Ba za mu bari a ƙwace mana ADC ba - Nafi'u Gombe

Asalin hoton, FB/Nafi'u Bala

Lokacin karatu: Minti 5

Yayin da ake ci gaba da ce-ce-ku-ce kan zargin maƙarƙashiya da kan halin da jam'iyyar hamayya ta ADC a Najeriya, ke ciki, mutumin da ake ja-in-ja da shi a kan shugabancinta Nafi'u Bala Gombe, ya bayyana wa BBC dalilinsa na bijera wa jagorancin David Mark a jam'iyyar.

Jam'iyyar ta ADCn da ta ƙunshi manyan ƴan hamayya a Najeriya dai ta shiga ruɗani ne bayan hukumar zaɓen ƙasar, INEC, ta cire sunan David Mark a matsayin shugaban jam'iyyar daga shafinta na intanet, saboda wani hukuncin kotu da ya shafi Nafiun.

Nafiun Bala Gombe ya ce har yanzu shi ne halattaccen shugaban jam'iyyar ta ADC, inda ya ce raina shekarunsa da aka yi, ya sa shi tashi tsaye wajen ganin ya ƙwatar wa kansa haƙki.

"Bayan da suka shigo ADC, sai suka bayyana kansu a matsayin shugabanninta, don su nuna cewar mu ne a ƙasa, saboda ni yaro ne, Allah ne Ya ba ni muƙamin nan na mulkin ADC, ba za su iya bi na ba, shi ya sa suka ayyana kansu a matsayin shugabanni. shi ya sa ni ma na yi tsayin daka, don tabbatar wa da duniya cewar ɗan talaka ma ɗa ne, in ba za ku bi mu ba to kuwa ba za ku zauna a ADC ba, in ji Nafi'u Bala.

Ya ce tabbas ya fito a wasu daga cikin hotunan bidiyo da aka yaɗa a kafofin sada zumunta.

Sai dai ya ce washegarin ranar da aka gudanar da wannan taro na shugabancin su David Mark ɗin, shi ma ya kira taron manema labarai ya barranta kansa da su, sannan a wannan makon ya shigar da ƙara kotu.

Ya kuma ce ba zai yiwu a ce, "a ranar da ka nuna sha'awar shiga jam'iyya kuma ka ayyana kanka a matsayin shugaba ba. Sun nuna cewar za su taka mu, har suna nuni da cewar sun riƙe muƙamai suna da iko, suna da kudi a hannunsu, shi ya sa muka ce to bari mu ƙalubalance su, in ji shi.

Ya kuma musanta zargin da wasu ke yi masa cewar rashin samun shugabancin jam'iyyar, da zargin karɓar kuɗi don haifar da rikici a jam'iyyar.

"Maganar shaci-fadi ce, ni ban san Ishaku Abbo ba, a ranar da suka shigo jam'iyyar ADC na fara ganinsa, kuma a lokacin na fada masa cewa, irin mutanen da suka shigo jam'iyyar su kuma ce ranar da suka shigo su yi kaka-gida, a jam'iyyar, a gaskiya hakan ya saɓa wa dimokuraɗiyya" a cewar Nafi'u Bala.

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Tuni dai wasu daga cikin gaggan ƴan jam'iyyar irin su tsohon mataimakin shugaban Najeirya Atiku Abubakar da tsohon gwamnan Kano, Rabi'u Musa Kwankwaso suka fara kiraye-kiraye da cewar ya kamata Nafi'u Balan ya bayar da kai bori ya hau.

Sai dai ya ce. "ina da labari su ne suka je suka yi mitin cewar za a taka ni, ina da shekaru kusan 50 a duniya, ban ga dalilin da zai sa in bari wani mutum da ke da shekaru 70 ko 80 ba ya ce zai taka ni, yanzu ruwa ne ya ƙare wa ɗan kada shi ya sa suke ta kuka" in ji Nafi'u.

Sai dai ya ce ƙofarsu a buɗe take a zauna a tattauna da ɓanagren shugabanicin David Mark, amma sai ya yi rajista da banagren shugabancinsa, kuma za su yi musu adalci tare da biya musu buƙatunsu.

