Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sassan duniya

Wannan shafi na kawo muku bayanai kai tsaye dangane da al'amuran da ke faruwa a Najeriya da sassan duniya

Rahoto kai-tsaye

Usman MINJIBIR da Abdullahi Bello Diginza

  1. UAE ta dakatar da jigilar mai a matatar Fujairah

    Fujairah

    Asalin hoton, Reuters

    Kamfanin man fetur na Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa ya dakatar da jigilar mai a matatarsa da ke Fujairah bayan harin jirgi mara matuƙi da Iran ta kai.

    Matatar dai tana kusa ne da hanyar shiga mashigar Hormuz. Tun da farko, jirgi mara matuƙi da aka harba a filin jirgin Dubai ya janyo tsaiko a sufurin jirgin sama.

    Ita ma dai Iran ta ce ta kai wasu hare-hare a birane uku mafiya girma a Iran, sannan ta ce ta tarwatsa wani gida a Tehran da ake amfani da shi wajen kitsa hare-hare.

    Ita dai Amurka ta nace cewa babban burinta shi ne daƙile barazanar makaman Iran masu linzami da jirage marasa matuƙa da sojin ruwa da kuma hana ƙasar ƙera su.

  2. Zakkatul Fitr: Waɗanda ke bayarwa da waɗanda ake ba wa

    Shinkafa

    Asalin hoton, Getty Images

    Malamai sun ce bisa nassi an fara Zakkar Fidda-kai bayan hijirar Annabi Muhammad SAW da shekara biyu, wato a shekarar da aka wajabta Azumin Ramadan, saboda haka Sunna ce mai karfi da ke da nufin wanzar da zaman lafiya tsakanin al'ummar Musulmai.

    Malam Halliru Maraya, malamin addinin Musulunci a Najeriya wanda BBC ta tuntuɓa a kwanakin baya ya lissafa wasu abubuwa guda uku da ya ce su ne dalilin da ya sa ake yin Zakkar Fidda kai a tsakanin Musulmi.

  3. Kyiv ya fuskanci hare-hare masu zafi

    Kyiv

    Asalin hoton, Reuters

    Babban birnin kasar Ukraine ya fuskanci wani hari ta sama da tsakar rana, wani abu da ba a saba gani ba.

    Jirage marasa matuka na Rasha sun yi ta kai hari Kyiv har na tsawon mintuna casa'in, a yayin da mazauna yankin ke tafiya wuraren aiki.

    Baraguzan jirage marasa matuƙa sun yi ta fadawa tsakiyar birnin na Kyiv, sai dai ba a samu rahoton asarar rai ba. Haka zalika an kai kai hari a birnin Kharkiv, inda mutum daya ya jikkata.

    Wannan dai na zuwa ne a daidai lokacin da Rasha ta sanar da dakile harin jirgi mara matuƙi mafi girma na Ukraine a birnin Moscow, inda ta harbo ko kuma lalata jirage marasa matuka 250 a karshen mako.

  4. Tarayyar Turai ta ce za ta kai agaji zuwa Gabas ta Tsakiya

    ..

    Asalin hoton, Getty Images

    Kungiyar Tarayyar Turai ta ce za ta kai agajin jin ƙai na sama da dala miliyan ɗari biyar ga kasashen yankin Gabas ta Tsakiya da kuma wasu ƙasashen da ke karbar 'yan gudun hijira.

    Kaso mafi girma, wato sama da dala miliyan ɗari biyu, zai je Siriya domin samar da taimakon abinci, kiwon lafiya, matsugunai da sauran muhimman abubuwa.

    Sauran kuma za a raba ne tsakanin Lebanon da Falasdinawan da ke Gaza da kuma gabar yamma da kogin Jordan da aka mamaye.

    Ƙungiyar ta kuma ce Jordan da Masar ma za su sami tallafin, don taimaka wa dimbin 'yan gudun hijira da masu neman mafaka da ke ƙasashensu.

  5. Isra'ila ta ce ta shirya yaƙi da Iran har mako uku mai zuwa

    ..

    Asalin hoton, Getty Images

    Isra'ila ta ce tana da shiri na musamman domin ci gaba da gwabza yaƙi a Iran na tsawon makonni uku masu zuwa.

