Bola Ahmed Tinubu
An rantsar da Bola Ahmed Tinubu Shugaban Najeriya na 16 a ranar 29 ga watan Mayu
Ya yi gwamnan Jihar Lagos daga 1999-2007
Ya taɓa zama sanata daga Lagos kuma ya samu horo a matsayin akanta
Daga: Africa Visual Journalism Team

Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya rantsar da ministocinsa a ranar Litinin, kimanin wata uku bayan kama aiki.
Majalisar ministocin mai ƙunshe da mutum 45 na cike da tsofaffin gwamnoni da ƴan majalisar dokoki.
Kimanin rabin ministocin tsofaffin gwamnoni ne da tsofaffin ƴan majalisa.
Majalisar ministocin kuma ta ƙunshi ƙwararru daga ɓangarori da dama, kamar lafiya da fasahar sadarwar zamani.
Shugaban ƙasar ya kuma ci gaba da ministoci biyu daga tsohuwar gwamnatin magabacinsa Muhammadu Buhari, wato Heineken Lokpobiri da Festus Keyamo.
Kamar sauran gwamnatocin baya, ban da ta Goodluck Jonathan, mata ba su samu abin da ya kai kashi 20 cikin ɗari na muƙaman ministocin ba.
Ga bayani game da sabbin jiga-jigan gwamnatin Tinubu da kuma rawar da za su iya takawa.
An rantsar da Bola Ahmed Tinubu Shugaban Najeriya na 16 a ranar 29 ga watan Mayu
Ya yi gwamnan Jihar Lagos daga 1999-2007
Ya taɓa zama sanata daga Lagos kuma ya samu horo a matsayin akanta
Kashim Shettima shi ne Mataimakin Shugaban Najeriya mai ci
Tsohon gwamnan Jihar Borno ne kuma tsohon sanata
Ya yi aiki a ɓangaren banki na tsawon lokaci
An naɗa Mohammed Badaru matsayin Ministan Tsaro
Ya yi gwamna a Jihar Jigawa daga 2015 zuwa 2023
Shi ne mai Gungun Masana'antun Talamiz, wani babban kamfani da ke da harkoki a ɓangaren motoci da sarrafa kaya da noma da kuma kiwo
Badaru Abubakar ya kammala Jami'ar Ahmadu Bello, Zariya inda ya samu digiri a fannin Akanta
An naɗa Bello Matawalle Ƙaramin Ministan Tsaro
Ya yi gwamna a Jihar Zamfara wa'adi ɗaya
Yana da horon aikin malanta, kuma ya taɓa zama Ɗan Majalisar Wakilai
An naɗa Olawale Edun Ministan Kuɗi kuma Ministan kula da Harkokin Tattalin Arziƙi
Shi ne Mashawarcin Shugaba Bola Tinubu na Musamman kan Manufofin Kuɗi
Ya taɓa zama Kwamishinan Kuɗi a Jihar Lagos
Ya yi aiki a Bankin Duniya kan tsare-tsaren tattalin arziƙi da harkoki kuɗi na ƙasashen Caribbean da Latin Amurka.
Ya haɗa gwiwa wajen kafa Bankin Stanbic IBTC.
An naɗa Atiku Bagudu Ministan Kasafin Kuɗi da Tsare-tsaren Tattalin Arziƙi
Ya yi gwamna a Jihar Kebbi daga 2015 zuwa 2023 kuma ya taɓa zama sanata.
Amini ne ga Sani Abacha, marigayi ɗan mulkin kama-karya na Najeriya. An taɓa kama shi a Amurka saboda halasta kuɗin haram, batun da ya cimma sasantawa a kan zaɓin a dawo da shi Najeriya.
An naɗa Tahir Mamman, Ministan Ilmi.
Ya kasance shugaban Jami'ar Baze ta Abuja
Kuma shi farfesa ne a fannin shari'a kuma lauya mai muƙamin SAN.
Ya taɓa zama babban darakta a Kwalejin Koyon Aikin Lauya ta Najeriya daga 2005 zuwa 2013.
