Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

KAI TSAYE, Yaƙin Iran da sauran abubuwan da ke faruwa a sauran sassan duniya, Laraba 8/4/2026

Wannan shafi ne da ke kawo muku rahoto kan yaƙin Iran da Amurka da Isra'ila da kuma abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya na ranar Laraba 8 ga watan Afrilun 2026.

Rahoto kai-tsaye

Daga Aisha Babangida, Haruna Kakangi da Muslim Muhammad Yusuf

  1. Kuwait ta ce Iran ta kai mata hari bayan yarjejeniyar tsagaita wuta

    Kuwait ta ce Iran ta kai mata hari da jiragen sama marasa matuƙa bayan sanarwar dakatar da wuta

    Kuwait ta bayar da rahoton ne inda ta ce harin ya faru a safiyar yau, bayan ‘yan sa’o’i da sanar da cimma yarjejeniyar dakatar da wuta tsakanin Iran da Amurka.

    A cikin sanarwar sojin Kuwait a tashar X-Channel, an ce: "Tun daga ƙarfe 8 na safiyar yau, Kuwait ta fuskanci hare-hare daga Iran amma kuma an yi nasarar kakkaɓo jirage marasa matuƙa 28 da aka kai harin da su."

    Sanarwar ta ƙara "duk da cewa an kakkaɓo makaman da aka kai wa harin da su, hare-haren sun janyo babban lalacewa ga matatun mai da tashoshin wutar lantarki, da kuma tashoshin tsarkake ruwa."

  2. 'Barazanar Trump kan Iran ta kusa jefa duniya cikin mummunar hali'

    Ministan harkokin wajen Spain, José Manuel Álvarez, ya ce barazanar Shugaban Amurka Donald Trump na lalata Iran ta kusan jefa duniya cikin mummunar hali.

    A cikin wata hira a rediyo, Álvarez ya bayyana cewa wa’adin Trump "abu ne da ba za a taba tunanin irin sa ga bil’adama ba."

    Duk da haka, ya ce har yanzu lokaci bai yi ba a tantance ko rikicin ya ƙare gaba ɗaya.

    "Duk lokacin da shugaban ƙasa mai karfin soja ya yi irin waɗannan barazanar, ina ɗaukar su da muhimmanci," in ji ministan harkokin wajen Spain.

    A jiya ne Trump ‘yan sa’o’i kafin yarjejeniyar dakatar da wuta ya yi barazanar cewa za a iya lalata Irandaba ɗaya a rana guda.

  3. An kai hari kan matatar man Iran bayan yarjejeniyar tsagaita wuta

    Kamfanin ƙera da rarraba man fetur na ƙasar Iran (NIOR) ya tabbatar da harin da aka kai wa matatar mai ta Lavan.

    A cikin wata sanarwa, kamfanin ya ce, "A kusan ƙarfe 10 na safiyar yau, Laraba, an kai harin ban tsoro ga matatar mai ta Lavan dake Tsibirin Lavan."

    Sanarwar ta ƙara da cewa, "Ƙungiyoyin tsaro da kashe gobara na aiki domin kashe gobarar da tabbatar da tsaron wurin."

    Haka zalika, Kamfanin Labarai na Mehr ya ruwaito wasu fashe-fashe a tsibiran Lavan da Siri a Tekun Fars.

    Waɗannan fhare-hare sun faru ne a daidai lokacin da Iran da Amurka suka amince da yarjejeniya ta dakatar da wuta na tsawon makonni biyu.

  4. Ana zanga-zangar adawa da matakin Inec kan jam'iyyar ADC

    Ga wasu hotuna da ke nuna yadda masu zanga-zanga ke tattaruwa a babban birnin tarayya, Abuja, domin nuna rashin amincewarsu da matakin hukumar zaɓe ta ƙasa, INEC da ke cewa ta daina amincewa da shugabancin David Mark a jam'iyyar ADC.

    Wannan mataki na INEC ya haifar da ce-ce-ku-ce cikin jam’iyyar da kuma magoya bayan jam'iyyar, inda ake zargin akwai sabani tsakanin shugabanni da mambobi.