    Ƙasar ta ce ta kai wasu hare-hare a birane uku mafiya girma a Iran, sannan ta yi ikirarin cewa ta tarwatsa wani gida a Tehran da ake amfani da shi wajen kitsa hare-hare.

    Ita ma dai Iran ta ce tana ci gaba da mayar da martani, a birane da garuruwan Isra'ila, inda hotunan da ke fitowa ke nuna irin ɓarnar da hare-haren na Iran ke yi wa Isra'ilar.

    Bugu da ƙari, Iran ɗin ta kai hari filin jirgin saman Dubai da cibiyar man fetur ta Fujairah mallakin Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa.

    Wakiliyar BBC ta ce akwai kuma wani makami mai linzami da ya faɗi kan wata mota a Abu Dhabi, inda ya kashe wani farin hula ɗan asalin yankin Falasɗinu.

    Sai dai kafar watsa labaran Iran ta ruwaito an samu mace-macen mutane a hare-haren Amurka da Isra'ila, sannan ƴan ƙasar ƙalilan ne ke shirye-shiryen gudanar da bikin Nowroz da ake yi na sabuwar shekara a ƙasar.

  6. Jamus da Burtaniya sun ce ba za su shiga yaƙin Iran ba

    ..

    Asalin hoton, Getty Images

    Jamus da Birtaniya sun ce ba su ga wata rawar da za su taka ba a yaƙin da ake yi da Iran.

    Jamus ta jaddada cewa wannan rikici ba shi da alaƙa da ƙungiyar tsaro ta Nato, kuma ba za ta tura sojoji ba don taimakawa wajen shawo kan rufe mashigin Hormuz da Iran ta yi.

    Firayim Ministan Birtaniya, Keir Starmer, ya ce ba ya son a ƙara jawo shi cikin rikicin Gabas ta Tsakiya, amma ya ce London na aiki tare da ƙawayenta a kan wani shiri na tabbatar da buɗe mashigin.

    "Wajibi ne mu sake buɗe mashigin Hormuz, domin samar da daidaito a kasuwar man fetir ta duniya, wannan ba abu ne mai sauƙi ba," in ji Kier Stermer.

    Tun da farko dai, shugaba Trump ya ce ba za su ji daɗin abin da zai faru ba in dai ƙasahsen ƙungiyar ta NATO suka ƙi taimakawa.

  7. Abin da ya faru da jirgin ƙasan Kaduna zuwa Abuja

    ..

    Asalin hoton, NRC

    Hukumar sufurin jirgin ƙasa ta Najeriya ta ce hatsarin da jirgin Kaduna zuwa Abuja ya yi da safiyar ranar Litinin karo ne ba sauka daga kan titinsa ya yi ba.

    Hukumar ta ce tarago ne ya bugi na kusa da shi sakamakon matsalar igiyar da ta haɗa su.

    RCN ta ce wasu daga cikin fasinjoji sun samu rauni inda kuma aka kai su asibiti mafi kusa da inda abin ya faru domin kula da lafiyarsu.

    Kuma bayan hakan an samu damar tuƙa jirgin har zuwa tasharsa ta Idu abin da ke nuni da cewa ba sauka ya yi daga kan kwangirin nasa ba.

  8. EU ta za kai agajin dala miliyan 500 zuwa Gabas ta Tsakiya

    Ƙungiyar Tarayyar Turai ta ce za ta kai agajin jin ƙai na sama da dala miliyan 500 ga ƙasashen yankin Gabas ta Tsakiya da kuma wasu ƙasashen da ke karɓar ƴan gudun hijira.

    Kaso mafi girma, wato sama da dala miliyan ɗari biyu, zai je Siriya domin samar da taimakon abinci da kiwon lafiya da matsugunai da sauran muhimman abubuwa.

    Sauran kuma za a raba ne tsakanin Lebanon da Falasɗinawan da ke Gaza da kuma Gaɓar Yamma da Kogin Jordan da aka mamaye.

    Ƙungiyar ta kuma ce ƙasashen Jordan da Masar ma za su sami tallafin, don taimaka wa ɗimbin ƴangudun hijira da masu neman mafaka da ke ƙasashensu.