An naɗa Olubunmi Tunji Ojo, Ministan Cikin Gida
Ya zama ɗan Majalisar Wakilai
Yana da digiri na biyu a fannin Sadarwar Dijital da Musayar Bayanai daga Jami'ar Lodon Metropolitan
An naɗa Tanko Snunu, Ƙaramin Ministan Ilmi
Tanko Sununu, ya kasance Ɗan Majalisar Wakilai daga Kebbi
Ya kasance likitan haihuwa da mata a Cibiyar Lafiya ta Tarayya, Birnin Kudu, inda ya yi aiki tun daga 2012
An naɗa Ali Pate Ministan kula da Harkokin Lafiya da Walwalar Jama'a
Likita ne kuma shi farfesa ne fannin Lafiyar Al'umma a Jami'ar Harvard
Ya taɓa zama Daraktan Lafiya da Abinci mai Gina Jiki da Yawan Jama'a kuma Daraktan Samar da Kuɗi kan Harkokin Mata da Ƙananan Yara da Masu tasowa a Bankin Duniya
An naɗa Tunji Alausa, Ƙaramin Ministan Lafiya da Walwalar Jama'a
Shi ne ya assasa kuma shugaban Cibiyar kula da Ƙoda da Cibiyar kula da Wankin Ƙoda ta Illinois a Amurka
Likitan ƙodan na da gogewar aiki ta tsawon shekara 30 a asibitocin gwamnati da masu zaman kansu
Ana naɗa Ibrahim Geidam, Ministan Harkokin Ƴan sanda
Ya yi gwamna a Jihar Yobe har karo uku kuma sanata ne daga jihar a wa'adi na biyu
Ya samu digirinsa ta farko a fannin Akanta kuma shi mamba ne a Cibiyar Ƙwararrun Akantocin Gwamnati ta Najeriya
An naɗa Imaan Suleiman Ibrahim Ƙaramar Ministar Harkokin Ƴan sanda
Ta kasance Babbar Daraktar Hukumar hana Fasa-ƙwaurin Ɗan'adam kafin a mayar da ita Kwamishiniyar Tarayya a Hukumar kula da 'Yan Gudun Hijira da 'Yan Ci-rani ta ƙasa
Ana naɗa David Umahi Ministan Ayyuka
Ya kasance sanata daga Jihar Ebonyi, inda ya yi gwamna daga 2015 zuwa 2023
An naɗa Ahmed Ɗangiwa, MInistan Gidaje da Raya Birane
Tsohon Manayan Darakta ne a Bankin Ba da Lamunin Gina Gidaje na Tarayya. Shi masanin zanen gine-gine ne
An naɗa Ahmed Tijjani Gwarzo, Ƙaramin Ministan Gidaje da Raya Birane.
Ya taɓa zama Mataimakin Gwamna a Jihar Kano daga 2007-2011
Tijjani Gwarzo a yanzu haka ƙwararren mai bincike ne a Cibiyar Wits School of Governance a Afirka ta Kudu.
Ya samu digirinsa ta farko a fannin kimiyya.
An naɗa Alƙali Ahmed, Ministan Sufuri
Ya taɓa zama sanata daga Jihar Gombe a tsakanin 2010 da 2023
Ya samu digirinsa na farko a fannin Kimiyyar Tattalin Arziƙi
An naɗa Dr Betta Edu Ministar Harkokin Jin Ƙai da Yaƙi da Fatara
Ta kasance Shugabar Mata ta ƙasa a Jam'iyyar APC kuma likita ce
Ta yi digiri na biyu a fannin kula da Lafiyar Al'umma a Ƙasashe masu Tasowa a Kwalejin Nazarin Tsafta da Likitancin Ƙasashe masu Zafi kuma Likitar kula da Lafiya Al'umma daga Jami'ar Amurka ta Texila
An naɗa Waheed Adebayo Adelabu Ministan Lantarki
Tsohon Mataimakin Gwamnan Babban Bankin Najeriya ne sashen Aikace-aikace
Ya yi takarar gwamna ba tare da yin nasara ba a Jihar Oyo a shekara ta 2019. Jami'in akantan ya fara aiki ne da Cibiyar PricewaterhouseCoopers.
