Yadda fasa-ƙwaurin cinnaka ya zama sana'a mai maiƙo a duniya

    • Marubuci, Wycliffe Muia
    • Aiko rahoto daga, Nairobi
  • Lokacin karatu: Minti 4

Lokacin damina, ana iya ganin cinnaku na barin Gilgil, wani gari mai zaman lafiya a yanki mai yawan tsaunuka na kasar Kenya wanda ya zama cibiyar gudanar da haramtattun kasuwanci.

Kuma wannan ne lokaci mafi dacewa na safarar cinnakun domin sayarwa a wajen masu fasa ƙwaurinsu.

Wannan nau’i na safarar cinnakar, ta zama babba a Afirka, kuma suna da faɗi kuma masu launin ja, su ne kuma aka fi son saya daga ƙasashen waje - inda mutum zai iya sayar da su kan dala 220 a kasuwar bayan fage, wadda ke ci ta hanyar intanet.

Cinnaka ɗaya da aka haifa na iya ƙirƙirar yanki gaba-ɗaya kuma zai iya rayuwa na tsawon shekaru.

"Da farko ban san cewa an haramta harkar ba," kamar yadda wani mutum wanda ya buƙaci a sakaya sunansa da ya taɓa zama dillali ya faɗa wa BBC, inda yake haɗa masu saya daga ƙasashen waje da mutanen da ke sayar da cinnakun a cikin gida.

Na'uin cinnakun da aka fi sani da Messor cephalotes, an fi samun su a Gabashin Afirka kuma suna tara iri daban-daban wanda ya sa suka shahara.

"Wani abokina ya faɗa min cewa wani ɗan ƙasar waje na biyan maƙudan kuɗaɗe don sayan jan cinnaka mace - babba da aka fi samu a nan," in ji tsohon dillalin.

Ƴan ƙasashen wajen ba su taɓa zuwa gidajen cinnakun ba da kansu - suna zama a cikin gari su jira, a wani gida ko cikin mota, sannan mu kai musu cinnakun cikin wasu abubuwa da suka buƙaci mu saka musu su a ciki."

An samu ƙaruwar wannan haramtacciyar kasuwa a Kenya a bara, lokacin da aka gano wasu cinnaku mata kusan 5,000 da ransu a wani gida a garin Naivasha, wanda ke kusa da wani kogi da masu yawon buɗe ido ke zuwa.

Waɗanda ake zargin – 'yan ƙasashen Belgium da Vietnam da kuma Kenya – sun cika bututun gwaji da allurai haɗe da auduga, wanda zai bai wa kowanne cinnaka damar rayuwa har tsawon watanni biyu, a cewar hukumar kula da namun daji ta Kenya (KWS).

An yi niyyar tafiya da su ne zuwa Turai da Asiya sannan a sayar da su.

Wannan kasuwanci na cinnaku ya bai wa masana kimiyya da hukumomi mamaki.

Ita dai Kenya ta saba kama masu safarar hauren giwa da ƙahon karkanda, amma ba wai ta safarar cinnaku ba.

"Ko ni, na yi mamakin irin kasuwanci da ake yi," a cewar Dino Martins, masanin halittu da ke Kenya, inda ake da nau'ikan cinnaku kusan 600, kamar yadda ya shaida wa BBC.

"Wasu cinnaku na iya rayuwa sama da shekaru 50, watakila ma har zuwa shekaru 70. Ni da kaina na san gidajen cinnaku da ke kusa da Nairobi waɗanda sun kai aƙalla shekaru 40 kuma na ɗauki tsawon lokaci ina ziyartar wuraren," in ji Martins.

Wannan na nufin cinnaku mata ma na iya rayuwa na tsawon lokaci - saboda da zarar sun mutu, mazajensu na iya gazawa sannan waɗanda suka rage kuma za su nemi wasu cinnaku mata.

Ƴan Kenya da ke fama da matsalar cinnaku ko kwari da ke shigar musu gonaki ko gidajensu sun san wannan - kuma sai an haɗa duka na'uikansu kafin a iya ƙawar da su.

Tsohon dillalin ya ce ana iya kama cinnaku sannu a hankali ta hanyar matsawa gidajensu da kuma cafke su yayin da suke ƙoƙarin tserewa.

"Har sai da na ga an kama wasu masu safarar sannan na gane cewa a ce ni ma ina ciki dumu-dumu - daga nan na fita daga harkar," in ji shi.

Waɗanda aka kama da laifi an yanke musu hukuncin biyan tara ko kuma ɗaurin watanni 12 a gidan yari - sai dai sun zaɓi biyan tarar dala 7,700, su kuma ƴan ƙasashen waje sun fice daga ƙasar.

Makonni biyu da suka wuce, an kama wani ɗan China da ake zargin ya na da hannu a safarar wasu cinnaku da yawa a bara wanda ya tsere ta hanyar amfani da wani fasfo na daban.

An same shi da cinnanu mata kusan 2,000 waɗanda ya ɗaure ya na son fita da su ta filin jirgin sama na Jomo Kenyatta da ke birnin Nairobi.

Wasu masu rajin kare namun daji a yanzu sun yi kira da a samar da kariya ga duk nau'in cinnaku.

"Waɗannan abubuwa za su ci gaba da faruwa idan ba a tsaurara dokoki ba da kuma sa ido," kamar yadda wani mai bincike kan tsarin kasuwancin cinnaku a duniya, Sergio Henriques ya faɗa wa BBC.

Amma hukumar kula da namun daji a Kenya, ta ce ya kamata a magance matsalar nan take - ta hanyar sa ido da daƙile fataucin cinnakun " da ba a cika bayar da rahoton irin waɗannan abubuwa ba", in ji hukumar.

Ta ba da shawarar inganta kayan sa ido a filayen jirgin sama da sauran wuraren kan iyakoki.

Martin ya amince da hakan inda ya ce: "Wannan zai iya zama kaɗan daga cikin cinnaku da ake fatauci a duniya wanda muka iya gano wa."