Erling Haaland shine gwarzon dan kwallon Agusta a Bundesliga
Asalin hoton, Getty Images
Dan kwallon Borussia Dortmund Erling Haaland shine gwarzon dan kwallon kafa a gasar Bundesliga na watan Agusta.
An fara gasar Bundesliga ta bana ranar 13 ga watan Agustan 2021, inda Borussia Dortmund ta fara da doke Eintracht Frankfurt da ci 5-2 ranar 14 ga watan Agustan 2021.
A karawar ce Haaland ya ci biyu ya kuma bayar da biyu aka zura a ragar Eintracht Frankfurt, sai kuma Dortmund ta yi rashin nasara da ci 2-1 a gidan Freiburg ranar 21 ga watan Agusta.
Wasan mako na uku kuwa ranar 27 ga watan Agusta, Dortmund ta yi nasara a kan Hoffenheim da ci 3-2, inda Haaland ya ci kwallo na uku a fafatawar.
Cikin watan na Agusta ya ci kwallo uku kenan ya kuma bayar da biyu aka zura a raga da ta kai ya zama gwarzon dan kwallon kafa a watan Agusta a gasar ta Jamus ta Bundesliga.
Haaland shine ya ci wa Dortmund kwallo na biyu da suka je suka ci Besiktas 2-1 a wasan farko na cikin rukuni a gasar Champions League ranar Laraba.
Kawo yanzu an buga karawa hudu a kakar bana a Bundesliga, inda dan kwallon Bayern Munich, Robert Lewandowski ke mataki na daya da kwallo shida a raga, sai Haaland na biyu mai guda biyar a raga.
Ranar 19 ga watan Satumba za a buga wasannin mako na biyar a Bundesliga, inda Borussia Dortmund za ta karbi bakuncin Union Berlin, ita kuwa Bayern Munich za ta yi wa Bochum masauki ranar 18 ga watan Satumba.
Babban Labari
Labarai na musamman
Labaran da suka fi shahara
Babu karin bayanai