  9. Ɓarnar da hare-haren Iran suka haifar a Isra'ila

    ..

    Asalin hoton, ..

    Wani harin makami mai linzami ya haifar da ɓarna da raunaka a cikin Isra'ila.

    ƴansandn Isra'ila sun ce mutum uku sun samu ƙananan raunuka bayan da bom mai ƴaƴa ya tashi a kusa da birnin Tel Aviv.

    Kamfanin dillancin labarai na AP ya bayar da rahoton cewa hare-haren Iran sun kashe mutum 12 a Isra'ila tun bayan fara yaƙin.

    An ci gaba da musayar hare-haren tsakanin ƙasashen biyu a tsawon daren da ya gabata.

    A halin da ake ciki kuma, Isra'ila ta sanar da wani sabon salon kai "manyan hare-hare " a wasu wuraren yammcin Iran

  10. Isra'ila ta ce ta kai hari 'tsakiyar Tehran'

    Sojojin Isra'ila sun ce sun lalata wani gida mallakin gwamnatin Iran a wani ''hari ta da kai tsakiyar Tehran'', babban birnin Iran.

    Cikin wata sanarwa da dakarun tsaron Isra'ilar suka fitar, sun ce sojojinta na sama sun yi aiki da bayanan sirri wajen lalata wani gini mallakin gwamnatin Iran.

    ''Ana amfani da ginin wajen kitsa hare-hare kan taurarin ɗan'adam, wani abu da ke barazsana ga taurarin ɗan'adam na ƙasashen duniya.''

  11. 'Iran ta kai hare-haren makamai masu linzami kan Isra'ila'

    Iran

    Asalin hoton, Getty Images

    Dakarun juyin juya halin Iran sun ce sun ƙaddamar da jerin hare-haren makamai masu linzami da na jirage masara matuƙa kan filayen jirage da sansanonin soji da cibiyoyin ƙera makamai a biranen Tel Aviv da Ben Gurion.

    Cikin wata sanarwa da rundunar ta fitar ta ce ta yi amfani da samfura daban-daban an makamai masu linzami da jirage masara matuƙa masu lalata wurare.

    Haka kuma rundunar ta IGRC ta ke ta kai hari kan sansanonin sojin Amurka da ke Al-Dhufra da Jufeir da Seikh Issa a yankin Gabas ta Tsakiya.

    Sansanin sojin sama na Al Dhafra mai nisan tazarar kilomita 30 daga binrin Abu Dhabi, shi ne kuma shalƙwatar sojojin saman Amurka a yankin.

    A cewar kamfanin dillancin labarai na Fars Amurka da Isra'ila sun kai hari gabashin birnin Tehran.

  12. China ta nemi ɓangarorin da ke yaƙi da juna su dakata

    ..

    Asalin hoton, Getty Images

    Bayan da shugaban Amurka ya yi wa China barazanar janye batun ganawa da Xi Jinping na China, a yayin wata hira da mujallar British Financial Times, kan ƙin taimakawa wajen buɗe mashigar Hormuz da ƙasar Iran ta datse.

    Mai magana da yawun da ma'aikatar harkokin wajen China, Lin Jian ya ce "batun diflomasiyya tsakanin Amurka da China ba abu ne da za a iya kawar da kai daga barin sa ba," inda ya ƙara da cewa "ƙasashen biyu na tattaunawa dangane da ziyarar Trump ɗin."

    Dangane kuma da batun rufe mashigar Hormuz, Lin Jian ya ce tankiyar da ake yi ta daƙile sufurin makamashi da zaman lafiyar duniya da sassa.

    "China ta nanata kiranta ga dukkan ɓangarorin da su dakatar da ayyukan soji," in ji Jiang inda ya ƙara da cewa "kuma mun duƙufa wajen tabbatar da an tsagaita wuta."

  13. Halin da farashin mai ke ciki a duniya

    ..

    Asalin hoton, Reuters

    Farashin makamashi ya tsaya a kimanin dala 100 tun bayan da shugaban Amurka, Donald Trump ya sanar da yin luguden wuta a tsibirin Kharg, wani wuri mafi muhimmanci ga ƙasar Iran dangane da fitar da mai.

    Sai dai rahotanni sun ce kasuwar man a yankin Asiya na cike da rashin tabbas.

