Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Newcastle na son Trafford, yayin da Madrid ke son ɗauko Wharton
Newcastle United na ci gaba da zawarcin James Trafford, idan har mai tsaron bayan Igila ya amince ya bar Manchester City, a yayin da ya ke ci gaba da neman ƙungiyar ƙwallaon ƙafa da zai takawa leda a kakar wasa mai zuwa. (Football Insider)
A banagare guda kuwa Man City, na tattaunawa da Magpies, kan ƴan wasan da za su biya bata a wani yunƙuri na siyen ɗan wasan tsakiyar Italiya Sandro Tonali, 25. (Teamtalk).
Sean Dyche ya musanta rahotannin da ke cewar ya na wata tattaunawa don maye gurbin Igor Tudor a matsayin kociyan Tottenham Hotspur. (Talksport)
Barcelona, da Tottenham, da Liverpool da Manchester United na cikin ƙungiyoyin da ke son ɗaukar Evan Ndicka, yayin da Roma ke ƙoƙarin amincewa da tayin da ya haura fam miliyan 39 kan ɗan wasan bayan na Ivory Coast. (Caught Offside)
Liverpool da Chelsea na cikin ƙungiyoyin da ke buga gasar Premier, da ke son ganin sun ɗauko mai tsaron bayan OH Leuven Swiss Roggerio Nyakossi, wanda kwantaragin sa zai ƙare da ƙungiyar a ƙarshen kakar wasa. (Sun)
Ɗan wasan Spaniya Marcos Llorente,na son ci gaba da zama a Atletico Madrid yayin da ya ke ci gaba da tattauna da hukumomin ƙungiyar don sabunta kwantaraginsa, duk da cewar akwai ƙungiyoyin ƙwallaon ƙafa masu yawa da ke buga Premier da ke son ɗaukarsa. (Fichajes - in Spanish)
Real Madrid na cikin jerin ƙungiyoyin ƙwallon ƙafar da ke son siyen Adam Wharton ɗan wasan tsakiya na Crystal Palace da Ingila. (AS - in Spanish)
Ɗan wasan bayan Jamus Nico Schlotterbeck, da abaya ake raɗe-raɗin Liverpool na son siyen sa, ya kusa cimma matsya kan shiga kwantaragin da Borussia Dortmund zuwa shekarar 2031. (Florian Plettenberg)