Shugaban Kenya na shan suka saboda ya ce ƴan Najeriya ba su iya turanci ba

William Ruto and Bola Tinubu

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Shugaba William Ruto ya ce ƴan Kenya na daga cikin waɗanda suka fi iya turanci a duniya
    • Marubuci, Wycliffe Muia
    • Aiko rahoto daga, Nairobi
  • Lokacin karatu: Minti 3

Shugaban Kenya William Ruto na shan suka a shafukan sada zumunta bayan wasu kalamai da ya yi na shaguɓe kan yadda ƴan Najeriya ke turanci. Ya ce idan ƴan Najeriya na turanci sai mutum ya nemi tafinta kafin ya gane abin da suke cewa.

Yayin da yake yi wa ƴan Kenya mazauna Italiya jawabi a ranar Litini, Ruto ya ce: "Idan kana sauraren yadda ƴan Najeriya ke magana, ba za ka gane me su ke cewa ba - sai ka nemi wanda zai fassara maka," inda ya bugi ƙirjin cewa ƴan Kenya na daga cikin mutanen da suka fi iya magana turanci a duniya.

Kalaman nasa na shan suka daga ƴan Najeriya da wasu ƴan Afrika da suka zargi shugaban Kenyan da cin fuskar ƙasar da take a Afrika.

"Turanci yaren mulkin mallaka ne, ba da shi ake gane basira ko ƙwazo ko kuma ci gaban ƙasa ba," in ji wani ɗanjarida daga Zimbabwe Hopewell Chin'ono.

A matsayinsu na waɗanda Birtaniya suka yi wa mulkin mallaka, Kenya da Najeriya duka suna amfani da turancin Ingilishi a matsayin harshen ƙasa, amma kowace ƙasa akwai salon harshe da yadda suke magana.

Wannan ya faru ne sakamakon yawan harsuna da ƙabilu da ake da su a ƙasashen - Kamar Najeriya, akwai yare sama da 500 da ake da su a ƙasar da suke tasiri kan yadda ƴan ƙasar ke magana, yayin da a Kenya kuma, yaren Bantu da Nilotic da Cushitic ke tasiri kan yadda kowanne ko furta lafazinsa.

Sai dai a jawabin da shugaban Kenyan ya yi mazauna ƙetare, ya ce tsarin ilimin ƙasar da yadda suka iya turanci ya sa ba su iya gane abin da ƴan Najeriya ke cewa idan suna magana da turancin.

"Tsarin ilimin mu yana da inganci. Turancinmu ma mai kyau ne. Muna daga cikin waɗanda suka fi iya turanci a duniya. Idan ka ji yadda ƴan Najeriya turanci, ba za ka gane me su ke cewa ba. Sai ka nemo mai fassara," in ji Ruto, yayin da aka bushe da dariya a ɗakin taron.

"Muna ɗaya daga cikin ƙasashen da suke da ayyukan samar da ci gaba a duniya. Muna buƙatar inganta hakan ne kawai da wani horo," in ji Ruto.

Kalaman nasa sun haifar da cece-ku-ce a a shafukan sada zumunta, inda da dama ke sukar shugaban Kenyan game da yadda ya nuna "dogaro da alfahari da tsarin turawan mulkin mallaka"

Me ya janyo kalaman na Ruto?

Wannan cece-ku-ce na zuwa ne a lokacin da shugaban Najeriya, Bola Tinubu ke shan shan suka daga ƴan Kenya saboda kwatanta "yadda ƴan Najeriya ke rayuwa fiye da ƴan Kenya da wasu ƙasashen Afrika "duk da tsadar farashin man fetur a ƙasar".

Duk da yake Ruto bai fayyace dalilin kalaman nasa ba, amma mutane da dama da ke sharhi kan batun na alaƙanta kalamansa da abin da Tinubu ya faɗa.

Gwamnatin Ruto ba ta ce komai kan batun ba, amma wasu ƴan Kenya suna kare shugaban a shafukan sada zumunta, inda suke cewa ba a fahimci kalaman da ya yi ba ne.

Martani

Tsohon Sanata Shehu Sani ya wallafa a shafinsa na X cewa: "Ruto na tsokanar turancin ƙasar da take da mutumin da ya lashe kambin adabin turanci na duniya. Ƙasar da ta ke da Achbe da Chimamanda," inda yake buga misali da Wole Soyinka manyan marubuta irinsu Chinua Achebe da Chimamanda Ngozi Adichie.

Wasu masu amfani da shafukan sada zumunta sun buƙaci Ruto da ya maida hankali wajen magance matsalolin da su ke damun ƴan ƙasarsa, irinsu tsadar rayuwa da rashin aikin yi, a madadin magana kan abubuwan da ba su da wani alfanu.

Ana yawan cacar baki da tafka muhawarori masu zafi tsakanin ƴan Najeriya da Kenya a shafukan sada zumunta musamman X.

Yawanci ana tafka irin waɗannan muhawarori ne kan abubuwan da suka shafi tattalin arziki, al'adu, wasanni da wasu harkokin siyasa.