    An ga masu zanga-zangar suna ɗauke da alluna da ke ɗauke da rubuce-rubuce irin su: “Muna bayan David Mark”, “Tsoron mai Tinubu yake yi”, “Muna tare da ADC”, da “Ina ɓangaren shari'ar da ta tsaya wa talakawa a lokacin mulkin soja?” da dai sauransu.

    Masu zanga-zangar sun bayyana cewa matakin INEC yana nuna tsoma bakin da bai dace ba a harkokin cikin gida na jam’iyyar.

  5. Shugaban Majalisar Ɗinkin Duniya ya yi maraba da tsagaita wutar Amurka da Iran

    Mai magana da yawun shugaban Majalisar Ɗinkin Duniya, António Guterres, ya ce ya yi maraba da sanarwar tsagaita wuta na makonni biyu tsakanin Amurka da Iran.

    Ya bayyana cewa, Guterres yana kira ga dukkan ɓangarorin da ke da hannu a rikicin Gabas ta Tsakiya da su mutunta dokokin ƙasa da ƙasa tare da bin sharuɗɗan yarjejeniyar tsagaita wutar, domin buɗe hanyar samar da zaman lafiya mai ɗorewa da cikakken kwanciyar hankali a yankin.

    Haka kuma, ya nuna godiya ga ƙoƙarin da ƙasar Pakistan da sauran ƙasashe suka yi wajen taimakawa wajen cimma wannan yarjejeniya ta tsagaita wuta.

  6. Amurka da Iran na iƙirarin samun nasara a yarjejeniyar tsagaita wuta

    Amurka da Iran na iƙirarin samun nasara a yarjejeniyar tsagaita wuta na tsawon mako biyu da suka cimma a tsakaninsu.

    An sanar da yarjejeniyar ne kafin cikar wa’adin da Shugaban Amurka, Donald Trump, ya bai wa Iran na ta buɗe mashigar Hormuz, ko kuma ta fuskanci mummunan hari da zai iya lalata ƙasar baki ɗaya.

    Iran ta ce za ta ba da damar wucewar jiragen ruwa cikin aminci ta mashigar na tsawon mako biyu, amma ƙarƙashin kulawar sojojinta.

    Isra’ila ta ce tana goyon bayan matakin da Amurka ta ɗauka na dakatar da hare-hare kan Iran.

    A cikin sabon saƙonsa a shafukan sada zumunta, Trump ya bayyana ranar a matsayin babbar rana ga zaman lafiya a duniya, yana mai cewa yarjejeniyar na iya kai wa ga wani sabon zamani mai armashi a Gabas ta Tsakiya.

    Sai dai har yanzu akwai manyan ƙalubale da ke gaban samun dawwamammen zaman lafiya, inda daga cikin buƙatun Iran akwai biyan diyya da kuma ɗage takunkuman da Amurka ta ƙaƙaba mata.

  7. Ƙasashen duniya na mayar da martani kan yarjejeniyar Iran

    Ƙasashen duniya sun yaba da yarjejeniyar da aka cimma ta tsagaita wuta tsakanin Iran da Amurka da kuma Isra'ila, lamarin da zai bayar da damar buɗe mashigar Hormuz mai matuƙar muhimmanci ga tattalin arziƙin duniya.

    Saudiyya ta ce tana sa ran yarjejeniyar za ta yi sanadiyyar samar da cikakken zaman lafiya mai ɗorewa.

    Babbar jami'ar diflomasiyya ta Tarayyar Turai Kaja Kalas ta bayyana lamarin a matsayin ƙoƙarin daƙile faɗawa karaya da zai bayar da damar warware rikicin ta hanyar tattaunawa.

    Shugaban Faransa Emmanuel Macron ya ce yana fatan za a yi cikakkiyar biyayya ga yarjejeniyar.

    Firaiministan Birtaniya Keir Starmer zai kama hanya zuwa yankin Gulf domin yin tattaunawa ta diflomasiyya kan yadda za a tabbatar da tsagaita wutar.

  8. Amurka da Iran sun cimma yarjejeniyar tsagaita wuta na mako biyu

    Amurka da Iran sun sanar da tsagaita wuta na tsawon mako biyu, bayan da shugaban Amurka, Donald Trump, ya janye barazanar kai wani gagarumin hari kan Iran, jim kaɗan kafin cikar wa’adin da ya bayar.

