Yadda ake zargin Rasha da ingiza zanga-zangar ƙin jinin gwamnati a Angola

    • Marubuci, Maria Jevstafjeva
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Global Disinformation Unit
    • Marubuci, Ilya Barabanov & Investigations Team
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Russian
    • Marubuci, Leandro Prazeres
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Brasil
  • Lokacin karatu: Minti 5

Wasu ƴan Rasha biyu na shirin fara fuskantar shari'a a Angola kan zargin ingiza zanga-zangar ƙin jinin gwamnati, inda suka riƙa yaɗa ƙarya da kuma ƙoƙarin katsalanda a zaɓen shugaban ƙasar da ke tafe a shekara mai zuwa.

An kama Igor Ratchin da Lev Lakshtanov a watan Agustan bara inda suke fuskantar tuhume-tuhume 11, ciki har da ta'addanci, leƙen asiri da sauransu.

BBC ta samu kwafin tuhumar da ake yi wa mutanen wanda ya ƙunshi har da wani shiri na sauya alƙiblar siyasar Angola.

Lauyoyin Rasha sun ƙalubalanci tuhumar kan cewa babu ƙwararan hujjoji.

A cewar zarge-zargen, ƴan Rashar sun yi aiki a matsayin wakilai ga wata ƙungiyar masu tattara bayanan sirri a Afirka waɗanda suka fito daga ƙungiyar sojojin hayar Rasha Wagner wadda babu ita yanzu, bayan mutuwar wanda ya kafa ta Yevgeny Prigozhin a hatsarin jirgin sama a 2023.

Ƴan siyasa da ke alaƙa da Wagner sun kasance suna da tasiri a faɗin Afirka na sama da shekara goma, musamman ma a Jamhuriyar Tsakiyar Afirka, Mali da kuma Madagascar.

Tawagar tsaron Rasha ta ce ba su da alaƙa da ƙungiyar masu tattara bayanan sirrin ko kuma Wagner, kuma ba da yawun Rasha suke aikata abubuwan su ba, sai dai suna ƙoƙarin samar da wani gida na Rasha a Luanda.

Angola na cikin ƙasashen Afirka manya da ke samar da mai da kuma fitar da dutsen demon. Albarkatun da ƙasar ke da shi ne ya sa Moscow ke nuna sha'awa a kanta. Sai dai Angola na sauya akala daga tasirin Rasha sannu a hankali yanzu.

An tilastawa kamfanin haƙar ma'adinai na Rasha Alrosa da kuma bankin VTB ɓarin Angola saboda takunkumai da aka ƙaƙabawa Rasha kan yaƙin Ukraine.

Shugaban Angola João Lourenço ya sauya akala zuwa yammaci, kuma bai sake haɗuwa da takwaransa na Rasha ba Vladimir Putin tun 2019.

Sojojin Rasha da ke Afirka na karkata wa zuwa Angola, kamar yadda aka yi iƙirari.

Ba ya ga ƴan Rashar biyu, akwai kuma ƴan Angola su biyu da su ma za su fuskanci shari'a saboda zarginsu da hannu a shirin Rasha na ingiza zanga-zangar.

Masu gabatar da ƙara sun yi zargin cewa ƴan Rashar sun yi hayar ƴan jaridar ɓangaren wasanni Amor Carlos Tome da ɗan gwagwarmayar siyasa Francisco Oliveira domin su gudanar da ayyukansu a ƙasar.

Suna fuskantar tuhuma kan zargin ta'addanci da kuma leken asiri.

Tawagar lauyoyi da ke kare ƴan Angola ta ce babu gamsassun hujjoji kan waɗanda ake zargin don haka "zargin ba shi da tushe".

Masu gabatar da ƙara sun ce tawagar sojojin Rasha sun isa Luanda babban birnin Angola, a 2024 kan shirin buɗe wata cibiyar gargajiya ta Rasha, abin da bai yi wu ba.

