Sharuɗɗa 10 da ke cikin yarjejeniyar tsagaita wutar yaƙin Amurka da Iran

Lokacin karatu: Minti 3

Donald Trump ya sanar da cewa bayan tattaunawa da shugabannin Iran, an cimma yarjejeniyar tsagaita wuta tsakanin Amurka da Iran domin bayar da damar wucewa ta mashigar Hormuz.

"Na amince in dakatar da ƙaddamar da harin bam kan Iran na tsawon makonni biyu," in ji shi.

"Wannan tsagaita wuta ce da duka ɓangarori suka amince da ita".

Trump ya ƙara da cewa ya amince da tsagaita wutar ta tsawon makonni biyu ne "bayan da Iran ɗin ta amince da dakatar da kai hare-hare nan take, da kuma buɗe mashigar Hormuz".

Trump ya ce Iran ta aika wa Amurka da Isra'ila sharuɗɗa 10.

Ministan harkokin wajen Iran Abbas Araghchi, ya sanar da cewa za ta amince da tsagaita wuta "idan aka daina kai wa Iran hari",.

Ya ƙara da cewa: "za a ci gaba da wucewa ta mashigar Hormuz na tsawon makonni biyu".

Hakan zai kasance ne "ƙarƙashin kulawar rundunar sojin Iran," in ji shi.

Me sharuɗɗa 10 suka ƙunsa?

Kafar yaɗa labaran Iran ta ce: "Trump ya sanar da tsagaita wuta ta tsawon makonni biyu, inda ya amince da sharuɗɗan da Iran ta gindaya na dakatar da yaƙin saboda gudun zubewar ƙimarsa bayan barazanar da ya yi".

  • Dakatar da yaƙi kan Iraƙi, Lebanon da Yemen nan take
  • Dakatar da yaƙi kan Iran da kai hare-hare gaba ɗaya ba iya na tsawon wani lokaci ba
  • Dakatar da yaƙi a yankin baki ɗaya
  • Buɗe mashigar Hormuz
  • A bai wa Iran cikakken ƴanci da iko da mashigar Hormuz
  • Biyan diyyar ɓarnar da aka yi wa Iran a yaƙin
  • A ɗage dukkanin takunkuman da aka ƙaƙaba wa Iran
  • Amurka ta saki kuɗaɗen Iran da ta riƙe
  • Iran za ta amince ba za ta mallaki makamin nukiliya ba
  • Tsagaita wuta nan take idan aka amince da dukkan buƙatun da aka gabatar

Me Isra'ila ta ce?

An ji ƙarar jiniyar ankararwa na ƙara a Isra'ila jim kaɗan bayan sanarwar da Donald Trump ya bayar, inda Isra'ilar ta ce garkuwar kariyarta ce ke kakkaɓo makaman da Iran ta harba mata.

An ji ƙararrakin abubuwan fashewa da yawa Ranar Talata a birnin Jerusalem.

Jim kaɗan bayan sanarwar Trump, Firaiministan Isra'ila Benjamin Netanyahu ya ce: "Isra'ila na goyon bayan matakin Shugaba Trump na dakatar da hare-hare na tsawon mako biyu matuƙar Iran ta buɗe mashigar Hormuz ba tare da ɓata lokaci ba tare da dakatar da kai wa Isra'ila da Amurka hari, da ma sauran ƙasashen yankin."

Bayanin nasa ya ƙara da cewa "tsagaita wutar ba ta shafi Lebanon ba", inda Isra'ila ta tura sojojinta.

Babu bayani kan ko an tuntuɓi Netanyahu kafin matakin da Trump ɗin ya ɗauka na amincewa da yarjejeniyar.

Me zai faru a gaba?

Pakistan, wadda ta shiga tsakani domin tabbatar da yarjejeniyar ta gayyaci tawagogin ɓangarorin biyu domin yin wata ganawa ranar Juma'a a birnin Islamabad "domin cimma yarjejeniyar ƙarshe ta kawo ƙarshen rikicin".

Mai magana da yawun fadar shugaban Amurka, Karoline Levitt ta amince cewa ana gudanar da tattaunawa, amma "babu wata matsaya ta ƙarshe sai abin da Donald Trump ko fadar White House ta sanar".

A yanzu dai a bayyane take cewa shruɗɗan ɓangarorin biyu sun sha bamban game da yarjejeniyar tsagaita wutar.

Iran da Amurka sun yi zaman tattaunawa sau biyu a shekarar da ta gabata. Sai dai an ga yadda ake samun tashin-tashina a lokacin da ake tsaka da tattaunawar.