Da gaske hasken waya na haifar da matsala ga bacci?

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Shuɗin hasken waya.
Lokacin karatu: Minti 6

Na shafe makwonni ina sanya wani gilashi na musamman har tsawon sa'o'i 3 kafin kwanciyar bacci.

An yi shi ne da wata roba mai ƙarfi kuma yana fidda wani irin haske wanda ke hana shuɗin haske tasiri.

Duk da haka, na rufe tagogin ɗakina da labule mai duhu na kuma kashe fitilun ɗakina, ina haska ɗakina kawai da hasken kyandir.

Wani gwaji da na yi sai na fahimci yanayin bacci na ya sauya, na gano abinda ke faruwa idan ka rage hasken shuɗiyar fitila.

Shekaru goma da suka gabata, an yi fargaba a duniya game da hasken da ke fita daga fitila.

Mun san cewa wayar salula da telebijin da kwamfuta da hasken fitilun da muke amfani da su zasu iya cutar da lafiyar mu saboda shuɗiyar fitilar da suke fitarwa mai ƙarfi. An yi tunanin hasken ya na yiwa bacci illa ta hanyar rikita agogon jikin halittar ɗan Adam.

Kimiyya ta tabbatar da wannan iƙirari. Wasu masana a yanzu sun ce akwai yiwuwar hasken waya zai iya katse maka bacci.

Wasu ƙirƙire ƙirƙire da aka samar don su rage ƙarfin shuɗin hasken waya ba su yi tasiri sosai wajen inganta bacci ba.

Don tabbatar da gaskiya game da wannan iƙirari na tuntuɓi masana.

Na ɗauki dukkan matakan kare kai na daga shuɗin haske don in samu cikakken bacci ba tare da na yi amfani da wani tabarau mai launi ba

Akwai yiyuwar wannan hanya ce sirrin samun ingantaccen bacci.

Mugun allo?

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Jama'a sun fara bayyana fargaba game da shuɗiyar filar jikin waya tun a shekara ta 2014. Yayin da wani bincike ya bayyana sakamakon gwajin da aka gudanar kan wasu mutane 12 da suka yi karatu da waya samfurin Ipad kafin kwanciyar bacci da kuma mutanen da suka karanta shafukan littafi kafin su kwanta.

Waɗanda suka yi amfani da wayar Ipad sun jima ba su yi bacci sannan kuma sun wayi gari da gajiya kuma jikinsu ya samar da sinadarin melatonin kaɗan.

Masu binciken sun yi iƙirari cewa hasken da ke fita daga jikin wayar Ipad ne ya hana su bacci.

Wani yanayi na sanya shuɗin hasken jikin waya rikita agogon jikin ɗan Adam. Sauran binciken da aka gudanar daga baya sun tabbatar da haka.

Kamar abu mai sauƙi ko? Amma ba haka bane.

Jamie Zeitzer wani farfesan kimiyyar ɗabi'un ɗan Adam a Jami'ar Stanford dake Amurka ya yi nazarin tasirin haske a agogon jikin ɗan Adam.

Zeitzer ya ce kimiyya ta na da kyau amma ta sanya mutane imani da hujjoji marassa tushe.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Kimiyya ta bayyana cewar hasken da wayoyin salula ke fitarwa bai yi tsananin da zai hana bacci ba.

Shuɗiyar fitila ta na iya shafar bacci. Zeitzer ya ce saboda sinadarin melanopsin da ke idanunmu wanda ke taka rawa wajen daidaita mana bacci.

"Melanopsin ba ya son shuɗin hasken da ke fita daga waya," in ji shi.

Wani sabon bincike da aka gudanar ya bayyana yadda hasken waya ke jinkirta bacci da minti 9.

Akwai wani binciken kuma da ya bayyana yadda kallon shuɗin haske na sa'o'i 24 daga na'urori ya ke daidai da ƙasa da minti ɗaya da mutum ya yi a waje.

Amma mene ne dalilin yawan gajiya da na ke fama da ita?

Zeitzer tare da sauran masu bincike sun yi iƙirari cewar kowanne irin haske zai iya rikita bacci ta hanyoyi da dama.

Ya zama tilas in ɗauki matakai masu tsauri idan ina son kare kai na daga matsalolin shuɗin haske.

