Shekarar da aka yi azumin Ramadan ‘28’ a Saudiyya

wata

Asalin hoton, Getty Images

Lokacin karatu: Minti 3

A shekarar 1984 daidai da shekarar 1404 bayan hijira, Saudiyya ta shaida wani abu da ba a saba gani ba a tarihin ƙasar game da watan azumin Ramadan.

A wannan lokaci watan azumin ya ƙare bayan azumi 28, maimakon 29 ko 30 da aka saba yi kowace shekara.

Wani abu da ya sa ƴan ƙasar imanin cewa ba su kammala azumin ba.

A ƙa'idar Musulunci dai akan fara azumi ne bayan samun labarin ganin jinjirin watan Ramadan, sannan a ajiye bayan samun labarin ganin jinjirin watan Shawwal.

Kuma akan yi azumin Ramadana 29 ko 30 ne a kowace shekara.

Abin da ya faru a wannan shekarar

A daren ranar 28 ga watan Ramadan sai kawai jinjirin watan Shawwal ya bayyana ƙarara a sararin samaniya.

Abin da bayyanar watan ke nufi shi ne ranar 29 ga Ramadan din ce ranar ƙaramar Sallah, wato 1 ga watan Shawwal.

Don haka mutane suka yi sallar idi bayan azumi 28, lamarin da ya haifar da ce-ce-ku-ce a faɗin ƙasar.

Wannan al'amari ya tabbatar da cewa an samu kuskure wajen ganin watan Ramadan a wannan shekarar.

A shekarar, an samu matsalar ganin watan Ramadan, lamarin da ya sa aka jinkirta fara azumin saɓanain ranar da ta kamata a fara.

A cewar kwamitin tantance ganin wata na ƙasar, wani mutum ya zo musu da labarin ganin watan tun da farko, amma kuma bayan tantance ganin nasa da kwamitin ya yi, sai ya gano cewa ba watan ya gani ba, duniyoyin Mercury da Venus ya gani.

Yaya ƴan ƙasar suka yi?

Bayan samun wannan matsala, ma'aikatar shari'ar ƙasar ta umarci ƴan ƙasar su ƙara yin azumi ɗaya, kwana ɗaya bayan ƙaramar salla domin cika azumi 29.

A huɗubar da ya gabatar lokacin sallar idi, limamin da ya ja sallar a babban masallacin Makka ya yi kira ga ƴan ƙasar su ƙara azumi ɗaya kafin ƙarewar watan Shawwal.

Musulunci na bin tsarin kalandar watanni, wadda ta dogara ta tafiyar wata.

Don haka Sha'aban ne wata na takwas a kalandar, daga nan sai Ramadan, a matsayi na tara, Shawwal kuma na 10.

Kalandar tafiyar watanni da ake kira Lunar da Turanci ko Hijir da Larabci na farawa ne da ganin jinjirin wata, bayan haihuwarsa, kuma tsawon wata yakan kama tsakanin kwana 29 zuwa 30.

Tsarin amincewa da ganin wata

Galibi duka ƙasashen Musulmi na da tsarin da suke bi wajen ganin sabon wata a ƙasashensu.

Abin da aka saba da shi ne akwai kwamitocin ganin wata da ke tantance ganin kowane wata a lokacin kamawarsa.

bayan tantancewar, kwamitocin kan fitar da sanarwar ganin wata, idan kuma ba su tabbatar ba sukan fitar da sanarwar cika azumi 30.

Wasu ƙasashen kan dogara da ganin ido ko ta na'urorin hangen nesa, kafin fitar da sanawar.

Amma wasu ƙasashen kan dogara da lissafin ilimin taurari, yayin da wasu kuma ke dogara da hukumomin addini na ƙasashensu ko ganin wata a makwabtan ƙasashe.

Waɗannan bambance-bambance ne ke haifar da saɓani a ranakun fara azumi da na salla a wasu ƙasashen, ko a cikin ƙasa ɗaya.