Hotunan abubuwan da suka faru a Afirka makon jiya

Mun zabo hotunan wasu daga cikin muhimman abubuwan da suka faru a Afiurka da 'yan Afirka a wanna makon.

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, A ranar Juma'a ne wannan yarinyar ta wuce ta kusa da baraguzan gidajen da suka rushe a yankin da ke makwabtaka da Kinshasa bayan mummunar zatfarewar kasa Ambaliyar ruwa ita ce babbar barazanar da mazauna babban birnin Jamhuriyar Dimokaradiyyar Congo suke fuskanta, saboda sun gina yawancin gidajensu su ne a gefen tsaunuka inda rashin magudanar ruwa ke haddasa ambaliya da rushewar gidaje.

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, A ranar ne dai wani dan kasar Sudan ya fito daga gidan biredi dauke da ledar biredi a Khartoum, babban birnin kasar.

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, Farashin biredi ya yi tashin gwauron zabi a Sudan, bayan da gwamnati ta janye tallafin fulawa, 'yan sanda sun tarwatsa zanga -zangar da dalibai suke yi sakamakon tashin farashin.

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, Har ila yau, ranar Juma'a ne aka ga wasu dawakai a wani daji lokacin da raba ke sauka a kusa da kangon birnin Shahhat na Libya inda Girkawa da Romawa suka zauna.

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, A Algeria, makwabciyar Libya, a ranar Lahadi ne wani mutum yake kallon yadda dusar kankara ta zuba a Ain Sefra. Wannnan ne karo na biyu cikin shekara uku da aka ga dusar kankara na zuba a hamadar Sahara.

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, Ranar Laraba, wani kwastoma a tsakiyar Nairobi yana kallon takalman da aka yi a China da aka baje don sayarwa.

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, Ranar Litinin wani dan Morocco shi kadai a gabar teku a babban birnin kasar Rabat. daidai lokacin da ake yin ruwa da iska. A 'yan kwanakin nan kasar ta fuskanci tsananin sanyi da ba a saba ganin irinsa ba.

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, Gomman jariran kunkuru ne ke jiran a sake su su shiga tekun Atlantic a Benin...

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, ... a daidai lokacin da masu fafutuka ke bikin tunawa da ranar kunkurun teku ta kasa.

Asalin hoton, Science Photo Library

Bayanan hoto, Duk yawan jariran kunkurun nan da aka dauki hotonsu a gabar teku, kadan daga cikinsu ne ke rayuwa har su girma, kamar wannan kunkurun da aka dauki hotonsa a Maliya daura da gabar tekun Masar.

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, Shugaban cocin Kifdawa ta Masar Fafaroma Tawadros 11, na jagorantar addu'a ranar Asabar. Ba kamar wasu mabiya addinin Kirista da suke bikin Kirsimati ranar 25 ga watan Disamba ba, su bakwai ga watan Janairu suke bikin Kirsimetinsu.

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, Wasu mabiya addinin Kirista a Masar na yin bikin Kirsimati ranar bakwai ga Watan Janairu. Wannan mabiyin yana karanta Linjila ta hanyar amfani da hasken kyandir a wata Coci da ke garin Lalibela na arewacin kasar.

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, Ranar jajiberin ne suke gudanar da addu'o'in safiya a Bete Amanuel, wata coci da ke garin.

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, A ranar Juma'a ne wani masunci dan kasar Somali ya dauko kifin da ya kama zai kai wata kasuwar kifi da ke kusa da tashar jiragen ruwa a Mogadishu.

Hotuna daga AFP, Reuters da Science Photo Library