Wane ne fir'aunan da ya yi zamani da annabi Musa?

Asalin hoton, Getty Images

Lokacin karatu: Minti 6

Labarin asalin mutanen Misra da kuma tarihinsu ya yi ƙasa, ba a jinsa har sai lokacin da aka samu ɓullar Yahudawan gargajiya da ke zaune a Misra, waɗanda aka ambata a littafin Injila, a surar ficewar Bani Isra'ila daga Misra, da kuma wasu ayoyin Qur'ani mai girma.

Littattafan addini na baya su ma ba su ambato sunan wannan "Fir'aunan" ba, wanda ya mulki Misra kuma ya yi rayuwa da Annabi Musa.

Wannan ya janyo wasu malamai da ke da sha'awar bibiyar tarihin mutanen Misra ta hanyar tattara duka bayanan da tarihi ya tanada domin warware dambarwar sanin Fir'aunan da kuma gano shaidun sanin da za su warware taƙaddamar da ke tsakaninsu.

A 1976, aka kai gawar Sarki Ramses na biyu filin jirgin Bourget da ke Paris babban birnin Faransa, aka kuma kai ta gidan tarihi na Breguet.

An yi wani taron biki a kan gawar, wanda tawagar shugaban Faransa na lokacin da shugaban sojojinsu da jakadan Masar a Faransa da sauran mutane suka halarta.

An yi kiɗe-kiɗen sojoji gabanin a ajiye gawar a gidan tarihin, da ke tsakiyar babban birnin ƙasar, a wani shiri da ake yi na killace gawar da dawo da ita kan ganiyarta da wasu masana kimiyyar Faransa za su yi saboda cutukan da ake tsoron zai shafe su.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Marigayi shugaban ƙasar Masar Mohamed Anwar Sadat yayin leƙa gawar Sarki Ramses II

Cikin watanni bakwai na lokacin daga 26 ga watan Satumbar 1976 zuwa 10 ga watan Mayun 1977 birnin Paris ya riƙa karɓar manyan baƙi "kamar yadda fitacciyar masaniyar kimiyyar nan Madame Christiane de Roche Noblecourt ta bayyana a littafinta na "Ramsey na biyu.

Labarin ya ƙara da cewa an ware wani dogon ɗaki domin gawar ta fir'auna kawai.

Domin gane kwayoyin cutar da suka shafi gawar basaraken, sannan a samar da wani tsari da za a kiyaye gawar, shugaban gidan tarihin ya samar da masu taimaka masa kimanin 120, waɗanda duk suka yi alƙawarin za su yi aikin kyauta, cikin har da masu bincike masana kimiyya 63 a mabanbantan fannoni."

Me ya sa aka kai gawar Ramses II birnin Paris?

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Madame Alice Saunier-Cité, tare da tawagar shugaban Faransa na lokacin Valéry Giscard d'Estaing, tana gabatar da bayani lokacin bikin gawar ta fir'auna ko kuma Sarki Ramesses II a "Bourges".

Akwai manufofi uku cikin aika gawar Sarki Ramses II zuwa birnin Paris.

Na farko a magance wasu cutuka da suka fara kama wasu sassan jikin gawar kamar ƙafar da, da dunduniyarta da kafaɗarta ta dama da kuma ƙasan cibiyar gawar.

Na biyu kuma a koyi wani ɓoyayyan sirri na yadda ake ajiye gawarwakin shugabannin Masar, sannan a gano yanayin da gawar take a yanzu.

Na uku kuma shi ne yunƙurin gano musabbabin mutuwar basaraken: shin mutuwa ce ta gaskiya saboda tsufa ko kuma mutuwa ce saboda nutsewa da ya yi a teku?

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Dakarun tsaron Faransa yayin bikin tarbar gawar Fir'auna Ramses II a Paris.

Masana kimiyyar na aikin gano ƙwayoyin halitta na ciki da wajen gawar, kamar ɓargo da gashi da ƙirji da kuma gefen haƙarƙarin gawar, sannan a yi wasu gwaje-gwaje masu yawa kan gawar.

Raɗaɗi da ɓacin rai kan Sarki Ramses II

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Lokacin da ake duba hoton gawar Sarki Ramses a Paris
Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Wani bincike kan ƙwayoyin cutuka da aka yi a ɓangaren ƙafa da dunduniya gawar da kuma kafadarta ta dama ya nuna wasu ƙwayoyin halitta sun kama gawar saboda sauyin da aka samu na yanayi tun lokacin da aka gano gawar a Deir el-Bahari - wanda masanin kimiyyar Faransa, Gaston Maspero ya gano a1881, sannan kuma aka warware naɗin da aka yi wa gawar a ranar 1 ga watan Janairun 1886.

Binciken masana kimiyyar ya nuna yadda ƙashin sama da ƙasan haɓa ke murmushewa sakamakon taruwar ruwa a wajen.

Hoton masana kimiyya ya nuna yadda aka samu zaman ruwa na zama da shekaru a ɓangaren haƙora.

Sai dai binciken bai nuna an taɓa yi wa sarkin aikin haƙori ba lokacin yana raye.

Bincike ya nuna kumburi a wajen haƙarƙarin gawar da bayan hannunta, jijiyoyin cinya da ƙafa, ƙashin ƙugun gawar duka ya lalace ga kuma murmushewar gashin kai da yake fama da ita.

