyesom Wike, wanda ya ziyarci babban filin wasa na ƙasa, inda ake shirye-shiryen gudanar da tarin, ya tabbatar da cewa za a gudanar da taron duk kuwa da ƙoƙarin sansantawa da ɓangarorin biyu ke yi.

    Wike ya ce ana sa ran wakilai kusan 2,500 ne za su halarci babban taron, wanda a nan ne za a zaɓi sabbin shugabannin da za su jagorancin jam'iyyar mam da shekara huɗu masu zuwa.

    PDP ta faa rikici ne tun gabanin zaɓen fitar da gwanin shugaban ƙasa na 2023, lamarin da ya sa wasu ƴaƴan jam'iyyar suka yi fushi.

    Haka ma bayan zaɓen jam'iyyar ta rasa mafi yawan gwamnoninta, waɗanda suka koma APC sanadiyyar rikicin jam'iyyar.

    Yanzu dai gwamnoni biyu ne kawai suka rage wa jam'iyyar.

  5. Isra'ila ta ƙaddamar da sabbin hare-hare kan Iran

    Isra'ila ta ƙaddamar da sabbin hare-hare ta sama kan Iran yayin da yaƙin ke shiga wata na biyu.

    Harin da Isra'ila ta kai birnin Zanjan da ke arewa maso yammcin ƙasar ya kashe aƙalla mutum biyar da ke tunanin ƴan gida ɗaya ne.

    Duk da jinkirta hare-hare kan cibiyoyin fararen hula na Iran da Donald Trump, Isra'ila ta ƙaddamar da hare-hare kan cibiyoyin kamfanoni da masana'antar ƙarafa da ke lardin Isfahan.

    Tuni dai Iran ta sha alwashin ɗaukar fansa kan hare-haren.

    Rundunar juyin juya halin ƙasar ma muma shakku game da ƙoƙarin Pakistan na kawo ƙarshen yaƙin.

  6. Pakistan za ta tattauna da Saudiyya,Turkiyya da Masar don kawo ƙarshen yaƙin Iran

    Ministan harkokin wajen Pakistan, Ishaq Dar ya ce ƙasarsa za ta karɓi baƙuncin tattaunawar ministaocin harkokin wajen ƙasashen Saudiyya da Turkiyya da kuma Masar a Islamabad daga gobe Lahadi zuwa Litinin.

    Cikin wata sanarwa a ya wallafa a shafinsa na X Mista Dar ya ce ministaocin za su yi ''tattaunawa mai zurfi'' kan yunƙurin ''kawo ƙarshen rikicin yankin Gabsa ta Tsakiya''.

    Tuni dai ma'aikatar harkokokin wajen Masar ta sanar cewa ministan harkokin wajen ƙasar ya tafi Pakistan domin halartar tattaunawar.

    Pakistan na yunƙurin zama mai shiga tsakani don kawo ƙarshen yaƙin Iran.

    A gefe guda ƙasar ta yi tayin karɓar baƙuncin tattaunawa tsakanin Amurka da Iran don kawo ƙarshen yaƙin, kodayake babu tabbaci ko za a yi wannan zama.

    A cikin makon nan ne Shugaba Trump ya wallafa wani saƙo a shafinsa na sada zumunta da a ciki Firaministan Pakistan ke cewa ƙasar a shirye take don shiga tsakani.

  7. Tinubu ya jajanta wa El-Rufai kan rasuwar mahaifiyarsa

    Tinubu da El-Rufai

    Asalin hoton, Others

    Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya aike da saƙon ta'aziyyarsa ga tsohon gwamnan jihar Kaduna da iyalansa, Mallam Nasir El-Rufai game da rasuwar mahaifiyarsa, Hajiya Umma da ta rasu ranar Juma'a.

    Cikin saƙon ta'aziyyar da ya fitar, Shugaba Tinubu ya bayyana marigayiyar a matsayin wadda ta cimma nasara a rayuwa wajen renon ƴaƴa da jikokin da suka taimaka wajen gina Najeriya.

    “Ina miƙa ta'aziyya ga El-Rufai da iyalansa kan wannan rashi, a matsayin wanda ni ma na rasa mahaifiyata na sa irin raɗaɗin da rashin mahaifiya ke da shi'', in ji Tinubu.

    Ya ce rasuwar mahaifiya na da ciwo fiye da komai, don haka ya yi addu'ar haƙurƙurtar da iyalanta game da rashinta.

    Hajiya Umma ta rasu en ranar Juma'a da daddare a wani asibiti da ke birnin Alƙahirar Masar, inda ta yi fama da jinya.

  8. 'An kai harin jirgi maras matuƙi babban filin jirgin saman Kuwait'

    Kakakin ma'aikatar harkokin sufurin jiragen sama na Kuwait ya ce an kai hare-haren jirage marasa matuƙa kan babban filin jirgin sama na ƙasar, kamar yadda kamfanin dillancin labaran KUNA ya ruwaito.

    Hukumomin na Kuwaita sun ce hare-haren sun lalata ɗakin da ake kula da zirga-zirgar jirage a filin jirgin, amma dai babu labarin rasa rai.

    Ba wannan ne karn farko da ake kai irin waɗannan hare-haren ba.

    Ko a ranar Laraba ma wani harin jirgi maras matuƙi na Iran ya faɗa kan rumbun ajiyar mai na filin jirgin ƙasar.

