Wane ɗauki Amurka za ta iya kai wa ƴan hamayyar Najeriya?

Asalin hoton, ADC/X

Lokacin karatu: Minti 3

Tun bayan da hukumar zaɓen Najeriya ta INEC ta sanar da cire sunan Sanata David Mark a matsayin shugaban jam'iyyar ADC daga na'urarta, jiga-jigan jam'iyyar suka ɗaura ɗamar yaƙi da abin da suka kira ƙoƙarin danne masu hamayya.

Bayan zanga-zanga da taron manema labarai da jiga-jigan jam'iyyar suka gudanar, sun kuma sanar da cewa za su aiki tare da wani kamfanin ƙasar Amurka wanda zai taimaka musu wajen kai ƙorafinsu a gaban majalisar dokokin Amurkar dangane da batun.

Kafar watsa labarai ta Sahara Reporters ta ambato sunan kamfanin da Von Batten-Montague York L.C.

Abin da kamfanin ya ce zai yi

A wani saƙo a shafinsa na X ranar Laraba, kamfanin na Von Batten-Montague York L.C. ya wallafa cewa za su ɗauki mataki a kan abin da hukumar INEC ta Najeriya ta yi.

"...Ƴan majalisar dattawa da wakilai na Amurka suna hutun bikin Easter...amma muna ƙoƙarin isar da saƙon manyan ƴan majalisar sannan muna shirin gabatar da batun ga jagorancin majalisar da kuma jagororin Majalisar Tsaron Amurka a farkon mako mai zuwa.

"Saɓanin gwamnatin Biden wadda ba ta ɗauki wani matakin a-zo-a-gani a zaɓen 2023, shi shugaba Trump ba zai yi haka ba domin ba halinsa ba ne ya zura ido yana ganin ana ci wa dimokraɗiyya dunduniya", in ji kamfanin.

Kamfani ya kuma bayyana irin matakin da yake son bayar da shawara a ɗauka a kan duk wani ɗan siyasar da ke da hannu a cikin abin da ya kira da yi wa mulkin dimokraɗiyya karan tsaye.

"Za mu bai wa ofishin shugaban ƙasa da ƴan majalisar dokoki shawara da a saka wa duk wani jami'i ko ɗan siyasa mai hannu a cikin al'amarin kawo naƙasu ga mulkin dimokraɗiyya takunkumin ƙasa da ƙasa da suka haɗa da riƙe da dakatar da kadarorinsu da taƙaita musu amfani da tsarin musayar kuɗaɗe na duniya da kuma haramta musu tafiye-tafiye tare da iyalansu," in ji kamfanin a shafinsa na X.

Daga ƙarshe kamfanin ya yi kira ga shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu da ya tabbatar ya gudanar da zaɓen 2027 cikin tsari sannan a buɗe ta hanyar bai wa ƴan Najeriya abin da suka zaɓa.

Amurka za ta iya taka rawa

Malam Kabiru Sufi, malami a kwalejin share fagen shiga jami'a ta Kano, CAS kuma masanin kimiyyar siyasa ya shaida wa BBCcewa akwai rawar da Amurka za ta iya takawa.

"A baya a zaɓen 2015, ita jam'iyyar APC ta yi amfani da irin wannan dabarar kuma hakan ya taimaka mata sosai wajen samun karɓuwa a ƙasashen yammaci musamman Ingila wadda ta rinƙa gayyatar su a matsyin ƴan adawa daga Najeriya domin su rinƙagabatar da taruka...

"An ga yadda su Muhammadu Buhari da Bukola Saraki suka rinƙa zarya wanda kuma hakan ya taimaka musu wajen samun nasarar lashe zaɓen da kuma haƙurin da Goodluck Jonathan ya yi kan kayen da ya sha. Lallai irin wannan abun na iya yin tasiri," in ji Malam Kabiru.

Jadawalin babban taron jam'iyyar ADC

Hukumar Zaɓe ta Najeriya Inec ta sanar cewar za a gudanar da zaɓen shugaban ƙasa da na ƴan majalisar wakilai ranar 16 ga watan Janairun shekara ta 2027 ya yin da za a gudanar da zaɓen gwamnoni da ƴan majalisar jihohi ranar 6 ga watan Fabrairun shekara ta 2027.

Kakakin jam'iyyar ya ce tuni sun sanar da Inec tsarin su kuma ba abinda zai hana su aywatar da shi.

  • Tantance ƴan takara- 7 April 2026
  • Ƙorafe-korafe da tantancewa -8 April 2026
  • Taron ƙananan hukumomi da mazaɓu - 9 April 2026
  • ƙorafe-ƙorafe-10 April 2026
  • Taron jam'iyya a jihohi-11 April 2026
  • Sauraron ƙorafe-ƙorafe da ɗaukaka ƙara- 12 April 2026
  • Babban taron jam'iyya-14 April 2026