2019: Buhari na jiran tabbatar ma sa da nasararsa

Asalin hoton, Presidency
Shugaban Najeriya mai ci Muhammadu Buhari na Jam'iyyar APC na jiran tabbatar da nasarar sake lashe zaben shugaban kasar da aka gudanar ranar Asabar.
Sakamakon jihohi 36 da aka bayyana ya nuna Buhari ya ba babban abokin hamayyarsa na jam'iyyar PDP Atiku Abubakar ratar kuri'a sama da miliyan hudu.
Zuwa yanzu Atiku yana da yawan kuri'a 11,262,978, bayan kammala tattara sakamakon dukkanin jihohin Najeriya.
Tuni dai jam'iyyar PDP ta yi watsi da sakamakon, wanda ta kira aringizon kuri'u saboda ya saba wa sakamakon da tattara daga wakilanta.
Sai dai jam'iyyar APC mai mulki ta yi Allah-wadai da matakin da PDPn ta dauka.
A shekarar 2015 aka fara zabar Shugaba Buhari bayan da ya kayar da shugaba mai ci a lokacin, Goodluck Jonathan, na PDP.
Jam'iyyar ta PDP ta shafe shekara 16 tana da mulkar Najeriya.
Kuma Buhari ne ya zamo dan siyasar adawa na farko da ya lashe zabe a kasar.
Yaya zaben yake aiki?

