Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Matakan da jam'iyyun adawar Najeriya ke shirin ɗauka gabanin 2027
Yayin da babban zaɓen Najeriya na 2027 ke ƙara matsowa, jam'iyyun adawa a ƙasar na cikin matsi, inda kusan duk wata jam'iyyar adawa mai ƙwari-ƙwari a ƙasar ke fama da shari'o'i a kotu kan shugabanci.
PDP, wadda ta kasance babbar jam'iyyar adawa, kuma wadda ta zo ta biyu a zaɓen shugaban ƙasa na 2023, a yanzu tana cikin mawuyacin hali bayan da kotu ta yi watsi da babban taronta da ta gudanar a jihar Oyo.
Wannan ya sanya manyan ƴaƴanta sun fice, ko dai sun koma jam'iyyar APC mai mulki ko kuma haɗakar ƴan adawa ta ADC.
ADC, jam'iyyar da ke samun tagomashi a baya-bayan nan bayan manayan ƴan adawar ƙasar sun koma cikinta, ita ma ta faɗa cikin sabon rikici bayan hukumar zaɓen ƙasar Inec ta janye amincewa da shugabanninta ƙarƙashin David Mark.
Wannan ya sanya kusan dukkanin jam'iyyun adawar ke cikin barazanar gaza tsayar da ƴan takara a zaɓe mai zuwa matuƙar ba su iya warware matsalolin nasu ba.
Jam'iyyun adawar sun zargi APC mai mulki da hannu a cikin rikice-rikicen, inda suka ce tana yin hakan ne domin yi musu zagon-ƙasa gabanin babban zaɓe na 2027.
Sai dai jam'iyyar APC ta sha musanta cewa tana da hannu a matsalolin da jam'iyyun ke ciki.
Manyan Jam'iyyun adawar a Najeriya sun ce sun fara daukar matakai daban-daban domin ganin sun ja hankalin duniya da hukumomin da suka kamata, kan ikirarin nasu na cewa dumukuradiyyar Najeriya na cikin barazana.
Ba za mu yarda ba - LP
A tattaunawarsa da BBC Dr Yunusa Tanko, wanda shi ne jagoran yakin neman zaben Peter Obi dan takarar jam'iyyar Labour a zaben shugaban kasa na 2023, kuma jigo a jam'iyar ADC a yanzu, ya ce sun shirya fuskantar yanayin da ke tunkarar su: ''Gaskiya za mu fito - mutane suna so su fito su yi gangami su ce ba su yarda ba da wannan taku da ake neman yi a dakushe 'yan adawa.''
''Na biyu za mu yi kokari kuma mu karasa kotu kuma mu je mu nemi 'yancinmu a kotu.
''Na uku za mu kara danganawa da kasar waje da ko'ina mu fada musu abin da ake ciki.
''Na hudu za mu yi kokarin mu tabbatar cewa ita wannan jam'iyya ta samu tsayawa zabe ta yanda ya kamata. Kuma duk wata hanya da za mu bi mu tabbatar cewa mun kwato wa kanmu 'yanci za mu bi ta, domin irin wannan bi-ta-da-kullin da ake yi ba zai taimaka wa dumukuradiyya ba. Gurgunta ta yake so ya yi. Ana so a tabbatar ba mu da murya gabadaya.''
Za mu ƙalubalanci INEC - PDP
Jam'iyar PDP ma da ake ganin tana fama da rikicin shugabanci, tana ganin wannan shi ne lokacin da ya fi dacewa jam'iyyun adawar su hada kai waje guda idan har suna son kalubalantar gwamnatin kasar da kuma samun damar fidda 'yan takararsu a dukkan matakai.
Farida Abdullahi, ita ce mai magana da yawun PDPn bangaren Kabiru Tanimu Turaki, inda ta yi wa BBC bayani : ''Ya kamata jam'iyyun adawa gabadaya mu fito kanmu tsaye mu dumfari INEC, don muna ganin kamar INEC ya kamata tana zaman kanta ne, amma abin da muke ganin tana yi kamar ba mai zaman kanta ba ce.''
''Idan ba mu fita, jam'iyyun adawa gabadaya mun hada kanmu ba, mun dumfari INEC ba suna so su yi mana wani abu da bai dace ba. Kuma na san muna da yakinin za mu zauna mu yi magana mu dumfari INEC saboda su tsaya su yi abin da ya dace.''
Dr Yunusa Tanko ya ce hadin kai a tsakaninsu a wannan yanayin da suke ciki, abu ne da ya zama wajibi:
''Kowace jam'iyyar adawa ta sani abin da ya faru da mu su ma zai iya samunsu, abin da ya faru da su mu ma zai iya samunmu. Amma idan aka samu sahihin zabe, dumukuradiyya kowa zai ji dadinta. To kuma mu sai mu zauna haka kawai muna kallo, mu bayi ne?''
Rikicin jam'iyyun adawa a Najeriya ya kara daukar hankali ne bayan wani mataki da hukumar zaben kasar, INEC ta dauka na cire shugabancin jam'iyyar ADC karkashin jagorancin Sanata David Mark, lamarin da 'yan adawar suka yi watsi da shi, tare da shan alwashin ci gaba da gudanar da babban taronsu da sauran al'amuransu yanda suka tsara.