KAI TSAYE, Yaƙin Iran da sauran abubuwan da ke faruwa a sassan duniya, 19/04/2026

Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran yaƙin Iran da sauran abubuwan da ke faruwa a sassan duniya, 19/04/2026

Rahoto kai-tsaye

Daga Abdullahi Bello Diginza

  1. 'Islamabad na shirin karɓar baƙuncin tattaunawar Amurka da Iran karo na biyu'

    Birnin Islamabad

    Asalin hoton, Reuters

    Kamfanin dillancin labarai na Reuters ya bayar da rahoton tsaurara matakan tsaro a Islamabad, babban birnin Pakistan.

    Yayin da jami'an Amurka da na Iran ke shirin ci gaba da tattauna batutuwan da suka sha bamban don kawo ƙarshen yaƙin Iran.

    Kawo yanzu dai ba a bayyana wuri da lokacin da za a gudanarwa da tattaunawar ba.

    Mashigar Hormuz - wadda ke cikin batutuwan da ɓangarorin biyu suka yi saɓani - ta kasance a rufe, saboda ci gaba da datse tasoshin ruwan Iran da Amurka ke yi.

    Iran ta ce jiragen ruwa za su wuce ta mashigar ne kawai bisa amincewar dakarun IRGC.

    Duka ɓangarorin biyu dai sun ɗauki tsauraran matsayi game da batun.

    Shugaba Trump ya jaddada cewa Amurka za ta bari jiragen Iran su shiga ko fita daga tasoshin ruwanta ne kawai idan aka cimma yarjejeniyar kawo ƙarshen yaƙin, yayin da Iran ta zargi Amurka da rashin mutunta yarjejeniyar wucin gadi da aka cimma.

  2. Fafaroma Leo ya gudanar da ibada tare da dubban mabiya a Angola

    Fafaroma

    Asalin hoton, Getty Images

    Fafaroma Leo na gudanar da taron Ibada tare da dubban Kiristoci da suka taru a wani wuri a Kilamba da ke wajen Luanda, babban birnin Angola.

    Masu ibadar - waɗanda ke sanye da farar riga da hula mai launin ruwan ɗorawa, manne da hotonsa - sun cika wurin ibadar.

    Jagoran ɗariƙar Katolikan zai kuma ziyarci Muxima, wani babban wurin ziyarar ibada a ƙasar da ke kudancin Afirka.

    A ranar Asabar ne Fafaroman ya ziyarci ƙasar - a wata ziyara da yake yi a ƙasashen Afirka huɗu - inda ya gana da shugaban ƙasar.

    Fafaroman ya buƙaci shugabannin siyasa kada su ji tsoron bayyana aƙidar addininsu, yana mai cewa Angola za ta ci gaba idan ta yi amfani da hanyoyi daban-daban na dukiyar da Ubangiji ya huwace mata.

  3. Alamu sun nuna cewa babu jirgin da ya wuce ta mashigar Hormuz

    Alamu daga safin Marine Traffic

    Asalin hoton, MarineTraffic

    Yayin da Iran ta sanar da sake rufe mashigar Hormuz, a matsayin martani ga matakin Amurka na ci gaba da rufe tasoshin ruwanta.

    Shafin da ke bibiyar ziraga-zirgar jiragen ruwa na Marine Traffic ya nuna cewa babu jirgin da ya tsallaka mashigar, duk da cewa akwai jiragen da dama a gaɓar mashigar, musamman gaɓar tekun Oman da na UAE.

    Shafin kula da sufurin jiragen ya nuna cewa jirage da dama ne suka matsa kusa a mashigar a jiya, to amma suka dakata bayan da Iran ta sanar da sake rufe ta.

    Jiragen ruwa da dama ne ciki har da na dakon kaya aka bayar da rahoton dakarun Iran sun kai musu hari a ranar Asabar.

  4. 'Tump na amfani da yaƙin Iran don karkatar da hankalin jama’a daga bankaɗar Epstein'

    Kamala Harris

    Asalin hoton, Getty Images

    Tsohuwar mataimakiyar shugaban Amurka, Kamala Harris, ta ce Shugaban Amurka, Donald Tump na amfani da yaƙin Iran ne domin karkatar da hankalin jama’a daga sakin bayanan bankadar mashahurin mai lalata da ƙananan yaran nan Jeffrey Epstein.

    Yayin da take jawabi a wani taron mata na jam'iyyar Democrat a jihar Michigan, tsohuwar ƴan takarar shugaban Amurka a jam'iyyar Democrats ɗin ta ce firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu ne ya yi wa shugaba Trump ingiza mai kantu ruwa wajen sanya shi shiga yaƙin.

    Sai dai ba ta bayar da hujjar iƙirarin nata ba, amma ta ce Amurkawa ba sa son yaƙin.

    Kawo yanzu dai babu wani martani daga Shugaba Trump kai-tsaye ga zarge-zargen na Mrs Harris, amma ya ce Isra'ila ''babbar ƙawa'' ce a cikin wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na sada zumunta.

    • "Ko mutane su so Isra'ila ko su ƙi ta, ta tabbatar da cewa ita babbar ƙawa ce ga Amurka. Suna da ƙwazo da ƙarfi da biyayya da kuma fikira, kuma ba kamar saura ba, da suka nuna mana halinsu na ainihi a lokacin yaƙi da na matsi, Isra'ila na yaƙi da himma, kuma sun san yadda za su yi nasara!"

    A makon da ya gabata ne Mrs Harris ta ce tana nazarin yiwuwar sake tsayawa takara, bayan da ta sha kaye a yunƙurin da ta yi a baya a hannun Mista Trump.

  5. Iran ta yi gargaɗin taƙaita zirga-zirga a Hormuz

    Jirage

    Asalin hoton, ...

    Shugaban Majalisar Dokokin Iran, Mohammad Baqer Qalibaf, ya ce dakarun Iran ne ke da cikakken iko da mashigar Hormuz.

    Mista Qalibaf ya yi gargaɗin ci gaba da takaita zirga-zirgar jiragen ruwa ta mashigar matsawar Amurka ba ta janye shingen da ta yi wa jiragen ruwan Iran ba.

    A baya-bayan rundunar sojin Iran ɗin ta riƙa mayar da jiragen da suka yu yunƙurin wucewa ta mashigar.

    Shugaba Donald Trump ya ce Amurka za ta ci gaba da hana jiragen ruwa zuwa ko fitowa daga Iran har sai an cimma yarjejeniya da Tehran.

  6. Assalamu alaikum

    Masu bibiyarmu barkanmu da hutun ƙarshen ako.

    Abdullahi Bello Diginza ke fatan sake kasancewa da ku a daidai wannan lokaci, domin kawo muku irin wainar da ake toyawa.

    Ku biyo mu a shafukanmu na sada zumunta domin tafka muhawara kan labaran da muke wallafawa.