Dan takarar da ya fi samun kuri'u ake ayyanawa a wanda ya yi nasara a zagayen farko, in dai har ya samu kashi 25 cikin 100 na kuri'un da aka kada a kashi biyu cikin uku na jihohin kasar.
'Yan takarar shugaban kasa 73 ne suka yi rijista, amma an fi yin gwagwarmaya ne tsakanin Buhari da Atiku.
Dukkansu sun fito ne daga arewacin kasar inda Musulmai suka fi yawa, kuma dukkansu sun haura shekara 70, yayin da mafi yawan 'yan kasar da suka yi rijistar zabe 'yan kasa da shekara 35 ne.
Bayanan 'yan takarar shugaban kasa a 2019
-
Jam'iyyaPeoples Democratic Party (PDP)Ranar haihuwa25 ga watan Nuwamba 1946, Jada, Jihar AdamawaTarihi
- Tsohon mataimakin shugaban kasar Najeriya a 1999 - 2007
- Ya nema kuma an ka da shi kujerar shugban kasa a 2007 a jam'iyyar AC
- A 1998 an zabe shi gwamnan jihar Adamawa. Kafin a rantsar da shi ne PDP ta dauke shi a matsayin mataimakin shugaban kasa ga Olusegun Obasanjo inda suka ci zaben a 1999, an rantsar da Atiku a ranar 29 ga watan Mayu na 1999 a matsayin zababben mataimakin shugaban kasa.
- Ya nemi kujerar gwamnan jihar Gongola ta da (wadda yanzu take (Adamawa da Taraba) a 1991, inda aka ka da shi.
- Jami'in Kastam na tsawon shekara 25. 1964 - 1989
-
Jam'iyyaAlliance for New Nigeria (AN)Ranar haihuwa12 ga watan Mayu na 1971, Ibadan, Jihar OyoTarihi
- Kwararre a kan harkar kasuwanci da jawabi
- Yana koyar da shugabannin kamfanoni da ke aiki a nahiyar Afirka da shugabanci a jami'ar Standford
- Shi ne shugaban kamfanin Gemstone na gogar da mutane a kan shugabanci,
-
Jam'iyyaYoung Progressive Party (YPP)Ranar haihuwa7 ga watan Mayu na 1963 a jihar LegasTarihi
- Lawya kuma masanin tattalin arziki
- Tsohon mataimakin gwamnan babban bankin Najeriya daga 2009 zuwa 2014, kuma mamba kwamitin kula da kudi
- Moghalu tsohon jami'i ne a hukumar kula da harkokin wanzar da zaman lafiya na Maja;loisar Dinlkin Duniya dake a New York daga 1996 - 1997.
- Tsohon jami'i mai ba da shawara kan harkokin shari'a na kotun majalisar dinkin duniya a kan Rwanda a 1997, daga baya aka yi masa karin girma zuwa jami'i mai hudda da jama'a na koyun.
- Shi ne tsohon shugaban Global Partnerships and Resource Mobilization a hukumar kula da lafiya ta duniya
-
Jam'iyyaJam'iyyar APCRanar haihuwa17 ga watan Disamba 1942, Daura, KatsinaTarihi
- Shugaban kasa daga 2015 zuwa yanzu
- Ciyaman din PTF, 1994
- Tsohon shugaban kasa, 31 ga watan Disamba zuwa 27 ga watan 1985
- Ya nemi kujerar shugaban kasa a 2003
- Dan takarar jam'iyyar CPC a 2011 inda Jonathan na PDP ya ka da shi
- Ministan Mai da Ma'adanai a 1976
- Gwamnan Jihar Borno Fabrairu - Maris 1976
- Gwamnan Arewa maso gabashin Najeriya a 1975 - 1976
-
Jam'iyyaAfrican Democratic Congress (ADC)Ranar haihuwa24 ga watan Disamba na 1956 a Randa, Sanga, Jihar Kaduna.Tarihi
- Masanin tattalin arziki, Ma'aikacin banki, masani kan ci gaban kasa-da-kasa
- Mataimakin gwamnan babban bankin Najeriya a 2005 - 2007
- Tsohon mai taimakawa tsohon shugaban kasa Jonathan a kan tattalin arziki da tsarin lamurra, mamba na kwamitin gudanar da tattalin arziki, kuma jami'i a bankin ci gaban Afirka.
-
Jam'iyyaAllied COngress Party of Nigeria (ACPN)Ranar haihuwa28 ga watan Afrillu na 1963, jihar Anambara.Tarihi
- Akawu kuma masaniyar tattalin arziki
- Tsohuwar mataimakin Babban Bankin Duniya sashen Afirka 2007 - 2012
- Ministar Ma'adanai 2005 - 2006
- Ministar Ilimi a 2006 - 2007.
- Wadda sunanta ya shiga jerin wadanda ake neman tantancewa na kyautar Nobel a 2018
- Wadda ta assasa kungiyar yaki da rashawa ta duniya da kuma gangamin Bring Back Our Girls
-
Jam'iyyaAfrican Action Congress (AAC)Ranar haihuwaAn haife shi a ranar 16 ga watan Fabrairun 1971 a Kiribi, jihar Ondo.Tarihi
- Dan jarida, dan gwagwarmaya
- Shi ne ya assasa jaridar yanar gizo ta Sahara Reporters a 2006, domin nuna al'adun Afirka da yaki da rashawa
- Shugaban dalibai a jami'ar Legas
Tsari
- Jam'iyyu a majalisa
- Sanannun jam'iyyu (masu dan takara wanda ba sananne ba)
- Sanannun 'yan takara a jam'iyyu wadanda ba sanannu ba
- Sananne a duniya yada labarai
- Sananne a duniyar shafukan sada zumunta
Mai hoton
Wadanda suka hada wannan aiki
Wadanne ne manyan batutuwan?
Najeriya ce kasar da ta fi kowacce arzikin man fetur a Afirka, amma cin hanci da gazawa wajen zuba jari ya sa abun da ake samu daga arzikin ya jawo matukar ci baya.
Farfadowar da har yanzu kasar ke yi daga koma bayan da tattalin arzikinta ya samu a 2016 na nufin babu isassun ayyukan yi ga dumbin matasan da ke fafutukar neman aiki.
Kusan kashi daya bisa hudu na matasan kasar ba su da aikin yi.

Zaben cikin alkalumma
- Masu katin zabe mutum miliyan
- Kashi 51 cikin 100 na masu kada kuri'a 'yan kasa da shekara 35
- 'Yan takarar shugaban kasa 73 ne
- Rumfunan zabe 120,000











