Dalilai 4 da suka sa ƙasashen Turai ke son likitocin Najeriya
Asalin hoton, Getty Images
Ƙasashen Turai da na Larabawa da dama na son ɗaukar likitoci daga nahiyar Afirka domin yin aiki a ƙasashensu.
A baya-bayan na ƙungiyar General Medical Council, GMC mai lura da ayyukan likitoci a Birtaniya ta bayar da rahoton cewa kimanin likitocin Najeriya 4,600 ne suka koma Birtaaniya da aiki cikin shekara uku.
Alƙaluman ƙungiyar sun nuna cewa a yanzu haka akwai likitocin Najeriya kusan 15,692 da ke aiki a Birtaniya, lamarin da ya sa Najeriya ta zama ƙasa ta biyu, bayan Indiya cikin manyan ƙasashen da Birtaniya ke samun likitoci.
Ƙaurar likitocin na haifar da fargaba ga fannin lafiyar ƙasa da ma tattalin arzikinta.
Gwamnatin Najeriya ta yi ƙiyasin cewa tana kashe dala 21,000 domin horas da kowane likita ɗaya a ƙasar.
Ƙiyasin ya nuna cewa ƙasar na asarar dala miliyan 98.5 a cikin ƙasa da shekara biyu.
Me ya sa ƙasashen Turai ke son likitocin Najeriya?
Baya ga Birtaniya akwai ƙasashe masu yawa kama daga na Turai da yankin Asiya zuwa Amurka da ke rububin ɗaukar likitocin Najeriya, domin yin ayyuka a can.
To me ya sa ƙasashen - waɗanda ake ganin da ci gaban fannin kiwon lafiya - ke son ɗaukar likitocin na Najeriya?
BBC ta tuntuɓi Dr Mannir Bature, sakataren yaɗa labaran ƙungiyar Likitoci ta Najeriya don jin dalilin hakan, wanda kuma ya lissafo wasu dalilai da ya ce su ne da sanya hakan.
Asalin hoton, Getty Images
- Ingancin horon aiki
Ƙwararren likitan ya ce babban dalilin shi ne yadda likitocin Najeriya suke da ingancin horon aiki.
''Likitocin Najeriya na da ƙwarewar aiki sosai, kuma galibi idan aak zo jarrabawar ɗaukar likitoci a ƙasashen waje, likitocin Najeriya ke nuna ƙwazo da ƙoƙari da kuam samun nasara'', a cewar Likitan.
Ya kuma alaƙanta ƙwazon da irin horon da suke samu a makarantun horon likitocin ƙasar.
- Hazaƙa da ƙwazon aiki
Dr Barure ya ce yadda likitocin Najeriya suka saba ayyuka masu yawa ya sa ƙasashen Turai ke sha'awarsu.
A Najeriya dai galibi za ka samu likita ɗaya yana aiki a asibitoci fiye da ɗaya, da aikin sa'o'in da suka zarta 10 ko 12 a wuni.
''Kasancewar akwai ƙarancin likitoci a asibitocinmu, za ka samu likita yana aiki fiye da abin da doka ta ƙayyade masa, to hakan ya taimaka musu yin ƙoƙari wajen gudanar da aiki'', kamar yadda ya yi ƙarin haske.
- Ƙwarewar amfani da dabarun aiki
Dr Bature ya ce saboda yanayin aiki a Najeriya ya sa likitocin ƙasar sun saba aiki ko da kuwa babu wasu daga cikin na'urorin da ya kamata su yi aikin da su.
''Wannan ya sa idan suka je Turai suke yin ayyukansu ba tare da tangarɗa ba,koda kuwa babu na'urorin da ake buƙatar'', kamar yadda ya yi ƙarin haske.
- Rashin ƙwarewar wasu likitocinsu
Dr Bature ya ce wani ƙarin dalilin shi ne wasu daga cikin likitocin ƙasashen na Turai ba su da ƙwarewar aiki kamar na Najeriya.
