Iran ta yi kakkausar suka ga Saudiyya da Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa (UAE), tana zargin ƙasashen biyu da bai wa Amurka damar amfani da yankunansu wajen kai mata hare-hare, inda ta bayyana hakan a matsayin babban take haƙƙinta da barazana ga tsaron ƙasarta.
A cikin wasiƙu guda biyu da ta aika zuwa Kwamitin Tsaro na Majalisar Ɗinkin Duniya da Babban Sakataren Majalisar Ɗinkin Duniya, Iran ta buƙaci waɗannan ƙasashe su mutunta ka’idojin makwabtaka mai kyau tare da dakatar da amfani da yankunansu wajen kai hare-hare kan ƙasar.
Jakadan Iran a Majalisar Ɗinkin Duniya, Amir Saeed Iravani, ya bayyana a cikin wasiƙun cewa ƙasashen biyu sun saba doka ta hanyar bai wa wasu ƙasashe damar kai hare-hare a Iran.
Iran ta kuma yi gargaɗi cewa duk da tana girmama Saudiyya da UAE, tana da haƙƙin ɗaukar dukkan matakan da suka dace domin kare kanta.
Tun bayan fara rikicin da ke tsakanin Amurka da Isra’ila da Iran, ƙasashe da dama a yankin, ciki har da Saudiyya da UAE, sun fuskanci hare-haren makamai masu linzami da jiragen yaƙi marasa matuki daga Iran.
Iran ta bayyana cewa hare-haren nata a kan sansoninin Amurka ne da wuraren da ke da alaƙa da Amurka da Isra’ila a yankin.