Fernandez na son tafiya Madrid, Man Utd ta rasa damar samun Anderson
Asalin hoton, Getty Images
Dan wasan tsakiya na Chelsea da Argentina Enzo Fernandez, mai shekara 25, na shirin mika bukatarsa ta neman tafiya Real Madrid a bazara. (El Chiringuito, daga Goal)
Tottenham na duba yiwuwar sayen mai tsaron ragar Manchester City da Ingila James Trafford, mai shekara 23, a matsayin wanda zai maye gurbin Guglielmo Vicario, na Italiya mai shekara 29 wanda shi kuma Inter Milan ke sonshi. (Sun)
Dan bayan Ingila Harry Maguire, mai shekara 33, ya yi watsi da bukatar tafiya kungiyar Inter Miami ta Amurka, kafin ya kulla sabon kwantiragi da Manchester United, inda yake son ya yi ritaya a kwallon kafa. (Sun)
Liverpool ta bi sahun Newcastle wajen sanya ido a kan matashin dan bayan Italiya Marco Palestra, mai shekara 21, wanda a yanzu yake zaman aro a Cagliari daga Atalanta. (Teamtalk)
Manchester United za ta sayar da dan wasanta na tsakiya Manuel Ugarte, mai shekara 24, dan Uruguay a bazara, inda Galatasaray, da Newcastle da kuma ke sha'awarsa. (Fabrizio Romano)
Bisa ga dukkan alamu United ta rasa damar samun Ingila Elliot Anderson, kodayake, dan wasan na tsakiya mai shekara 23, ya fi son tafiya Manchester City daga Nottingham Forest a bazaran nan. (Mirror)
Dan wasan tsakiya na Barcelona Marc Casado, na da damar barin kungiyar ta Sifaniya a bazara, bayan da matashin mai shekara 22, ya rasa gurbinsa a jerin 'yan wasa 11 na farko da kungiyar ta fi ji da su. (SER Catalunya)
Kungiyar Fenerbahce ta Turkiyya na son sayen dan wasan tsakiya na Tottenham Yves Bissouma a bazara. Dan wasan na tawagar Mali mai shekara 29ya taka leda sau takwas ne kawai a kakar nan. (TurkishFootball)
Tottenham da Chelsea na duba yuwuwar sayen dan wasan tsakiya na Sporting Maxi Araujo. Araujo mai shekara 26 zai iya wasa a gaba a bangaren hagu ko kuma a baya bangaren na hagu, kuma yana yi wa Uruguay wasa kodayaushe. (CaughtOffside)
Crystal Palace na dab da sayen matashin dan baya Harris Afzal -mai shekara 16 wanda ake wa lakabi da Andy Robertson - na gaba daga Queen's Park. (TeamTalk)
Chelsea na neman dauko tsohon dan bayan Brighton Valentin Barco daga kungiyar Strasbourg, wadda Chelsea din ke da alaka da ita, a bazarar nan. Mai shekara 21 Barco ya buga wa Brighton wasa 6 na Firimiya, amma kuma ya taka wa Argentina leda. (FourFourTwo).
Babban Labari
Labarai na musamman
Labaran da suka fi shahara
Babu karin bayanai