Kwankwaso ya fice daga jam'iyyar NNPP

Lokacin karatu: Minti 2

Jagoran jam'iyyar NNPP, Sanata Rabiu Kwankwaso ya fice daga jam'iyyar bayan aƙalla shekara huɗu a cikin jam'iyyar.

Matakin na zuwa ne bayan da manyan jiga-jigan adawar Najeriya ke ƙoƙarin ƙulla wani ƙawancen siyasa domin ''kawar da jam'iyyar APC a 2027''.

Tsohon gwamnan jihar Kano ya ce ya ɗauki matakin ficewa daga NNPP ne la'akari da halin da siyasar Najeriya ke ciki, wanda ke bukatar haɗin kai.

''Matakin ya zama tilas domin haɗa kai da wata jam'iyyar da za ta ba ni damar kawo sauyi nagari ga ƙasarmu'', kamar yadda Kwankwason ya bayyana.

Sanata Kwankwaso ya kuma gode wa magoya bayansa da jagororin jam'iyyar daga matakin mazaɓa zuwa ƙasa bisa damar da ya ce sun ba shi a tsawon zamansa na NNPP.

Kwankwaso - wanda ya tsaya takarar shugaban ƙasa a zaɓen 2023 ƙarƙashin jam'iyyar NNPP an yi ta hasashen komawarsa APC a watannin baya.

A 2022 ne Kwankwaso ya koma jam'iyyar NNPP sannan tsaya takarar shugaban ƙasa, ya kuma yi nasarar kafa gwamnati a Kano, bayan da jam'iyyarsa ta ci zaɓen gwamna.

Kawo yanzu dai Kwankwaso bai bayyana jam'iyyar da zai shiga ba, amma alamu na nuna cewa ADC zai koma.

An ga yadda a bayan sallah wasu jiga-jigan ADC cikin har da Peter Obi suka kai masa ziyara a gidansa da ke Kano.

Ko a ranar Asabar ma , Kwankwaso ya ziyarci Atiku Abubakar a gidansa da ke Abuja.

Raunin NNPP

Jam'iyyar NNPP ta fara gamuwa da rauni ne tun bayan da tawagar wasu an majalisun tarayya daga jihar Kano, ciki har da sanatan Kano ta Kudu suka fice daga cikinta tare da komawa APC mai mulki.

Ƴanmajalisun da suka haɗa da Sanata Kawu Sumaila da Ali Madakin Gini da Kabiru Al'assan Rurum, sun fice daga NNPP ne bayan da suka yi zargin ana yi musu ƙarfa-ƙarfa a jam'iyyar.

Sannan a watan Janairu gwamnan jihar Abba Kabir tare da wasu ƴan majalisun dokokin jihar ciki har da kakakin majalisar suka fife daga NNPP tare da komawa APC.

Matakin da Kwankwaso ya ce ya yi matuƙar ba shi mamaki, cikin wata hira da BBC a lokacin.

Kwankwaso a siyasar Najeriya

Tsohon gwamnan jihar Kanon, Rabi'u Musa Kwankwaso na ɗaya daga cikin ƴan siyasa a arewacin Najeriya da suka daɗe suna tasiri, musamman saboda yadda ya shiga zuciyar matasa.

Ana dai ganin tun bayan Malam Aminu Kano ba a sake samun wani ɗan siyasa ba da ya fito da wani tsari na siyasa a arewa da ya saka wa suna, kuma yake da mabiya na ga-ni-kashe-ni, sai Kwankwason.

Kwankwaso ne jagoran aƙidar siyasa mai suna ɗarikar Kwankwasiyya da mabiyanta ke saka jar hula.

Bayan kammala wa'adinsa ne ya tsayar da mataimakinsa, Abdullahi Umar Ganduje, wanda ba a daɗe ba, suka samu saɓani aka raba-gari.

Wannan ya sa a lokacin da Ganduje yake neman wa'adi na biyu, Kwankwaso ya tsayar da Abba Kabir Yusuf a zaɓen 2019, amma Ganduje ya kayar da shi bayan an yi zaɓen cike gurbi a garin Gama.

Har ila yau, Kwankwaso ya tsayar da gwamnan Kano mai-ci, Abba Kabir Yusuf inda ya kayar da ɗantakarar gwamna mai barin gado, Nasiru Yusuf Gawuna