    Farashin ɗanyen mai dai a kasuwar mai ta Amurka ya faɗi da kusan kaso shida cikin 10 na farashinsa na $14.98 a kowace ganga, inda shi kuma man nau'in Brent ya zama kimanin $103.17 ba tare da wani sauyi ba.

    Duk da cewa dai ƙasashe mambobi ƙungiyar ƙasashe masu yawan makamashi sun sha alawashin sakin ganga miliyan 400 daga rumbun ajiyarsu domin daidaita farashin man a kasuwar duniya, farashin man har yanzu ya hauhawa fiye da farashin asali kafin fara yaƙi.

  14. Tarayyar Turai na duba yiwuwar buɗe mashigar Hormuz

    ..

    Asalin hoton, Getty Images

    Babban jami'i mai tsare-tsare na Tarayyar Turai, Kaia Kallas ta ce ƙasashen Tarayyar Turai na shirin fara tattaunawa kan matakan da tarayyar za ta dauka wajne tabbatar da buɗe mashigar Hormuz.

    "Yana daga cikin muradanmu tabbatar da cewa mashigar Hormuz ta kasance a buɗe," in ji Kallas, gabanin taron ministocin harkokin waje na tarayyar a Brussels, kamar yadda Reuters ya rawaito.

    Wannan dai ba ya rasa nasaba da kiran da shugaban Amurka, Donald Trump ya yi wa ƙasashen na Turai da ma na ƙungiyar tsaro ta Nato da su taimaka wajen tabbatar da cewa mashigar ta kasance a buɗe.

    Ofishin firaiministan Burtaniya ya sanar ranar Lahadi cewa Mista Trump ya tattauna da firaiministan Burtaniyar, Keir Starmer dangane da muhimmancin buɗe mashigar ta Hormuz domin daƙile yanayin da sufurin makamashi ke fuskanta a duniya.

  15. An dakatar da sauka da tashin jirage a Dubai

    ..

    Asalin hoton, Getty Images

    Hukumomi a Dubai sun sanar da tsagaita sauka da tashin jirage na wani ɗan lokaci "domin tabbatar da lafiyar fasinjoji da ma'aikata".

    Kafin nan dai an rahotanni sun ce ma'aikatan agajin gaggawa sun yi fama da wata wuta da ta tashi a filin mai alaƙa da harin jirgi maras matuƙi da ya lalata tankin mai.

    An nemi fasinjoji da su nemi bayanan sauka da tashinsu daga wurin kamfanonin da suke hulda da su.

    Kafin dai fara yaƙin da Amurka da Isra'ila suka ƙaddamar kan Iran, filin jirgin saman na Dubai shi ne wanda ya fi kowanne hada-hadar sauka da tashin jirage a duniya inda fasinjoji miliyan 90 suka yi amfani da filin a 2025.

  16. Ma'aikatan jirgin Thailand da harin Iran ya rutsa da su sun isa gida

    ..

    Asalin hoton, Reuters

    Ma'aikatan jirgin ruwan nan na Thailand - wanda harin makami mai linzami na Iran ya fada masa a makon da ya gabata, ya kuma kama wuta a mashigin Hormuz, su 20 sun isa Thailand din.

    Akwai wasu mutum uku da ba a gan su ba har yanzu a cikin ma'aikatan, kuma an yi amanna harin ya rutsa da su a cikin jirgin na dakon mai, me suna Mayuree Naree, wanda aka fice aka bar shi bayan harin.

    Wakilin BBC ya ce jirginsu na daya daga cikin sama da gomman jiragen ruwa na kasuwanci da Iran ta kai wa hari, bayan da ta yi gargadin cewa za ta datse mashigin na Hormuz.

    Gwamnatin Thailand ta gabatar da korafinta ga Iran din a kan harin , ta kuma bukaci taimakonta wajen ceto ragowar ma'aikatan.

    ..

    Asalin hoton, Getty Images

  17. Isra'ila da Iran na ci gaba da yi wa juna luguden wuta

    ..

    Asalin hoton, Getty Images

    Bayanan hoto, Wasu gine-gine da hare-haren Iran suka rugurguza a arewacin Isra'ila.

