Manyan kungiyoyin Firimiya da Turai na son Hall, Chelsea ta nace wa Messi

Lewis Hall sanye da jesin Newcastle na tafa hannu

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Lewis Hall ya fara taka wa babbar tawagar Ingila wasa a Nuwamban 2024
Lokacin karatu: Minti 2

Masu farautar 'yan wasa daga Manchester City, da Liverpool, da Arsenal, da RB Leipzig, da Borussia Dortmund, har ma da Barcelona, na sa ido a kan matashin dan bayan Newcastle, Lewis Hall, dan Ingila. (Caughtoffside).

Haka kuma Manchester City, watakila ta sayi, dan bayan Sifaniya Pedro Porro, mai shekara 26, a kasa da farashin da aka yi masa fam miliyan 80, saboda halin rashin kudi da Tottenham ke ciki, idan har ta fadi daga gasar Firimiya. (Football Insider).

Ita ma Sunderland a shirye take ta biya yuro miliyan 15 a kan matashin dan wasan tsakiya Thiago Pitarch, dan Sifaniya mai shekara 18 daga Real Madrid. (Fichajes).

Kungiyoyi a Ingila da kuma wasu kasashen Turai sun tuntubi Liverpool, kan ko za ta sayar musu da mai tsaron ragarta, Giorgi Mamardashvili, dan Georgia, mai shekara 25. (Teamtalk).

Tottenham na nazari a kan masu horad da 'yan wasa har guda takwas domin maye gurbin kociyanta Igor Tudor, wanda ke cikin matsi, inda Sean Dyche, da Mauricio Pochettino, da Roberto de Zerbi ke cikin jerin. (Talksport).

Crystal Palace na shirin gogayya da abokiyar hamayyarta Leeds, wajen zawarcin dan gaban Derby Patrick Agyemang, Ba'amurke mai shekara 25. (Football Insider).

Watakila Chelsea, ta tashi tsaye ta hanzarta cinikin matashin dan wasan gaba na gefe, Rayane Messi, daga Strasbourg, ganin yadda Bayern Munich, da Barcelona, da kuma Paris St-Germain, ke son matashin na Faransa, mai shekara 18. (Teamtalk)