    Ministan harkokin wajen Iran, Abbas Araghchi, ya tabbatar da cewa za su buɗe mashigar Hormuz domin jiragen ruwa su riƙa wucewa a lokacin tsagaita wutar, amma da rakiya daga sojojin Iran.

    Rahotanni sun nuna cewa an cimma yarjejeniyar ne mintuna goma kafin cikar wa’adin da Trump ya bayar na kai hare-hare.

    An kulla yarjejeniyar da ƙarfe 6:30 na yamma agogon Washington, wanda ya yi daidai da ƙarfe 11:30 na dare a agogon Najeriya.

    Firaministan Pakistan ya sanar da fara aiki da yarjejeniyar nan take, inda yayi maraba da matakin tare da gayyatar dukkan ɓangarorin da su hallara a wani babban taro a Islamabad ranar Juma’a 10 ga watan Afrilu, domin ci gaba da tattaunawa da nufin samun fahimtar juna.

    Daga cikin buƙatun da Iran ta gabatar akwai tabbacin cewa ba za a sake kai mata hari ba, za ta ci gaba da kula da mashigar Hormuz, da kuma ci gaba da sarrafa makamashin uranium da take da shi. Haka kuma ta buƙaci a ɗage takunkuman da aka ƙaƙaba mata.

    Sauran buƙatun sun haɗa da dakatar da wasu yarjejeniyoyi da suka shafi Majalisar Tsaron Majalisar Ɗinkin Duniya da Hukumar Kula da Makamashin Atomic ta Duniya da biyan diyya da janye sojojin Amurka daga yankin Gabas ta Tsakiya, da kuma dakatar da dukkan hare-hare ciki har da na Lebanon.

    A nata ɓangaren, Amurka ta amince da tsagaita wutar ne da sharadin cewa jiragen ruwa za su rika wucewa ta mashigar Hormuz ba tare da wata barazana daga Iran ba.

    Isra’ila ma ta goyi bayan matakin na tsagaita wutar, bayan da Iran ta amince da buɗe mashigar Hormuz da kuma dakatar da hare-hare kan Amurka, Isra’ila da ƙasashen yankin Gulf.

    Sai dai har yanzu akwai ƙarancin yarda da juna tsakanin Amurka da Iran, a daidai lokacin da ake shirin ci gaba da tattaunawa. A baya, sau biyu kasashen biyu sun fara irin wannan tattaunawa, amma rikici ya kan ɓarke kafin a kai ga cimma matsaya.

  9. Ba za mu bari a ƙwace mana ADC ba - Nafi'u Gombe

    Yayin da ake ci gaba da ce-ce-ku-ce kan zargin maƙarƙashiya da kan halin da jam'iyyar hamayya ta ADC a Najeriya, ke ciki, mutumin da ake ja-in-ja da shi a kan shugabancinta Nafi'u Bala Gombe, ya bayyana wa BBC dalilinsa na bijera wa jagorancin David Mark a jam'iyyar.

    Jam'iyyar ta ADCn da ta ƙunshi manyan ƴan hamayya a Najeriya dai ta shiga ruɗani ne bayan hukumar zaɓen ƙasar, INEC, ta cire sunan David Mark a matsayin shugaban jam'iyyar daga shafinta na intanet, saboda wani hukuncin kotu da ya shafi Nafiun.

    Nafiun Bala Gombe ya ce har yanzu shi ne halattaccen shugaban jam'iyyar ta ADC, inda ya ce raina shekarunsa da aka yi, ya sa shi tashi tsaye wajen ganin ya ƙwatar wa kansa haƙki.

  10. Assalamu alaikum

    Jama'a barkanmu da wannan safiya ta Laraba ga wannan shafin namu na BBC Hausa, inda za mu ci gaba da kawo muku labaran kai-tsaye na abubuwan da suke faruwa a Najeriya da sassan duniya.

    Aisha Babangida ce ke fatan kasancewa da ku a dai dai wannan lokaci.

    Za ku iya leƙawa shafukanmu na sada zumunta na facebook da X da kuma whatsapp domin karanta wasu labaran da kallon bidiyo da ma tafka muhawara.

    Ku kasance tare da mu.