    An bayar da rahotannin fashewa da tashin hayaki a babban birnin ƙasar Iran, Tehran, yayin da Isra'ila ta ce tana faɗaɗa hare-haren da take kaiwa.

    Ita ma Iran ta sanar da ci gaba da kai hare-haren ramuwar-gayya a faɗin biranen Tel Aviv da Jerussalam da sauran yankunan Isra'ila.

    Hare-haren na ramuwar gayya na Iran na ci gaba da ta'azzara a ƙasashen yankin Gabas ta Tsakiya inda muradan Amurka suke. Iran ta ce tana kai wa muradan Amurka hari ne ba ƙasashe masu maƙwabtaka ba.

    An sake rufe filin jirgin sama na Dubai bayan wani harin jirgin sama maras matuƙi da aka kai ya tayar da wuta a wani tankin mai da ke kusa.

    Can ma a Iraqi jami'ai sun tabbatar da raunata mutum biyar a wani harin roka da aka kai filin jirgin sama na Baghdad, inda ofishin jakadancin Amurka yake.

    Shugaba Trump na Amurka ya sake cewa ana tattaunawa da jami'an Iran, to amma kuma ministan harkokin wajen Iran ya musanta hakan tun da farko.

    Wannan dai ba shi ne karon farko ba da Shugaba Trump ke iƙrarin tattaunawa da Iran amma kuma shugabannin Tehran su musanta, wani abu da masana ke yi wa kallon kamar Amurkar ta gaji da yaƙin.

  18. Japan ta fara fitar da mai daga rumbun ajiyarta

    ..

    Asalin hoton, Getty Images

    Japan ta fara fitar da ɗimbin man da take ajiye da shi - bisa raɗin kanta, domin ta taimaka wajen rage damuwar da ake nunawa kan ƙarancin man da yaƙin Iran ya haddasa.

    Japan ɗin ta yi haka ne tun ma kafin fara gudanar da shirin haɗin guiwa da aka tsara yi na fitar da man da ƙasashe - mambobin hukumar makamashi ta duniya suke da shi, ƙasashen da suka hada da ita Japan din.

    Kasar ta dogara ne sosai a kan yankin Gabas ta Tsakiya wajen samun mai, kuma ta tara man da yana ɗaya daga cikin mafi yawa da aka adana a duniya.

    Japan ta tanadin man ne tun bayan da ta shiga halin ƙa-ƙa-ni-ka-yi na ƙarancin man a duniya da aka shiga a shekarun 1970, sakamakon dambarwar siyasar Gabas ta Tsakiya.

  19. Me ya sa Trump ke neman ɗauki daga ƙungiyar NATO?

    ..

    Asalin hoton, Getty Images

    Shugaba Trump ya ce yana tattaunawa da ƙasashe da dama domin taimakawa wajen ƙwace ikon mashigin Hormuz a daidai lokacin da yaƙinsa da Iran ke ci gaba da illa ga tattalin arzikin duniya.

    Sai dai Mista Trump ya yi gargaɗi ga ƙungiyar tsaro ta NATO idan har ba ta taimaki Amurka ba.

    "NATO za ta fuskanci mummunar makoma," kamar yadda shugaban ya bayyana a wata hira da ya yi da jaridar Financial Times.

    Shugaban ya sake yin kira ga ƙasashe su shiga ƙoƙarin tabbatar da buɗe mashigar Hormuz da yake yi domin ba jiragen ruwa damar tsallake shingen Iran.

    Ya ce Amurka ta taimaka wa Ukraine a yaƙinta da Rasha, don haka yana tsammanin taimakon ƙasashen Turai kan babbar hanyar ruwa ta Hormuz da Iran ta toshe.

  20. Buɗewa

    Masu bibiyarmu barkan ku da safiyar ranar Litinin da Hausawa ke yi wa kirari da tushen aiki. A wannan rana ma mun sake dawowa kamar kullum da rahotanni da bayanai na musamman dangane da irin wainar da ake toyawa a faɗin duniya.

    Da fatan za ku ci gaba da kasancewa da shafin na kai tsaye na BBC Hausa domin ci gaba da samun zafafan labarai da ke ɗaukar hankali a Najeriya da sassan duniya.

    Mun gode.