Dakatar da amfani da shuɗin haske.

A ranar farko na tabbar na ci abincin dare da misalin ƙarfe 8:30 na kuma shaidawa kai na cewar lokacin komawa ta gida ya yi watau lokacin da zan fita daga hasken.

Masana bacci sun ce ana fara shirin kwanciya bacci kafin a kwanta a gado a rufe jiki da bargo.

"Bai kamata mu yawaita kallon shuɗin haske ba," in ji Håvard Kalestad, shugaban ƙungiyar binciken barci a Jami'ar Kimiyya da Fasaha ta Norway.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Shuɗin haske na zamani.

Na zauna akan kujera na fara tunanin irin sadaukarwar da na yiwa aikin jarida.

Na dauki waya ta na fara duba Instagram. Allon wayar ya koma kalar ja.

Manufar ita ce ina son fahimtar tasirin haske akan barci na.

"Ina ganin ya kamata ku mai da gidajenaku kamar kogo," kamar yadda Kallestad ya bani shawara. "Ku toshe dukkan haske ku kunna kyandir."

Fitilar LED ta zamani na fidda shuɗin haske mai yawa. Hasken tsoffin fitulun ba ya cutarwa sosai yayin da kyandir kusan ba shi da shuɗin haske mai cutarwa.

Inda nake zaune a New York da ke Amurka ba shi da duhu ko kaɗan. Don haka na sanya labule mai duhu akan tagogi na. Hasken Wayata da kyandira biyu sun raba ni da duhu.

Har yanzu na kasa barci.

Da rana

Masana sun amince cewar abinda ya fi muhimmanci shi ne adadin hasken da jiki ke samu a rana.

Don samun ingantaccen bacci jiki na buƙatar hasken rana cikin yini yayin da ya ke buƙatar ƙarancin haske da maraice.

Don haka ana yiwa bacci shiri da zarar gari ya waye.

Sannan a fara shiryawa idanuwa bacci ta hanyar rage shuɗin haske da yamma.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Masana sun ce hasken da ake amfani da shi wajen yiwa masu lalurar damuwa magani, ya na wartsakar da jiki cikin rana.

"Yawan hasken da muka samu cikin rana na tasiri wajen bacci cikin dare," in ji Zeitzer.

Kafin annoba mun saba da shige da fice cikin hasken rana kamar tafiye tafiye da hasken ofisoshi da na wuraren cin abinci.

Amma yanzu da dama daga cikinmu na zama cikin haske ɗaya tun daga tashi daga bacci zuwa kwanciyar bacci da daddare, jiki ba ya banbancewa tsakanin rana da dare.

Fita waje cikin hasken rana na daidaita bacci fiye da duk wani launin haske.

Kallestad ya bada shawara cewa, idan zaka iya ka fita daga gida ko ka yi amfani da haske na musamman da aka yi tanadi.

Tafiyar mintuna 30 da safe kawai zata yi tasiri.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Bidiyo da shafukan da muke dubawa su na tasiri a bacci.

''Idan kuna aiki daga gida to ku kunna fitilu masu haske da rana sannan ku fara rage musu haske da maraice," in ji Zeitzer.

Amma shuɗin hasken da waya ke fitarwa ba shi da tasiri sosai a baccin mu. Babban matsalar a cewar Zeitzer, ita ce yawan lokacin da muke akan wayoyin hannu da kwamfuta kafin mu kwanta barci.

Blue light blocking?

Ina amfani da wata na'ura mai bibiyar bacci don fahimtar yadda jiki na ke hutawa.

A ƙarshen mako na biyu na gwajin da na yi, hakan ya sa ina kwanciya da wuri kuma bacci ya na dauka ta cikin sauƙi.

''Jiki ya na sabawa da duk abind aka mayar da shi al'ada kafin kwanciya misali duba waya ko kallon fim ko karatu daga waya,'' cewar Zeitzer

''Tabbas amfani da gilashin da ke kare fuska daga shuɗin haske da maraice ya na taimakawa mutane da dama."

Idan ka kawo min ziyara ba zaka same ni da gilashin da ke kare shudin haske ba, amma zaka samu kyandir a wuri na.

Thomas Germain ɗan Jarida ne a BBC mai bibiyar yadda na'urorin zamani ke tasiri a rayuwar mutane.