Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

KAI TSAYE, Yaƙin Iran da Amurka da Isra'ila da kuma abubuwan da ke faruwa a Najeriya 01/04/2026

Wannan shafi ne da ke kawo muku rahoto kan yaƙin Iran da Amurka da Isra'ila da kuma abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya na ranar Laraba 01 ga watan Afrilun 2026.

Rahoto kai-tsaye

Daga AishaBabangida da Haruna Kakangi

  1. Ana ci gaba da musayar wuta tsakanin Iran da Isra'ila da Amurka

    Rahotanni sun ce an sake yi wa Iran ruwan bama-bamai, inda rundunar sojin Isra'ila ta ce ta kammala abin da ta kira wasu jerin hare-hare ta sama a kan wuraren da ta ce na gwamnatin Iran din ne, a babban birnin ƙasar, Tehran.

    A cikin dare rundunar sojin Amurka ta fittar da wani bidiyo da ke nuna sojojinta na jefa abin da ta kira bama-bamai na yankan-shakku a wuraren da ta ce na soji ne da ke karkashin kasa.

    Kamar dai yadda aka saba, ita ma Iran din ba ta sarara ba a martanin da take kai wa, inda jamiai a Kuwait suka ce wuta ta tashi a babban filin jirgin sama na kasar, sakamakon harin jirgin sama maras matuki da Iran ta kai a kan wasu tankunan mai.

    Can a Bahrain Iran din ta kai hare-hare cikin dare inda gobara ta tashi .

    Haka kuma hukumar jamian tsaro na teku ta Birtaniya ta ce wani makami mai linzami ya fada kan wani jirgin ruwa na dakon mai a gabar tekun Qatar

  2. Iran ta kai wa tankar man Qatar hari da makami mai linzami

    Ma'aikatar tsaron Qatar ta sanar da cewa Iran ta kai mata harin makamai mai linzami kan tankar man ta a ranar Laraba.

    Iran ta kaddamar da hare-haren makamai masu linzami guda uku, amma Qatar ta ce ta kakkaɓo biyu daga ciki, inda na ukun ya sauka kan tankar man ta, ta Aqua-1.

    Sai dai ba a samu asarar rai a harin ba.

    Hukumar kula da sufurin jiragen ruwa ta Birtaniya da hukumar kula da makamashin Qatar, sun ce harin ya lalata jirgin da ke cikin tekun ta a arewacin Ras Laffan.

    Matatar iskar gas mafi girma a duniya tana yankin Ras Laffan ne a ƙasar Qatar, amma an rufe ta saboda hare-haren Iran.

  3. Yaƙin Iran zai zo ƙarshe cikin ƴan makonni masu zuwa - Trump

    Shugaban Amurka, Donald Trump ya nuna cewa yana son ya rage hare-haren da ake kai wa Iran, yana mai alƙawarin cewa yaƙin zai zo karshe a cikin mako biyu ko uku masu zuwa ko da an cimma yarjejeniya ko ba a cimma ba.

    Ya ce yanzu Iran tana da sababbin shugabanni waɗanda suka fi sauƙin samu, ba masu tsattsauran ra'ayi ba kuma wadanda suka fi magabatansu hankali.

    Ya ce gwamnatin Amurka ta cimma burinta, duk da cewa ba ta iya kwace mashigar Hormuz ba daga hannun Iran. Yuwuwar ci gaba da karancin mai, farashin danyen man ya kara tashi a yau Laraba.

    To amma kuma Mista Trump ya ce nan gaba kadan farashin zai sauka. A yau zai gabatar da jawabi ga al'ummar kasar ta Amurka ta talabijin.

  4. Haɗakar ADC : Wane tasiri shigar manyan ƴan'adawa za ta yi a zaɓen 2027

    Bisa ga dukkan alamu a Najeriya an kama hanyar gina babbar hadaka ta siyasa gabanin babban zaben kasar na 2027, bayan shigar tsohon gwamnan Kano Rabiu Musa Kwankwaso jam'iyyar ADC.

    Ana kallon hadewar Kwankwaso da tsohon mataimakin shugaban kasar, Atiku Abubakar da kuma Peter Obi, wadanda dukkaninsu sun tsaya takarar shugaban kasa a zaben 2023, a matsayin wani babban ci gaba a bangaren hamayya a Najeriya, kuma wani babban kalubale ga jam'iyya mai mulki.

    Yayin da ake ganin cewa siyasar hamayya a Najeriya tamkar ta shude - ganin yadda ake ta sauya sheka zuwa APC mai mulki, wasu masana na ganin wannan sabuwar hadaka ta jam'iyyar ta ADC ka iya zama wani babban kalubale ga Shugaba Tinubu da jam'iyyarsa ta APC a zaben 2027.

    Haka kuma masanan na ganin siyasar hamayya a kasar wadda ta fi yawan jama'a a Najeriya za ta sake farfadowa fiye da yadda ba a zata ba.

  5. Assalamu alaikum

    Jama'a barkanmu da wannan safiya ta Laraba ga wannan shafin namu na BBC Hausa, inda za mu ci gaba da kawo muku labaran kai-tsaye na abubuwan da suke faruwa a Najeriya da sassan duniya.

    Za ku iya leƙawa shafukanmu na sada zumunta na facebook da X da kuma whatsapp domin karanta wasu labaran da kallon bidiyo da ma tafka muhawara.

    Ku kasance tare da mu.