Fitattun ƙasashen da ba za su buga kofin duniya ba a 2026

Lokacin karatu: Minti 5

Saura kwanaki kaɗan a fara buga gasar cin kofin duniya ta shekarar 2026. Wasu manyan ƙasashe da dama sun rasa samun damar fafatawa a gasar.

Wannan ne karo na uku da Italiya ta rasa damar buga gasar a jere, duk da ƙasar ta lashe kofin har sau huɗu.

Fitattun ƙasashe da ke taka rawar gani a nahiyar turai da dama sun kasa samun damar buga gasar kofin duniya a wannan karon, da ma wasu ƙasashen Afrika.

Amurka da Kanada da Mexico ne za su karɓi baƙuncin gasar daga 11 zuwa 19 ga watan Yulin 2026, inda za a buga wasan ƙarshe a filin wasa na MetLife da ke New Jersey na Amurka.

Ga jerin wasu manyan ƙasashen da ba za su samu damar buga gasar kofin duniya ba.

Italiya (ƙasa ta 12 a jerin hukumar FIFA)

Italiya wadda ta lashe kofin duniya har sau huɗu ta rasa damar fafatawa a gasar ta shekarar 2026 karo na uku a jere, bayan rashin nasara a bugun fenariti a wasan da ta buga da Bosnia-Herzegovina a ranar Talata.

Babu wata kungiya da ta taɓa lashe kofin duniya kuma ta gaza zuwa gasar cin kofin duniya har sau uku a jere sai Italiya.

Ƙasar ba ta samu damar buga gasar kofin duniya ba shekarar 2018 a Rasha, da kuma Qatar a shekarar 2022.

Italiya ta yi rashin nasara ne a hannun Bosnia-Herzegovina ne bayan tashi wasa kunnen doki 1-1.

Kafin a tafi hutun rabin lokaci, an ba Alessandro Bastoni jan kati, bayan ya yi wa ɗanwasan Bosnia ƙeta, inda suka kammala da ƴanwasa 10.

Denmark (ƙasa ta 20 a jerin hukumar FIFA)

Denmark na daga cikin fitattun ƙasashen da suka samu koma baya, inda su ma ba za su buga gasar cin kofin duniya ta shekarar 2026 ba, bayan rashin nasara a hannun Czechia a bugun fenariti.

Czechia ita ce ƙasa ta 43 a jerin ƙasashen da suka fi shahara wajen taka leda a duniya na FIFA.

Denmark na da fitattun ƴanwasa, ciki har da matashin ɗanwasa Rasmus Hojlund da ya taka leda a Manchester United da Napoli.

A yanzu Denmark ba za ta sake samun wannan damar ba sai nan da shekarar 2030.

Najeriya (ƙasa ta 26 a jerin hukumar FIFA)

Tawagar Super Eagles ta Najeriya, na daga cikin fitattun ƙungiyoyi a Afrika.

Ta rasa damar buga gasar cin kofin duniyar 2026 bayan rashin nasara a hannun DR Congo, tun a wasan neman cancantar shiga gasar.

Najeriya ce ta 26 a jerin hukumar FIFA, kuma wannan ne karo na biyu da ba za ta samu damar bugar gasar ba a jere.

Ƙasar ba ta samu damar shiga gasar ba a 2022 da aka yi a Qatar, tun bayan rashin fafatawarta a shekarar 2006.

Najeriya na taka rawar gani a duniyar tamaula, inda take da fitattun ƴanwasa irin su Victor Osimhen, Ademola Lookman, Alex Iwobi, Calvin Bassey, da Samuel Chukwueze.

Sai dai duk da haka sun kasa kaiwa matakin nasara.

Poland (ƙasa ta 35 a jerin hukumar FIFA)

Rashin samun nasarar Poland a gasar cin kofin duniya na shekarar 2026 ya sare gwiwar fitattun ƴanwasanta.

Wannan ce dama ta ƙarshe ga ɗanwasa Robert Lewandowski da zai buga wa ƙasar gasar kofin duniya.

Poland ta yi rashin nasara ne a hannun Sweden da ci 3-2.

Bayan rashin nasarar, Lewandowski ya wallafa a shafinsa na X cewa ya yi bankwana da buga wa ƙasarsa wasa.

Rasha (ƙasa ta 36 a jerin hukumar FIFA)

Rasha na cikin manyan ƙasashen da ba za su buga gasar kofin duniya ba a shekarar 2026.

An haramta wa ƙasar shiga dukkanin wasannin FIFA da UEFA saboda mamayar da ƙasar ta yi wa Ukraine a 2022.

Duk da cewa ƙasar ta ɗaukaka ƙara game da hukuncin a kotun sauraren ƙorafe-ƙorafen wasanni ta CAS, amma ba ta samu nasara ba.

Rasha ita ta ƙarbi baƙuncin gasar cin kofin duniya a shekarar 2018, kuma har yanzu ba a san ranar da za a janye mata takunkumin ba.

Ƙasashen da za su buga gasar cin kofin duniya ta 2026

Ƙasashe shida da suka rage sun kammala wasanninsu, abin da ke nuna cewa yanzu ƙasashe 48 ne za su fafata.

Jamhuriyar Dimokradiyyar Kongo da Iraƙi su ne ƙasashe biyu na ƙarshe da suka samu nasarar shiga gasar.

DR Congo ta doke Jamaica, yayin da Iraƙi ta doke Bolivia.

An tabbatar da sauran ƙasashen turai huɗu ne a ranar Talata, inda Bosnia-Herzegovina da Jamhuriyar Czech da Turkiya da Sweden suka samu nasara.

Cikin ƙungiyoyi 48 da za su fafata, ƙasashe ukun da za su ƙarbi baƙuncin gasar sun samu tikiti kai tsaye, yayin da 43 kuma suka fafata a wasannin neman cancantar shiga gasar, sai kuma biyu da suka samu gurbin ta hanyar wasannin kifa ɗaya ƙwala a nahiyoyinsu.