'Daga yau ke ba ƴar'uwata ba ce' - yadda yaƙi ke raba kan ƴan'uwan juna a Iran

Asalin hoton, Supplied

Bayanan hoto, Ɗaya daga cikin mutanen da BBC ke magana da su ne ya ɗauki wannan hoto na abin fashewa a Tehran a tsakiyar watan Maris
    • Marubuci, Ghoncheh Habibiazad
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News Persian
  • Lokacin karatu: Minti 6

"Ya faɗa mata: 'Daya yau ke ba ƴar uwata ba ce', ita kuma ta faɗa masa sai me."

Wannan cacar baki tsakanin wani mutum da ƴar uwarsa a wani gari kusa da Tehran - wanda ɗaya daga cikin ɗan uwansu ya gani - yana nuna yadda yaƙin Iran ke raba kan iyalai da ƴan uwa yayin da Amurka da Isra'ila ke ci gaba da kai hare-hare.

Ɗan uwan mutanen, da muke kira Sina, ya ce lokacin da ƴan uwan suka haɗu a gidan kakarsu, an samu ɓacin-rai nan da nan, abin da ke nuna rarrabuwar kawuna.

Kawunsu, mamban mayaƙan sa-kai na Basij waɗanda yawanci ake tura wa don murkushe masu sukar gwamnati a Iran - ya ki gaishe da ƴar uwarsa ta jini, wadda ke adawa da gwamnatin da ke mulki.

Bayan haka, kawun nasu ya zauna "shiru... sannan bai daɗe ba ya fita," in ji Sina.

Shi tare da wasu matasa Iraniyawa sun kwatanta yadda ake samun saɓani tsakanin ƴan uwa yayin da ake ci gaba da gwabza yaƙi,

Ko a cikin waɗanda ke adawa da gwamnatin, akwai rarrabuwar kawuna kan cewa ko yaƙin zai taimaka ko kuma kawo tsaiko wajen samun cigaba.

Duk da katse hanyoyin intanet da gwamnati ta yi, BBC ta samu damar ci gaba da tuntuɓar wasu ƴan Iran kalilan waɗanda suka nemi hanyoyin samun intanet.

Duk ɗan Iran da aka samu yana tattaunawa da kafofin yaɗa labarai na ƙasashen waje za a tura shi gidan yari. Sai dai, duk da haka, a tsawon wata ɗaya da aka shafe ana yaƙi, waɗannan mutanen sun yi ta aika bayanai ta hanyar sakon karta-kwana da kuma sakon murya.

Da farko sakonninsu sun kasance na tsoro da firgici, amma yanzu sun fara saba wa, inda suke sauya wurare da kuma hanya. Sun ce suna yawan yin wasan motsa jiki na yoga duk da ƙarar abubuwan fashewa, cin kek na murnar ranar haihuwa su kaɗai da kuma fita zuwa kantunan sayar da gahawa waɗanda mutane kalilan ke zuwa.

Sannan a wasu sakonnin bazata, sun bayyana yadda yaƙin ke shafar yanayin mu'amalarsu. Mun sauya duka sunayen da ke cikin wannan labari.

Asalin hoton, Supplied

Bayanan hoto, Maral ta aika wannan hoto na cincin da aka soya lokacin bikin sabuwar shekaraer Farisawa a Tehran, wajen da mutane suka koma rayuwa da jin ƙarar abin fashewa
Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

A karshen watan Maris, ƴan Iran sun yi bikin Nowruz, wato sabuwar shekarar Farisawa, kuma lokaci ne da iyalai ke haɗuwa wuri ɗaya.

Sina, wanda ya haura shekara 20, yana adawa da bikin kuma yana ci gaba da nuna goyon baya ga hare-haren Isra'ila da Amurka, inda yake fatan cewa hakan zai taimaka wajen kifar da gwamnatin ƙasar.

Ya ce kawunsa, mamban rundunar Basij, wanda bai halarci bikin ba a shekarun baya-bayan nan wanda ya haɗa iyalansu, ya samu zuwa wannan karon, inda kowa ya cika da mamaki cikin ƴan uwansa. Da ma ba mu cika magana da shi ba, har ma da ƴaƴansa", in ji Sina.

Ya ce bai sake magana da kawunsa ba tun lokacin zanga-zangar 2022 da ya janyo mutuwar matashiya Mahsa Amini a hannun jami'an tsaro, wadda aka zarga da kin saka hijabi.

A baya-bayan nan, rundunar Basij da sauran jami'an tsaro sun yi ta murkushe masu zanga-zanga a Iran wadda ta karaɗe faɗin ƙasar a watan Disamba da kuma Janairu. Aƙalla mutum 6,508 ne aka kashe sannan an kama 53,000, a cewar ƙungiyar kare hakkin ɗan'adam a Amurka.

Sina ya ce, wasu ƴan uwansa sun ce kawunsa ya fusata sosai da zanga-zangar wadda ya ce ko da yaransa ne suka fita aka kashe su, ba zai je karɓan gawarsu ba.

Duk da haka, Sina ya ce, kawunsa yana "tsoron mutuwa" a yaƙin da ake yi kuma alamu sun nuna yana kokarin kyautata alakarsa da wasu ƴan uwa, ciki har da mahaifiyarsa.

Lokacin bikin sabuwar shekarar ta Farisawa (Nowruz), kawun da matarsa "na cikin wani yanayi", in ji Sina. "Ban shiga wani takun tsaka da su ba. Ya kamata suna gidan yari."

Asalin hoton, Supplied

Bayanan hoto, Iyalai da dama na haɗuwa wuri ɗaya don bikin sabuwar shekarar Farisawa

Shi ma wani matashi, Kaveh daga Tehran, ya yi bikin shi kadai.

