Su wane ne ke takarar shugabancin Najeriya?
Karin bayani kan 'yan takarar shugaban ƙasa na Najeriya
Zaɓi ɗan takara don ganin bayanansa
Bola Tinubu
All Progressives Congress (APC)
- Shekaru: 70
- Ya yi karatun akanta a jami'ar Chicago State University.
- Gwamnan Jihar Legas karo biyu daga 1999 zuwa 2007.
- Ya wakilci Legas ta Kudu a Majalisar Dattijai daga 1992 zuwa 1993.
- Gagarumin ɗan siyasa a Najeriya, wannan ne karon farko da yake yin takarar shugaban ƙasa.
- Adawa da mulkin soja.
- Ya ninka kuɗin shigar Jihar Legas na shekara-shekara sama da sau huɗu daga biliyan N22.2 a 1999 zuwa biliyan N220.9 a 2007.
- Ya fara aiki a matsayin mai binciken kuɗi da kuma ma'aji a kamfanin Mobil Producing Nigeria, ɗaya daga cikin kamfanonin man fetur mafiya girma a ƙasar.
- Inganta harkokin fitar da kaya daga Najeriya zuwa ƙasashen waje da kuma rage dogaro da sayen kaya daga waje.
- Rage rabin adadi na rashin aikin yi tsakanin matasa cikin shekara huɗu da kuma ƙirƙirar ayyukan yi miliyan ɗaya a ɓangaren sadarwa cikin shekara biyu.
- Gyara tsarin shari'a don mayar da hankali kan kare afkuwar laifuka da kuma inganta yarda kan jami'an tsaro.
Atiku Abubakar
Peoples Democratic Party (PDP)
- Shekaru: 76
- Ya rike mukamin mataimakin shugaban Najeriya daga 1999 - 2007.
- Ya samu digiri na biyu a ɓangaren alaƙa tsakanin ƙasashe daga jami'ar Anglia Ruskin University da ke Ingila.
- Tsohon jami'in kwastam ne wanda ya shiga siyasa a farkon shekarun 1980.
- Sau biyar yana yin takarar shugaban ƙasa ba tare da nasara ba; a 1993, 2007, 2011, 2015, da kuma 2019.
- Ya kafa jami'ar American University of Nigeria, wadda ta bai wa 'yan matan Chibock tallafin karatu bayan Boko Haram ta sake su.
- Hamshaƙin ɗan kasuwa ne da ke da jari a harkokin fetur da noma da bankuna da sashen haɗa magunguna.
- Ƙudirin sayar da kadarorin gwamnati.
- Bai wa 'yan kasuwa ƙarin dama wajen haɓaka tattalin arziki.
- Inganta haɗin kan ƙasa ta hanyar daidaito, da adalci tsakanin ƙabilun Najeriya.
- Sauya tsarin tafiyar da gwamnati.
Peter Obi
Labour Party (LP)
- Shekaru: 60
- Gwamnan Jihar Anambra sau biyu daga 2007 zuwa 2014.
- Mataimakin ɗan takarar shugaban ƙasa a zaɓen 2019.
- Ɗan kasuwa ne da ya karanta fannin falsafa a Jami'ar Najeriya, Nsukka.
- Ya kafa wata gidauniya mai kuɗi dala miliyan 156 ƙunshe da kadarori ya zuwa lokacin da ya bar gwamnati.
- Ya sauya Anambra daga matsayi na 26 zuwa na 1 a jerin jihohin da suka fi cin jarrabawar fita daga sakandare ta NECO da WAEC.
- Ya mallaki harkokin hada-hada da suka samar da dubban ayyukan yi.
- Tabbatar da sa ido a aikin gwamnati da kuma yaƙi da rashawa.
- Mayar da Najeriya ƙasa mai sayarwa maimakon mai saye.
- Fifita rayuwar ɗan Adam ta hanyar zuba jari a ɓangaren ilimin-komai-da-ruwanka na STEM, da sashen lafiya, da kuma ayyukan raya ƙasa.
Rabiu Kwankwaso
New Nigeria Peoples Party (NNPP)
- Shekaru: 66
- Ministan Tsaro daga 2003 zuwa 2007
- Gwamnan Jihar Kano daga 1999 zuwa 2003, da kuma 2011 zuwa 2015.
- Ya wakilci Mazaɓar Madobi a Majalisar Wakilai a 1992 da kuma Mazaɓar Kano ta Tsakiya a Majalisar Dattawa daga 2015 zuwa 2019.
- Yana da digirin digirgir a injiniyanci daga jami'ar Sharda University da ke Indiya.
- Ba da tallafin karatu da yunƙurin taimaka wa mutane.
- Ƙara yawan ɗaliban firamare a 2011 daga miliyan ɗaya zuwa miliyan uku a 2015 lokacin da ya bar ofis.
- Ya ƙaddamar da ciyar da ɗalibai 'yan firamare da ba su kayan makaranta kyauta.
- Ya kafa Jami'ar Kimiyya da Fasaha ta Wudil da kuma jami'ar Northwest, waɗanda su ne jami'o'in gwamnatin Kano kawai zuwa yanzu.
- Samar da ayyuka ta hanyar zuba jari a ɓangaren noma.
- Shawo kan matsalar tsaro.
- Bin doka da ƙa'idar aiki.