Kumburin da aka gano bayan mutuwarsa an ce ya samo asali ne shekaru gabanin ya mutu a ƙarshen shekarun rayuwarsa.

Duk waɗannan na nuna cewa lafiyar fir'aunan ta taɓarɓare, inda ya riƙa fama da cutar sanyin ƙashi a shekaru ashirin na ƙarshen rayuwarsa, kamar yadda nazarin Nabelcore ya nuna.

'Fir'aunan da ya fi kowa a tarihin Misra'

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Zanen Sarki Ramses II

Sarki Ramses na biyu ana masa kallon fir'auna mafi ɗaukaka a tarihin Masar, kuma ɗaya daga cikin mafiya ɗaukaka tsakanin sarakunan duniya.

Yana ɗaya daga ckin sarakuna ƙalilan da suka yi mulkin dogon zamani, inda ake cewa ya kai shekara 67 kan karagar mulkin Misra.

Yana da yara da yawa kimanin 52 maza ne 32 kuma mata ne, kuma shi ne mijin fitacciyar matar nan Sarauniya Nefertari.

Ya sa mutane sun gina mutum-mutumi da hannu a lokacin mulkinsa masu nauyin ton dubu, yanzu suna nan a wajen bautar Ramesseum bayan faɗuwar da suka yi a baya saboda girgizar ƙasa.

Sarki Ramses na biyu ya ɗare kujerar iko ne bayan mutuwar mahaifinsa, Sarki Seti na ɗaya.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Wata majami'a da Sarki Ramses II ya gina a Masar

Ramses II ne Fir'aunan da aka ambata a littafin Injila da Qur'ani?

Asalin hoton, Getty Images

Malaman tarihin da ke bibiyar tarihin Masar sun yi ta bayyana mabambantan ra'ayi kan wannan batu.

Wasu daga cikinsu, ba tare da kafa hujja da wata shaida ta masana kufai ko tarihi ba, sun yi amannar cewa Bani Isra'ila wadda aka ambata a cikin ayoyin Injila da kuma Alƙur'ani ta faru ne a zamanin sarakunan Huksus waɗanda suka mulki Masar.

Wasu ra'ayoyin kuma sun ce sun rayu ne yayin daular Masar ta 18, kamar yadda malaman tarihin Masar suka bayyana, musamman lokacin sarki Thutmose III.

Wasu sun ce an yi Bani Isra'ila lokacin Sarki Amenhotep na biyu.

Yayin da ra'ayi na huɗu suka ce sun yi amannar ya faru ne lokacin Sarki Amenhotep III.

Wasu masu tarihin sun wuce gaba inda suka ce ƙissar Bani Isra'ila ta faru ne bayan mutuwar Sarki Amanhoteo na huɗu "Akhenaten", amma ra'ayin da ya fi zama mafi karɓuwa a tsakanin mutane shi ne labarin Bani Isra'ila ya faru ne lokacin Sarki Ramses na biyu, kuma shi ne ra'ayin da masu shirya fim na duniya da sauran marubuta suka fi nunawa, irin shi aka nuna a shahararren fim ɗin "The Ten Commandments", wanda aka shirya a 1956 wanda Cecil B. Demille ya ba da umarni, a cikin fim ɗin akwai ɗan Amurkan nan Charlotte Heston (a matsayin Annabi Musa) da kuma Yul Brynner (a matsayin Fir'auna).

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Yul Brynner a matsayin Sarki Ramses II a fim ɗin "The Ten Commandments" a 1956.

Wata marubuciya Noblecore ta ce "ko shakka babu zai fi dacewa a ce wannan kissa ta faru ne tsakanin mulkin fir'aunoni tsakanin shekara ta 10 zuwa ta 18, kamar yadda bincikenta ya nuna.

"Saboda babu wasu takardun shaida daga Masar da suka yi nuni kan shekarun da lamarin ya faru.

"Idan har muka dage sai mun fito da matsalolin ƙissar domin mu bayyana lokacin da lamarin ya faru ba za mu iya ba, saboda akwai abubuwan da tarihi bai bayyana ba.

Sunan Musa (yana nufin haihuwa) tabbas asalinsa na Misrawa ne, kuma ya yi daidai da alamun gaɓa ta biyu da ta uku ta sunan Ramesses."

Malamar nan ta tarihi ta Faransa ta ware wani babi guda na gudun hijirar Bani Isra'ila da aka bugata a littafin da Nobelcore da ta wallafa, inda suka ce ƙissar ta faru a ƙarnin mulkinsu na 18 kafin haihuwar Annabi Isa.

Tana cewa: "Musa ya samu kariya ta musamman daga Fir'auna, kuma Sarki Horemheb wanda rikicin Bani Isra'ila ya dabaibaye.

Lokacin da Musa ya kammala karatunsa sai ya koma cikin danginsa.

A wannan lokacin Sarki Seti na ɗaya ya gina wata madatsar ruwa a Delta, sannan ya gina fadarsa a Qantir wadda ta zama mazaunin Ramses na biyu.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Hoton zanen dakarun Fir'auna na nutsewa a ruwa lokacin hijirar Bani Isra'ila.