Cikinsu akwai Maxim Shugalei, wanda ke alaƙa da Wagner da Tarayyar Turai ta saka wa takunkumi saboda jagorantar shirin yaɗa labaran ƙarya.

Ya yi tafiya zuwa Angola tare da mai yi masa fassara, Same Suaifan. BBC ta tuntuɓe su.

Yayin da Suaifan ya amince da sanin waɗanda ake zargin, shi kuwa Shugalei ya musanta saninsu.

A cewar takardar tuhumar, a 2024 waɗanda ke kare kansu a shari'ar sun biya ƴan jaridar Angola kuɗaɗe sau da dama da kuma kwararru don yaɗa farfaganda da kuma labaran ƙarya a kafofin yaɗa labaran cikin gida don "janyo sauyin siyasa".

Kuɗin sun kai dala 24,000.

Hukumomin Angola sun ɗauki hakan a matsayin shiri na janyo rashin yarda daga ƙawayen ƙasar na yamma da yi wa tsarin harkokin wajen shugaba Lourenco zagon kasa.

Hukumomin Angola sun yi zargin cewa ƴan Rashar Lakshtanov da Ratchin sun haɗu da manyan jagororin siyasa daga jam'iyya mai mulki ta MPLA da kuma Unita, inda suka ba da gudummawa.

An ce sun haɗu da wani jigon jam'iyyar MPLA Janar Higino Carneiro da kuma na jam'iyyar Unita Adalberto Costa Junior.

Ana ɗaukar dukkansu a matsayin ƴan takarar shugaban ƙasa a zaɓen shekara mai zuwa.

Masu gabatar da ƙara sun yi iƙirarin cewa Rasha ta yi tayin dala miliyan 15 a kamfe ɗin da za a yi, da ba da taimakon tsaro, shawarwari da kuma tattara bayanan sirri.

Sai dai babu hujja kan wannan taimakon da suka yi niyyar bayar wa a cikin kwafin tuhumar da muka gani.

"Ban san cewa an yi irin wannan zama ba," in ji Elizeu Nguiniti, lauyan da ke wakiltar Ratchin da Lakshtanov.

Masu haddasawa ko masu fakewa?

A watan Yulin bara, Angola ta fuskanci ƙazamar zanga-zangar da ba a taɓa gani ba tun bayan kawo karshen yaƙin basasa tsakanin jam'iyyar Unita da kuma MPLA a 2002.

Abin da ya fara da zanga-zangar lumana ta masu motocin haya a Luanda ta rikiɗe zuwa tarzoma a faɗin ƙasar.

Masu gwagwarmaya sun ce masu zanga-zanga sun fuskanci fushin ƴansanda matuka.

A cewar alƙaluman hukumomi, aƙalla mutum 20 ne suka mutu sannan an kama sama da 1,200.

Masu gabatar da ƙara sun ce waɗanda ake tuhumar ne suka shirya zanga-zangar, inda suka ba da hujja da rubuce-rubuce da suka samu a wayoyinsu da kuma hotuna da Ratchin ya ɗauka.

Sai dai lauyoyin Ratchin sun ce ya ɗauki hotunan ne saboda dalilai na kariya, don ya samu hujja idan aka far masa. BBC ba ta rubuce-rubucen ba ko kuma hotunan.

Ƴan jarida da masu gwagwarmaya a Angola da dama sun ce ba a shirya zanga-zangar ba, inda suka ce hukumomin Angola na son fakewa da Rasha don ɓoye laifinsu.

Bankin duniya ya yi ƙiyasin cewa kashi 40 na ƴan Angola na rayuwa ƙasa da abin da aka kayyade a rana na dala uku.

"Mutane na zanga-zanga ne saboda tsadar rayuwa, ba wai saboda wani daga wata ƙasa ya ce su yi ba," in ji Sheila Nhancale, wani mai bincike a ƙungiyar kare hakkin ɗan'adam ta Human Rights Watch.