Birtaniya ta ce ƴan China na sayar da bayanan sirrin jama'a
Wani shirin tattara bayanai na lafiya na Birtaniya ya ɗora alhaki a kan masu bincike 'yan China marasa taka-tsantsan, kan yadda ake sayar da bayanan sirri na wajen mutum rabin miliyan da suka bayar da bayanansu bisa radin kansu.
Ana dai sayar da bayanan ne a yanzu a wani shafin kasuwanci na intanet na China.
Wata ƙungiyar agaji wadda ke gudanar da shirin tattara bayanan na Birtaniya ta gabatar da kanta ga hukumar da ke sa ido wajen kare bayanai ta Birtaniya.
Shirin dai yana amfani da bayanan lafiya, na dubban mutane da na ƙwayoyin halittarsu na DNA, wajen inganta hanyoyin gano wasu cutuka masu tsanani da kuma magance su.
Masu bincike a faɗin duniya na iya samun bayanan, amma bisa sharaɗi mai tsanani na tabbatar da kare sirri.




