Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Kasuwar 'yan kwallo: Makomar Rice, Garcia, Havertz, Torreira, Sarr, Sessegnon, Tomori
Chelsea tana son tara £65m ta hanyar sayar da wasu 'yan wasanta da zummar samun kudin sayo dan wasan West Ham mai shekara 21 dan kasar Ingila Declan Rice, in ji jaridar (Star).
Barcelona za ta ware £14m don sayo dan wasan Manchester City dan kasar Sufaniya mai shekara 19 Eric Garcia bayan ya gaya wa City ba zai sabunta kwangilarsa ba. (Goal)
Dan wasan Bayer Leverkusen dan kasar Jamus Kai Havertz, mai shekara 21, yana iya isa Chelsea a makon gobe a kan £71m, yayin da Bayern Munich ta daina sha'awar daukarsa. (Star)
AC Milan na so dauko dan wasan Arsenal da Uruguay Lucas Torreira, mai shekara 24, wanda aka daina damawa da shi a Emirates a karkashin jagorancin Mikel Arteta. (Telegraph - subscription required)
Dan wasan Watford da Senegal Ismaila Sarr, dan shekara 22, yana cikin 'yan kwallon da Liverpool take son daukowa a bazara. (Liverpool Echo)
Ajax na son karbo aron dan wasan Tottenham dan kasar Ingila Ryan Sessegnon, mai shekara 20. (Telegraph - subscription required)
Rennes ta soma tattaunawa da zummar dauko dan wasan Chelsea da Ingila mai shekara 22 Fikayo Tomori. (L'Equipe - in French)
Wolves za ta soma tattaunawa kan sabunta kwangilar kocinta Nuno Espirito Santo. (Mail)
Manchester United tana zawarcin golan Napoli da Italiya mai shekara 23 Alex Meret. (Star)
Everton tana son dauko dan wasan Atletico Madrid da Faransa Thomas Lemar. (Le10 Sport - in French)
Tottenham ta yi nisa a tattaunawar da take yi da Inter Milan domin dauko dan wasan Slovakia Milan Skriniar, wanda Liverpool da Manchester United suke zawarci. (Tuttosport via Sport Witness)
Leeds na duba yiwuwar kashe £15m don dauko dan wasan Liverpool da Wales mai shekara 23 Harry Wilson. (Sun)
Newcastle tana son kulla yarjejeniyar karbo aron Wilson, wanda ya kwashe kakar wasan da ta wuce yana zaman aro a Bournemouth, kuma tana son dauko dan wasan Chelsea mai shekara 20 dan kasar Ingila Conor Gallagher. (Northern Echo)
Crystal Palace za ta fafata da Fulham a yunkurin dauko dan wasan Southampton dan kasar Ingila Harrison Reed. Dan wasan mai shekara 25 ya kwashe kakar wasan da ta wuce yana zaman aro a Craven Cottage. (Football Insider)
Arsenal, Juventus da kuma Manchester City suna gogayya domin dauko dan wasan Lyon da Faransa mai shekara 22 Houssem Aouar. (L'Equipe via Mail)