Ya ce alaƙarsa da ƴar uwarsa, wadda ita ma mamba ce a rundunar Basij, ta riga ta zama mai wahala. Bayan ya shiga zanga-zangar 2022, tayi ta sukar harkokinsa kuma ta nuna halin ko'in kula kan mutuwar abokansa a zangaz-zangar watan Janairu.

Kaveh ya kasance yana samarwa ƴan uwansa da kuma abokai hanyoyin intanet. A Iran, mallaka ko amfani da hanyar intanet na Satarlink haramun ne kuma hukuncinsa shi ne zaman gidan yari na shekara biyu.

Da farko ya haɗu da ƴan uwansa don murnar bikin, sai dai ya ce ya bar wajen da suke zama, inda daga baya ya koma ya samu ƴar uwarsa ta lalata hanyar intanet da ya haɗa da kuma sauran na'urori. Lokacin da ya kalubalance ta, daga nan musu ya ɓarke, in ji shi.

"Ba zan iya ci gaba da jurewa ba... na faɗa mata ya isa haka kuma ba zan lamunci hakan ba sanna na bar wajen," in ji shi.

"Ina farin ciki sosai da bikin sabuwar shekarar. Na haɗa kayana don na tafi na samu ƴan uwana," kamar yadda Kaveh ya faɗa. "Amma a yanzu ba na jin komaia kan bikin."

Iraniyawa da dama ba su da hanyar samun intanet. Samun Starlink yana tsada kuma haramun ne amfani da shi a ƙasar, don haka waɗanda ke da shi sun kasance masu kuɗi. Wasu kalilan ne ke samun amfani da wasu hanyoyi.

Iraniyawa da dama da suka amince su tattauna da sashen Farisa na BBC na adawa da gwamnati mai mulki.

Sai dai akwai bambancin ra'ayi kan tasirin wannan yaƙi har cikin masu sukar gwamnatin.

A cewar ƙungiyar agaji ta Red Cross da kuma Red Crescent, hare-haren Amurka da Isra'ila sun kashe mutum 1,900 a Iran, yayin da ƙungiyar kare hakkin ɗan'adam ta HRANA ta ce duka mutanen da aka kashe sun kai 3,400, inda sama da fararen hula 1,500 suke ciki.

Maral, wadda ɗaliba ce da ta haura shekara 20 da ke zama a birnin Rasht a arewacin Iran, ta ƙara fusata da mahaifinta saboda ci gaba da goyon bayan yaƙin da ake yi.

Ya kasance yana goyon bayan tsohon ɗan tsohon sarkin Iran Reza Pahlavi.

A yanzu Pahlavi na zaune a Amurka kuma yana ayyana kansa a matsayin wanda zai iya karɓar mulkin ƙasar. Yana goyon bayan hare-haren Amurka da Isra'ila kan Iran duk da mutanen da ake kashewa. Ya kwatanta hare-haren a matsayin "ɗaukin jin-kai" inda ya buƙaci Amurka kada ta sassauta.

Yana samun goyon baya a Iran a baya-bayan nan, inda wasu masu zanga-zanga suka yi ta kiran sunansa a watan Janairu.

"Ina son yakin nan ya zo karshe nan ba da jimawa ba," a cewar Maral. "Mutane da dama sun mutu."

Ta ce tana jin "haushi" saboda mahaifinta na ci gaba da goyon bayan yaƙin, duk da irin ruwan bama-bamai da ake yi.

"Mun yi kokarin yi masa magana, amma ya ci gaba da ambaton sunan ɗan tsohon sarkin ƙasar," in ji ta.

"Mahaifina yana cikin tunanin cewa Iran za ta buɗe iyakokinta kuma cikin shekara biyar za a sake gina komai, komai zai koma kamar yadda yake. Ya yarda da farfagandar Isra'ila cewa ƙasashen biyu za su zama abokai."

Mahaifinta da kuma mahaifiyarta sun sha yin mujsu kan Pahlavi, in ji Maral.

Asalin hoton, Supplied

Bayanan hoto, Duk da irin ɓarnar da aka yi a titunan Tehran, wasu mutane na zuwa kantunan sayar da abinci

Ita kuwa, Tara, wata ƴar shekara 20 a Tehran , ta ce ƴan uwanta sun yi ta sukarta saboda nuna adawa da yaƙin.

"Dukkansu suna goyon bayan kai hari kan Iran... mahaifiyata da yar uwata sun faɗa min cewa: "Ba ki rasa kowa ba a zanga-zanga, shi ya sa kike adawa da yaƙin. Ba ki son a kawo maki tsaiko a harkokin ki na yau da kullum irinsu zuwa shan gahawa... idan wannan gwamnatin ta kashe ɗaya daga cikin kawayenki ko ƴan uwa (lokacin zanga-zanga) ba za ki yi adawa da yaƙin ba."

Sai dai Tara ta ce: "An kashe dubban mutanen da ba su aikata komai ba a wannan yaƙin, ba tare da wani ya tuna da su ba."

Duk da haka, ta ce ra'ayin ƴar uwarta - kamar sauran mutane da dama waɗanda BBC ta tattauna da su - ya ɗan ragu na goyon bayan yaƙin yayin da ake ci gaba da kai hare-hare. Musamman ma a baya bayan-nan da aka kai hari kusa da inda muke, ta ce ƴar uwarta ta faɗa cewa: "Ina fatan wannan yaƙin zai kare nan kusa."

Duk da irin bambancin ra'ayi da suke da shi, iyalan suna yin komai tare da afiya wurare, in ji Tara. Ta hakan, "dukkan mu za mu mutu tare idan aka far mana".