Tun dai bayan da hukumar zaɓen Najeriya Inec ta cire sunan Sanata David Mark da sauran ƴan kwamitin zartarwar jam'iyyar ta ADC daga shafinta na intanet, jam'iyyar ta ADC ta yi zargin cewar akwai wasu mutane a cikin gwamnatin Bola Ahmed Tinubu, da jam'iyyar APC da hannu kan rikicin da suka tsinci kansu.

Sai dai fadar shugaban na Najeriyar ta yi watsi da zarge-zargen, inda ta bayyana su da marassa tushe balle makama.

Rikicin shugabancin jam'iyyar ADC ya kunno kai ne a watan Yulin 2025 lokacin da shugabannin jam'iyyar suka yi murabus, kuma David Mark ya zamo sabon shugaba na riƙon-ƙwarya, inda aka zaɓi sauran ƴan kwamitin zartarwa babu hamayya.

Sai dai kuma tsohon mataimakin shugaban jam'iyyar, Nafi'u Gombe ya ƙalubalanci zaɓen inda ya dage cewa dole ne a samar da shugabanci ta hanyar da kundin tsarin mulkin jam'iyyar ya tsara.

Ya kuma garzaya kotu yana neman ta ayyana shi a matsayin shugaban ADC saboda a lokacin da shugabanninta suka yi murabus shi kadai ya rage, kuma a matsayin mataimakin shugaba mai barin gado, shi kundin mulki ya bai wa damar ɗarewa shugabancin kai tsaye a cewarsa.

Wane ne Nafiu Bala Gombe?

An haifi Nafiu Bala Gombe a shekarar 1986 a mazaɓar Nassarawo da ke ƙaramar hukumar Gombe ta jihar Gombe a arewa maso gabashin Najeriya.

Ko da yake babu cikakken bayani kan yarintarsa da kuma karatunsa, amma maƙotansa a unguwar Nassarawo, sun ce Nafi'u ya yi karatunsa a makarantar firamare da ƙaramar sakandare ta Nassarawo daga bisani kuma ya zarce kwalejin fasaha ta Government Day Technical College (Vocatational) Gombe, inda ya kammala sakandire a 2010.

Daga nan ne Nafi'u ya zarce zuwa kwalejin nazarin Shari'a ta AD Rufai College for Legal studies da ke Misau a jihar Bauchi, inda ya samu ƙaramar difloma a fannin shari'a a 2012.

Kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito, yawanci Nafiu ya yi aiki ne a matsayin mai aikin sa-kai a cibiyoyin shari'a masu zaman kansu a Gombe, kafin ya tsunduma harkar siyasa dumu-dumu inda ya zama mamba a jam'iyyar DPP, wadda tsohon gwamnan jihar Sokoto Attahiru Dalhatu Bafarawa ya kafa.

Bayan zama na takaitaccen lokaci da ya yi a jam'iyyar, Nafi'u Bala ya koma jam'iyyar PRP, inda daga nan ya koma jam'iyyar ADC ta yanzu.

A jam'iyyar ADC, matashin ɗan siyasar ya yi takarar kujerar gwamnan jihar Gombe a zaɓen 2023, amma ya sha kaye a hannun gwamnan jihar mai ci yanzu, Muhammad Inuwa Yahaya na jam'iyyar APC.

Wani jigo a jam'iyyar ADC a jihar Gombe, Mustapha Hadi ya shaida wa jaridar cewa Nafiu Bala ya yi suna a siyasar jihar a lokacin da ya yi takarar gwamnan jihar Gombe a zaɓen 2023, kuma daga bisani ya ƙalubalanci sakamakon zaɓen a kotun sauraren ƙararrakin zaɓe.

Ya ce daɗewar da Nafi'u Bala ya yi yana shari'ar zaɓen ce ta fito da sunansa a idon jama'a, har ya samu gurbin zama a jam'iyyar ADC a matakin ƙasa.