'Nigeria ba ta da tsarin tattalin arziki'

Mataimakin shugaban Najeriya, Prof. Yemi Osinbajo ne dai yake jagorantar majalisar tattalin arzikin Najeriya.
Bayanan hoto, Mataimakin shugaban Najeriya, Prof. Yemi Osinbajo ne dai yake jagorantar majalisar tattalin arzikin Najeriya.

Masana tattalin arziki a Najeriya sun ce kasar ba ta da tsarin tattalin arzikin kasa na gajere da matsakaici da kuma dogon zango.

Dr. Nazifi, malami ne a jami'ar Abuja ya alakanta matsalolin da kasar take fuskanta sakamakon rashin tsarin da kasar take da shi.

Sai dai kuma masanin ya shawarci gwamnatin kasar da ta kira masanan a tsara sabon kundin tsarin tattalin arzikin kasar.

A ranar Litinin din nan ne dai Majalisar Tattalin Arzikin Najeriyar ta za ta fara wani taro na kwanaki biyu da nufin tattaunawa a kan matakan da ya kamata gwamnatocin tarayya da jihohi su dauka don zaburar da tattalin arzikin su.

Alhakin majalisar dai,shi ne bai wa shugaban kasa shawara a kan al'amuran da suka shafi tattalin arzikin kasa.

Mataimakin shugaban kasaR, Prof. Yemi Osinbajo ne yake jagoranta majalisar, ta kuma kunshi gwamnonin jihohin kasar 36.