  9. Su wane ne sabbin shugabannin da APC ta zaɓa?

    Nentawe

    Asalin hoton, Nentawe Media Advocates

    Jam'iyyar APC mai mulkin Najeriya ta zaɓi sabbin shugabannin da za su jagorance har an da shekaru huɗu masu zuwa.

    An zaɓi sabbin shugabbnin ne a lokacin babban taron jam'iyyar na ƙasa da aka gudanar ranar Juma'a a Abuja.

    APC ta sanar da zaɓen Farfesa Nentawe Yilwatda - shugaban riƙon jam'iyyar - a matsayin cikakken shugabanta na ƙasa.

    Haka kuma jam'iyyar ta tabbatar da Surajudeen Basiru a matsayin cikakken sakataren jam'iyyar na ƙasa.

    An dai zaɓi mafi yawan jagororin jam'iyyar ta hanyar masalaha, kamar yadda jam'iyyar ta fi bai wa fifiko.

    Ga jerin sunayen sabbin jagororin jam'iyyar:

    • Shugaban Jam'iyya na ƙasa: Farfesa Nentawe Yilwatda
    • Mataimakin Shugaba (Arewa): Ali Bukar Dalori
    • Mataimakin Shugaba (Kudu): Dr. Benjamin Obi Nwoye
    • Sakataren Jam'iyyar na ƙasa: Sen. Surajudeen Ajibola Basiru
    • Mataimakin Sakatare: Prof. AbdulKarim Abubakar Kana
    • Babban Lauyan Jam'iyya: Murtala Aliyu Kankia
    • Babban Ma'aji na ƙasa: Uguru Mathew Ofoke
    • Babban Sakataren Kuɗi: Amb. Haruna Ginsau
    • Babban Sakataren tsare-tsare: Muhammad Sulaiman Argungu, OFR
    • Sakataren Walwawa: Donatus Enyinnah Nwankpa
    • Sakataren Yaɗa Labarai: Felix Morka
    • Babban Mai Binciken kuɗi: Sen. Abubakar Maikafi
    • Shugabar Mata: Dr Mary A. Idele
    • Shugaban Matasa: Dayo Israel
  10. Ƴantawayen Houthi sun ƙaddamar da hari kan Isra'ila

    Houthi

    Asalin hoton, Getty Images

    Ƴantawayen Houthi da ke samun goyon bayan Iran sun tabbatar da kai hari kan Isra'ila karon farko tun bayan fara yaƙin Amurka da Isra'ila da kuma Iran.

    Ƙungiyar ta ce ta harba makamai masu linzami kan ''wuraren sojin Isra'ila masu muhimmanci'' a matsayinm martanin kai wa Iran da Lebanon da Iraƙi da kuma yankunan Falasɗinawa hare-hare.

    Houthi ta ce za ta c gaba da kai ''hare-hare'' ta kowane ɓangare.

    Sanarwar ƙungiyar na zuwa ne bayan da sojojin Isra'ila suka sanar da kakkaɓo makamai masu linzami daga Yemen.

  11. Trump ya sake sukar mambobin NATO kan yaƙin Iran

    Donald Trump

    Asalin hoton, Getty Images

    Shugaban Amurka, Donald Trump, ya sake sukar mambobin ƙungiyar tsaro ta NATO, kan ƙin bayar da tallafin soji a yaƙin Iran.

    Yana mai cewa nan gaba, ita ma Amurka na iya rama biki.

    Da yake jawabi ga masu zuba jari a birnin Miami, Mista Trump ya ce: “Me ya sa za mu ba su gudummawa alhalin mu sun juya mana baya'' .

    Tun bayan da Amurka da Isra’ila suka ƙaddamar da hare-hare kan Iran a watan da ya gabata, Mista Trump ke nuna ƙarin rashin jin daɗinsa game da yadda ƙasashen yamma ke jan ƙafa wajen tura dakarunsu domin taimakawa wajen sake buɗe mashigin Hormuz.

    Ya dage kan cewa Iran na ɗanɗana kuɗarta, kuma tana son a ƙulla yarjejeniya ido rufe.

  12. 'Harin Iran ya jikkata sojojin Amurka 12 a Saudiyya'

    Trump

    Asalin hoton, Getty Images

    Rahotanni sun ce wani harin makami mai linzami daga Iran ya jikkata sojojin Amurka 12 a wani sansanin soji da ke Saudiyya.

    Jami’ai sun shaida wa abokiyar hulɗar BBC, wato CBS, cewa wasu daga cikin sojojin sun samu munanan raunuka a sansanin jiragen sama na Yarima Sultan.

    Harin ya kuma lalata wasu jiragen sojin saman Amurka da dama.

    A gefe guda Iran ɗin na ci gaba da kai sabbin hare-haren makamai masu linzami kan Isra’ila.

    Wani mutum ya mutu cikin dare a yankin Tel Aviv.

    Haka kuma, Hadaddiyar Daular Larabawa ta ce garkuwar tsaron sararin samaniyarta, ta kakkabo makamai da dama.

  13. Sallama

    Masu bin shafin shafin BBC Hausa kai-tsaye barkanmu da safiyar wannan rana ta Asabar.

    Sannunmu da sake haɗuwa a wannan rana domin ci gaba da kawo muku sabbin labarai.

    Ku ci gaba da bibiyarmu a shafukanmu na sada zumunta, domin tafka muhawara kan labaran da muke wallafawa.