Yadda adawa ke ƙara ƙazancewa tsakanin Boko Haram da Iswap
Asalin hoton, Boko Haram
Masu sharhi a Najeriya da kuma kafofin sada zumunta da ke da alaƙa da masu iƙirarin jihadi sun yaɗa wani sabon bidiyo da aka danganta da mayaƙan Boko Haram. Bidiyon ya yi alawadai da aƙidun ƙungiyar ISWAP'
Bidiyon mai tsawon minti 7 zuwa 13 an ce ya fito ne daga Jamatul Ahl al-Sunnah lil Da'awahti wal-Jihad.
Ana kyautata zaton ya fito daga wani ɓangare na ƙungiyar Bokon Haram da Bakura ke jagoranta, da ke da zama a Tafkin Chadi, kusa da iyakar Nijar da Chadi da Kamaru da kuma Najeriya.
Mutum ɗaya aka gani ya na jawabi a bidiyon - sai dai ba a gane ko wane ne ba. Ana zaton cewa shi ne mai magana da yawun ƙungiyar, maimakon shugabanta.
Mutumin ya yi magana sosai cikin harshen Larabci, inda ya yi ta kawo ayoyin al-Qur'ani. Sai dai bisa dukkan alamu ya na karanta jawabinsa ne daga wayar salula.
Masu sharhi kan ta'addanci a yammacin Afirka sun yi ta yaɗa bidiyon ranar 30 ga watan Maris. An wallafa hoton bidiyon a shafin intanet na Boko Haram.
Haka kuma, wasu kafofin sada zumunta na ƙungiyoyi masu iƙirarin jihadi sun yi ta yaɗa bidiyon, ciki har da shafuka da ke goyon bayan IS, waɗanda da alamu suka mayar da hankali kan bidiyon.
Bidiyon ya zaburar da tattaunawa kan masu jihadi game da bambance-bambancen aƙida da ke tsakanin IS da Boko Haram.
Mubaya'a ga Abu Umaima
Tun bayan mutuwar shugaban Boko Haram Abubakar Shekau a 2021 bayan faɗa da ISWAP, wasu rahotanni ke bayyana cewa shugaban ƙungiyar ɓangaren Bakura Ibrahim Bakura (wanda aka fi sani da Abu Umaima) ya kasance shugaban wasu ɓangarorin Boko Haram da dama. Bidiyo ya bayyana da Abu Umaima a matsayin shugaban ƙungiyar.
A can tsakiyar bidiyon an ga yadda duka mayaƙan suka zo suka "sabunta" mubaya'a ga Abu Umaima.
Mutumin da ya yi jawabi a cikin bidiyon ya yi gaisuwa ga "shugabannin" duka ɓangarorin ƙungiyar a larduna daban-daban ba tare da bayyana wace ƙungiya yake nufi ba.
Wannan na iya nufin wasu sassan Boko Haram da ke faɗin jihar Borno da kuma tsaunukan Mandura da ke lardin arewa mai nisa na ƙasar Kamaru.
Sai dai, hakan zai iya nufin wasu ƙungiyoyi da ke sassan arewacin Najeriya waɗanda sau tari ake alaƙantawa da Boko Haram.
Yin alawadai da ISWAP
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Bayan jawabi sosai a farkon bidiyon, mai magana a cikin faifen bidiyon ya karkatar da sakon shi zuwa ga ISWAP. A can cikin bidiyon ya kwatanta ISWAP da cewa suna zagon ƙasa ga dokokin addini.
IS ta sha kwatanta Boko Haram a matsayin masu tsattsauran ra'ayi saboda yadda suke harkokinsu.
A baya Boko Haram ta yi ƙaurin suna wajen kashe fararen hula - Musulmai da waɗanda ba Musulmi ba. Suna yin haka ne bisa tsarin aƙidunsu da suka nuna cewa duk wani wanda ba ya cikin ƙungiyar, to za a iya far masa kuma hakan ya halasta.
Mai magana a bidiyon ya ayyana cewa Boko Haram ba ta saduda ba wajen yin fito na fito da ISWAP ba.
Ya zargi ISWAP da zama tare da mushrikai cikin talakawa, mabiya azzalumai da kafurai. Ya ce irin waɗannan ne a ke kiran kansu Musulmai kawai "saboda suna azumi da sallah, yayin da suke zargin mu da kasancewa masu tsaurin ra'ayi."
Mutumin ya yi kira ga ISWAP da ta "tuba" da kuma "komawa kan turbar gaskiya", tare da gargaɗin cewa za su yi da-nasani idan suka gaza yin haka.
Faɗan bangaranci tsakanin ISWAP da Boko Haram
Kashe Shekau a 2021 ya kasance wani koma-baya ga Boko Haram a matsayinta na ƙungiya, inda ISWAP ta yi ƙoƙarin ɗaukar mayaƙanta zuwa cikinsu da kuma dubban mayaƙa da suka miƙa wuya ga hukumomi.
A cikin shekaru da suka gabata, akwai ƙungiyoyi da dama waɗanda aka alaƙanta da Boko Haram a faɗin arewa maso gabashin Najeriya da yankin Tafkin Chadi, inda wasu daga ciki ke kai ƙananan hare-hare, ta hanyar far wa ƙauyuka don satar abinci da kayan masarufi.
An kuma sha alaƙanta ƙungiyar da wasu manyan hare-hare da aka kai kan mutane da sojoji, ciki har da amfani da ƴanmata a matsayin masu ƙunar bakin-wake wajen kai hari.
An ɗorawa ɓangaren Bakura alhaki kan wasu hare-hare da aka kai wa sojojin Chadi a lardin Lac, ciki har da hare-haren da aka ruwaito sun kashe gomman sojoji a watan Maris ɗin 2020 da kuma Oktoban 2024.
An sha samun rahotannin ƙazamin faɗan ɓangaranci tsakanin ISWAP da mayaƙan Boko Haram.
Tafkin Chadi ya fuskanci ƙazamin faɗace-faɗace tsakanin ISWAP da ɓangaren Bakura, inda sau tari suke amfani da kwale-kwale wajen kai wa juna hari a tsibirai masu nisa.
An samu ƙaruwar tashe-tashen hankula a cikin watan Janairu.
A baya-bayan nan jaridar al-Naba mai alaƙa da IS ta miƙa ta'aziyya ga wani mayaƙin ISWAP da aka kashe a arangamar da suka yi da ɓangaren Bakura.
Wasu manyan al'amura guda biyu na baya-bayan nan da ake dangantawa da Boko Haram, su ne harin da aka kai ranar 4 ga watan Maris a garin Ngoshe na jihar Borno, inda aka kashe mutane da dama har da sojoji, tare da sace mutum kusan 30.
Sai kuma harin ƙunar baƙin-wake na ranar 16 ga Maris a Maiduguri babban birnin jihar, wanda ya janyo mutuwar mutane da dama da jikkata wasu.
Babban Labari
Labarai na musamman
Labaran da suka fi shahara
Babu karin bayanai