An naɗa Abubakar Kyari, Ministan Noma da Wadata ƙasa da Abinci
Ya yi sanata daga daga Jihar Borno a tsakanin 2015 - 2022
Ya yi digirinsa ta biyu a fannin Gudanar da Harkokin Kasuwanci a Jami'ar Webster a St Louis cikin Missourin Amurka
An naɗa Aliyu Sabi, Ƙaramin Ministan Noma da Wadata Ƙasa da Abinci
Ya yi sanata tsawon wa'adi biyu daga Jihar Neja a tsakanin 2015 da kuma 2023
An naɗa Joseph Ustev, Ministan Albaraktun Ruwa da Tsafta
Ya yi digiri na uku a fannin Albarkatun Ruwa da Injiniyancin Muhalli
Ya taɓa zama Darakta a Cibiyar Bunƙasa Sana'o'in Dogaro da Kai a Jami'ar Tarayya ta Noma da ke Makurɗi daga 2013 zuwa 2017
Ya kuma riƙe muƙamin Kwamishina a Ma'aikatar Albarkatun Ruwa da Muhalli ta Jihar Binuwai
An naɗa Bello Muhammad Goronyo, Ƙaramin Ministan Albarkatun Ruwa da Tsafta
Ya taɓa zama Kwamishinan Yaɗa Labarai a Jihar Sokoto
An naɗa Abubakar Momoh, Ministan Raya Neja Delta
Shi injiniyan gine-gine ne kuma ya taɓa zama ɗan Majalisar Wakilai har karo biyu
An naɗa John Eno, Ministan Bunƙasa Wasanni
Ya zama sanata daga Jihar Ribas a tsakanin 2015 da 2019
Ya kuma yi ɗan Majalisar Wakilai da ɗan Majalisar Dokokin Jiha
An naɗa Adegboyega Oyetola, Ministan Arziƙin Teku
Ya zama Gwamnan Jihar Osun daga 2018-2022
Ya fara aiki a ɓangaren inshora bayan ya kammala Jami'ar Lagos da digiri a kan Inshora cikin 1978
An naɗa Bosun Tijani, Ministan Sadarwa, Ƙirƙire-ƙirƙire da Arziƙin Dijital
Da haɗin gwiwarsa aka kamfanin CcHub
Ya yi digiri na uku a fannin Tattalin Arziƙin Bunƙasa Ƙasa da Ƙirƙire-ƙirƙire daga Jami'ar Leicester
Ana naɗa Yusuf Maitama Tuggar, Ministan Harkokin Waje
Ya taɓa zama ɗan Majalisar Wakilai daga 2007 zuwa 2011
Ya kasance Jakadan Najeriya a Jamus tun daga 2017
An naɗa Festus Keyamo, Ministan Sufurin Sama da Bunƙasa Harkokin Samaniya
Ya yi Ƙaramin Ministan Raya Neja Delta da Ƙaramin Ministan Ƙwadago da Samar da Aikin Yi a gwamnatin Buhari
Shi lauya ne kuma ɗan fafutukar kare haƙƙin ɗan'adam
An naɗa Ishak Salako, Ƙaramin Ministan Muhalli
Shi likita ne kuma tsohon Kwamishinan Lafiya a Jihar Ogun
Ya kasance Babban Jami'i a Inuwar Masu Ruwa da Tsaki ta Ogun ta Yamma
An naɗa Uche Nnaji, Ministan Sabunta ƙere-ƙere, Kimiyya da Fasaha
Shi ɗan kasuwa ne
An naɗa Muhammad Idris, Ministan Labarai da Wayar da Kai
Shi ne mawallafin jaridar Blueprint kuma Babban Jami'in Talbijin ta Blueprint
Yana da digiri na biyu a Ingilishi
An naɗa Dr Dorris Aniche Uzoka, Ministar Masana'antu, Kasuwanci da Zuba Jari
Likita amma ta koma harkar banki, ita tsohuwar Kwamishiniyar Kuɗi ce da kula da Harkokin Tattalin Arziƙi a Jihar Imo
An naɗa Shuaibu Abubakar, Ministan Bunƙasa Ƙarafa
Shi Babban Darakta ne a Bankin Stanbic IBTC kuma yana da gogewa a fannin harkar bankin kamfanoni da zuba jari da kula da Kadarori
Ya samu digirinsa ta biyu a Jami'ar Oxford ta Birtaniya da kuma digirin farko da ƙarin ta biyu a Jami'ar Leicester.
