Liverpool na harin Camavinga, Barca da Juventus na son Silva

Lokacin karatu: Minti 1

Liverpool na cikin shirin ko ta kwana wajen siyen ɗan wasan Real Madrid Eduard Camavinga, da Liverpool din ta jima tana son ɗaukarsa. (L'Equipe - in French)

Barcelona da Juventus na cikin ƙungiyoyin da ke son ɗaukar ɗan wasan Manchester City Bernardo Silva, ba tare da wani kwantaragi na kansa ba, a wannan kaka. (Sky Sports)

Juventus na da kwaringuiwar cewar samun gurbin buga gasar Champion zai iya basu gurbin ɗauko dan wasan Tsakiyar Uruguay Manel Ugarte kan fam miliyan talatin da biyar ga Manchester United. (Corriere dello Sport - in Italian)

Arsenal na da dama kan Liverpool, wajen aniyar ta na ɗauko ɗan wasan gefen RB Leipzig Yan Diomande. (Caught Offside)

Tottenham ba zata amince da tayin kyaftin ɗin ta Cristian Romero ƙasa da euro miliyan 50 ba (£43.6m), yayin da Atlentico Madrid ke harin ɗan wasan. (Fichajes - in Spanish)

Idan har ta tabbata Vinicius zai bar Real Madrid, Paris St-Germain ko ƙungiyoyin da ke buga Premier ne kaɗai mafita gare shi. (ESPN)

Newscastle ta shiga sahun ƙungiyoyin da ke Turai da ke son mai tsaron bayan Werder Bremen Karim Coulibaly. (Fabrizio Romano)

Liverpool da Manchester sun ƙara matsawa kan ganin sun ɗauko ɗan wasan Monaco da Fransa Maghnes Akliouche. (Teamtalk)

Borussia Dortmund na son ɗauko ɗan wasan Strasbourg da Belgium Diego Moreira, sai dai Chelsea na son ɗan wasan. (Florian Plettenberg)

Roma na son ɗaukar ɗan wasan Midtjylland Dario Osorio, da Franculino, yayin da farashin ƴan wasan gefen na Chile da Guinea-Bissau ya kai euro miliyan 55m (£48m). (Gazzetta dello Sport - in Italian)