''Wannan kuma ba ya rasa nasaba da irin horon da suke samu a makarantunsu, domin kuwa galibi ɗalibansu ba sa wahala wajen koyarwa, domin a lokacin koyar da su an sabar musu da nuna gabatar musu duka na'urorin da ake buƙata wajen kowane aiki''.
''Don haka a duk lokacin da a asibiti aka gabatar musu majinyacin da ke buƙatar wata na'urar da babu ita a asibitin to ba za su iya taɓa shi ko yi masa aiki ba, saɓanin likitocin Najeriya da aka horar da su yin aiki ko ba na'ura'', kamar likitan ya bayyana.
Me ya sa likitocin Najeriya ke tafiya Turai?
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Dr Mannir ya ce babban dalilin da ya sa likitocin Najeriya ke komawa Turai rashin albashi mai kyau da alawus-alawus.
''Yawanic albashin da ake biyansu ba ya wadatar da su wajen sauke nauyin d ake kansu, na biyan kuɗin makarantar yara da abinci da sauran buƙatu'', kamar yadda ya bayyana.
Ya ci gaba da cewa a ƙasashen na Turai, likitocin kan samu wadataccen albashin da za su iya biyan buƙatunsu na rayuwa har ma su taimaki wani.
Ƙwararren likitan ya ce wani ƙarin dalilin shi ne rashin wadattun kayan aiki a asibitinmu.
''Yawanci a asibitocin namu babu kayan aikin da ya kamata su yi aiki da su, kuma kowane ƙwararren likita na son ya riƙa aiki a fannin da ya ƙware'', in ji shi.
Dr Mannir ya kuma lissafo matsalar rashin tsaro a Najeriya cikin dalilan da ke sa likitocin ƙasar tafiya ƙadsashen Turai da zarar sun samu dama.
''Daga bayanan da muke da su likitoci masu yawa sun bar ƙasar nan saboda matsalar tsaro, mun ga yadda ake kai hare-hare har a kan cibiyoyin lafiya'', in ji shi.
Me ya kamata hukumomin Najeriya su yi?
Dr Aliyu Umar Tilde mai sharhi kan al'amuran yau da kullum a Najeriya ya ce abin da ya kamata hukumomin ƙasar su yi shi ƙara yawan likitocin da ake horas wa ƙasar.
''Gaskiya yawan likitocin da jami'o'in ƙasarmu ke horas wa sun yi kaɗan, likitocin jami'o'inmu ke yaye wa shekara 20 zuwa 30 da suka gabata su ne dai har yanzu ake yayewa, don haka yana da kyau a ƙara yawansu'', in shi.
Haka ma Dr Tilde ya ce babban abin da ya kamata gwamnati ta yi shi inganta albashin likitocin ƙasar.
''Su ma fa likitocin nan wasu ba da son ransu suke fita ba, suna fita ne domin nemar wa kansu mafaita, kamata ya yi gwamnati ta ninka musu albashinsu da alawus-alawus da suek samu'', in i shi.
Shi ma Dr Mannir ya ce yana da kyau gwamnati ta ƙara albashi da alawus alawus ɗin da ake biyan likitocin ƙasar.
''A riƙa biyansu albashin da zai wadace su biyan duka buƙatunsu na rayuwarsu da ta iyalansu'', in ji shi.
ya kamata gwamnatin Najeriya ta riƙa bai wa fannin lafiya fififko, ta hanyar samar da wadattun kayan aiin kula da lafiya a asibitocin ƙasar.
''Wanan shi ne ƙashin bayan aikin likitanci, kowane likita na da burin idan an zo damarar lafiya, ya kasance yana da kayan aikin da zai yi masa aiki, to amma a Najeriya yawancin asibitocin suna da wannan matsalar'', in ji Dr Mannir.
Babban Labari
Labarai na musamman
Labaran da suka fi shahara
Babu karin bayanai