Babu tabbas kan makomar ƴan wasan Arsenal uku, Man U da Bayern na son Anderson

Asalin hoton, AFP via Getty Images
Manchester United za ta fuskanci gasa wajen neman dan wasan tsakiya na Nottingham Forest Elliot Anderson, mai shekaru 23, inda Bayern Munich za ta nemi dan wasan na Ingila. (Mail)
Dan wasan gefe na Aston Villa Morgan Rogers, mai shekaru 23, zai iya komawa wata kungiyar da za ta buga gasar kwallon kafa ta Zakarun Turai idan kungiyar Aston Villa ta kasa samun gurbin shiga gasar a kaka mai zuwa. (Talksport)
Dan wasan gefe na Arsenal Gabriel Martinelli, mai shekaru 24, yana fuskantar rashin tabbas a kungiyar, shi da dan wasan baya na hagu na Ingila Myles Lewis-Skelly, mai shekaru 19, da kuma dan wasan gefe na Ingila Ethan Nwaneri mai shekaru 18. (Times)
AC Milan da Inter Milan na son dan wasan baya na Manchester City Nathan Ake dan kasar Netherlands, mai shekaru 31, wanda ba ya samun damar buga wasa a kungiyar. (Caughtoffside)
Arsenal ba ta da niyyar barin ɗan wasan baya na Italiya mai shekaru 23 Riccardo Calafiori ya bar ƙungiyar a wannan bazarar duk da yadda kungiyoyin Seria A ke ta nuna sha'awarsu ya daukarsa. (Teamtalk)
Liverpool na neman yarjejeniyar da za ta iya siyan ɗan wasan tsakiya na Real Madrid da Faransa Eduardo Camavinga, mai shekaru 23, a wannan bazarar. (Football Insider)
Juventus na jiran tayi kan dan wasanta Jonathan David, mai shekaru 26, yayin da West Ham, da Tottenham da Nottingham Forest ke nuna sha'awarsu ta daukarsa. (Tuttosport)
Paris St-Germain ba ta da wani shiri na sayar da ɗan wasan gefe na Georgia mai shekaru 25 Khvicha Kvaratskhelia ga Arsenal. (Fabrizio Romano)
Kyaftin ɗin Roma Lorenzo Pellegrini yana cikin waɗanda Juventus ke nema, yayin da ɗan wasan tsakiyar na Italiya mai shekaru 29 zai ƙare kwangilarsa a Giallorossi a ƙarshen kakar wasa. (Gazzetta dello Sport)











