Mutum 2,360 aka kashe a Najeriya a wata ukun farkon 2026 - Rahoto

Asalin hoton, ADABKA

Lokacin karatu: Minti 3

Kamfanin Beacon Security mai nazarin matsalolin tsaro a yankin Sahel ya ce an ƙara samun taɓarɓarewar al'amuran tsaro a Najeriya cikin watanni uku farkon 2026.

Cikin rahoton wata-wata da kamfanin ke fitarwa ya ce duk da matakan da jami'an tsaron ƙasar ke ɗauka har yanzu matsalar ba ta sauya ba.

Rahoton na Beacon Security ya ce mutum 2,360 aka kashe a Najeriya cikin watanni ukun farkon shekarar 2026 da muke ciki.

Najeriya dai ta jima tana fama da matsalolin tsaro, inda ƴanbindiga a sassan ƙasaer da dama ke kai hare-hare da kashe mutane tare da kama wasu domin neman kuɗin fansa.

Ƙungiyoyin ƴanbindiga irin su Boko Haram da ISWAP da ƴan fashin daji ne ke yawaitar kai hare-hare.

Waɗanne yankuna aka fi samun kashe-kashen?

Asalin hoton, Getty Images

Rahoton ya nuna cewa yankin arewa maso gabashin Najeriya ne kan gaba a samun kashe -kashen cikin wata ukun farkon wannan shekara.

Beacon Security ya ce mutum 801 aka kashe a yankin cikin watannin uku.

Yankin na arewa maso gabashin Najeriya ya yi ƙaurin suna a ayyukan ƙungiyoyin masu iƙirarin jihadim Boko Haram da ISWAP.

A cikin wannan shekara kaɗai an samu manyan hare-haren da waɗannan ƙungiyoyi suka ƙaddamar kan sojoji da fararen hula, ciki har da wanda suka kai garin Ngoshe a cikin watan Maris.

Baya da Yankin arewa maso gabas, yankin da ya biyo baya a samun kashe-kashen shi ne Arewa ta Tsakiyar ƙasar mai fama da rikicin ƙabilanci da na manoma da makiyaya, inda rahoton ya ce an kashe mutum 762.

Yankin arewa maso yammcin ƙasar - mai fama da matsalar hare-haren ƴan fashin daje masu garkuwa da mutane - ne ya zo na uku a samun kashe-kashen, wanda aka kashe mutum 508,

Sai kuma kudu maso gabashi, inda aka kashe mutum 157, da kudu maso kudu mai mutum 64, sai kuma kudu maso gabas da aka kashe mutum 58 cikin watanni ukun farkon 2026.

Jihohin da aka fi samun kashe-kashen

Rahoton na ya kuma fayyace jerin jihohin da ke kan gaba a inda aka samu kashe mutanen a farkon wannan shekarar.

Beacon Security ya ce jihohin da aka fi samun kashe-kashe sun haɗar da:

  • Borno da aka kashe mutum 546
  • Filato mai mutum 203
  • Kwara mai mutum 198
  • Benue mutum 174
  • Katsina mutum 125
  • Kebbi mutum 122

Ya batun garkuwa da mutane?

Rahoton na Beacon Security ya nuna cewa daga 1 ga watan Janairu zuwa 31 ga watan Maris na 2026 an sace mutum 1,175 a faɗin Najeriya.

Ƴanbindiga kan sace mutane domin neman kuɗin fansa, wasu kuma sukan yi garkuwa da su kariya daga hare-haren jami'an tsaro.

''Yankin arewa maso yammacin Najeriya ne kan gaba a yawan mutane da aka yi garkuwa da su, inda aka sace 661, sai kuma arewa ta tsakiya da aka sace mutum 261'', in ji rahoton.

Kamfanin na Beacon Security ya kuma ce yankin kudu maso gabashin ƙasar ne yankin da ba a sace mutane da dama ba a farkon shekarar da muke cikin, inda aka sace mutum 8.

Asalin hoton, NPF

Jihohin da aka fi sace mutane

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Sabon rahoton ya ce jihar Kaduna da ke yankin arewa maso yammcin ƙasar ne kan gaba a sace mutane a watanni ukun farkon wannan shekara.

Ko a ranar Ladadin da ta gabata ma sai da ƴanbindiga suka sace wasu masu ibada a Cocin Evengelika da ke jijar Kaduna.

Beacon Security ya ce a jihar Kaduna kaɗai an sace mutum 296, sai jihohi:

  • Zamfara da aka sace mutum 191
  • Borno mai mutum 125
  • Katsina mutum 95
  • Kwara mutum 93

A cewar alƙaluman Matsayin ta'addanci na duniya (GTI) wanda cibiyar tattalin arziki da zaman lafiya ta wallafa a watan Maris ya nuna cewa an samu ƙaruwar kashe mutane sakamakon ayyuka masu alaƙa da ta'addanci da kashi 46 cikin 100 daga shekarar da ta gabata.

Lamarin da ya sa ta zama ƙasa ta huɗu da ta fi fuskantar matsalar kashe-kashe masu alaƙa da ayyukan ta'addanci, inda take bin bayan Pakistan da Burkina Faso da Nijar.

Beacon Security ya kuma ce ƙaruwar ayyukan ta'addanci a Najeriya ya saɓa wa yadda ake ganin raguwar mace-mace masu alaƙa da ta'addanci a duniya, wanda ya ragu da kashi 28 cikin 100, wani abu da ke nuna ƙaruwar matsalar tsaro a yankin Sahel da Afirka ta Yamma.