An naɗa Dele Alake, Ministan Bunƙasa Ma'adanai
Shi ne Mashawarci na Musamman ga Shugaba Bola Tinubu kan Ayyukan na Musamman da Sadarwa da Tsare-tsare
Ya taɓa zama Kwamishinan Labarai da Tsare-tsare a Jihar Lagos
Shi ɗan jarida ne
An naɗa Uba Maigari, Ƙaramin Ministan Bunƙasa Ƙarafa
Shi tsohon Mataimakin Gwamna ne a Jihar Taraba amma an tsige shi a wani yanayi mai cike da taƙaddama bayan zaɓen 2003
Lauya ne shi
An naɗa Heineken Lokpobiri, Ƙaramin Ministan Albarkatun Man fetur sashen Mai
Ya kasance sanata karo biyu kafin Shugaba Buhari ya naɗa shi Ƙaramin Ministan Noma da Raya Karkara a 2015.
undefined
An naɗa Ekperipe Ekpo, Ƙaramin Ministan Albarkatun Man fetur harkar Gas
Ya taɓ zama ɗan Majalisar Wakilai daga 2007 zuwa 2011
An naɗa Simon Baƙo Lalong, Ministan Ƙwadago da Samar da Aikin Yi
Ya kasance Gwamnan Jihar Filato har karo biyu
An zaɓe ɗan Majalisar Dokokin Jihar Filato a 1998 kuma ya zama Shugaban Majalisar a 2000
Lalong shi ne babban daraktan kwamitin yaƙin neman zaɓen Shugaba Tinubu
Lola Ade-John ce Ministar Yawon Buɗe Ido
Ƙwararriya ce a fannin fasahar sadarwa wadda ta yi aiki a Bankin Access da Bankin UBA da Ecobank da Novateur Business Technology
Ta karanta fannin Kimiyyar Kwamfyuta a Jami'ar Ibadan
An naɗa Nkeiruka Onyejeocha, Ƙaramar Ministar Ƙwadaga da Aikin Yi
Ta kasance 'yar Majalisar Wakilai daga Jihar Abiya
Ta taɓa riƙe kantomar Ƙaramar Hukumar Umunneochi a Jihar Abiya
An naɗa Lateef Fagbemi, Ministan Shari'a kuma Atoni Janar na Tarayya
Shi Babban Lauya ne mai lambar SAN wanda ya zama lauya a 1984
An naɗa Uju Kennedy-Ohanenye, Ministar Mata
Ta kasance 'yar kasuwa da harkoki wajen gina rukunin gidaje da ilmi
An naɗa Nyesom Wike, Ministan Babban Birnin Tarayya
Ya yi Gwamna a Jihar Ribas daga 2015-2023 kuma shi lauya ne
An naɗa Mairiga Mahmud, Ƙaramar Ministar Babban Birnin Tarayya
Ta taɓa zama kwamishiniyar Ilmi mai Zurfi a Jihar Kano
Ta kasance wakiliya a Kwalejin Karatun Likitanci na Gaba da Digiri da Cibiyar Likitoci a Kwalejin Afirka ta Yamma
An naɗa Hannatu Musawa, Ministar Fasaha, Al'adu da Arziƙin Ƙage-ƙage
Ta kasance Mashawarciya ta Musamman ga Shugaba Tinubu a kan Al'adu da Nishaɗantarwa
Ita lauya ce kuma tana karatun digiri na uku
An naɗa Zephanian Jisalo, Ministan Ayyuka na Musamman da Hulɗa tsakanin Gwamnatoci
An zaɓe shi har karo biyu ɗan Majalisar Wakilai kuma sau biyu yana zama shugaban Ƙaramar Hukumar Abuja Municipal (AMAC)
Yana da babbar difloma a fannin nazarin halayyar ɗan'adam da difloma a fannin Shari'ar Manyan Laifuka daga Jami'ar Jos, yana kuma da difloma a fannin Hulɗa da Jama'a daga Cibiyar Horas da Aikin Jarida da Fasaha
Yawan mata a majalisar ministocin Tinubu
Mata ba su da yawa a cikin gwamnatin Tinubu.
Kamar sauran gwamnatocin da suka gabata, baya ga ta Goodluck Jonathan, yawan ministoci mata ba su kai kashi 20% ba.
Sai dai yawan ministoci mata a gwamnatin Tinubu sun zarta na gwamnatin tsohon shugaban ƙasar Muhammadu Buhari.

Wanda ya tsara: Olaniyi Adebimpe; Bincike: Damilola Ojetunde da David Ayoola; Wanda ya zana: Boaz Ochieng; Shugabar aiki: Dorothy Otieno.