Hotuna: Rayuwa a garin Shasha bayan rikicin Hausawa da Yarbawa

BBC Hausa ta kai ziyara garin Shasha na jihar Oyo inda aka yi rikicin ƙabiolanci tsakanin Hausawa da Yrabawa a makon da ya gabata, kuma abokin aikinmu Yusuf Yakasai ya ɗauko mana waɗannan hotunan na halin da garin ke ciki a yanzu haka bayan lafawar rikicin.

Bayanan hoto, Wasu mata Hausawa na tsaye suna zantawa, kwana uku bayan lafawar rikicin da ya yi sanadin mutuwar Hausawa fiye da 10 a garin Shasha na jihar Oyo.
Bayanan hoto, Nan kuma wata daba ce ta samari ake ci gaba da hada-daha bayan lafawar faɗan.
Bayanan hoto, Mafi yawan ƴan kasuwa Hausawa daga arewa na sayar da kayan gwari a kasuwar ta garin Shasha, amma an tafka asarar dukiya sakamakon faɗan.
Bayanan hoto, Abokin aikinmu Yusuf Yakasai ya ce kasuwar ta zama tamkar bola saboda kayayyakin da aka lalata.
Bayanan hoto, Mata da yara da dama na samun mafaka a yanzu haka a wasu wuraren da suke da yaƙinin suna cikin aminci a garin.
Bayanan hoto, Wasu kuwa tuni suka fara loda kayayyakinsu a motoci don barin yankin gaba ɗaya.
Bayanan hoto, Mutane musamman ƴan kasuwar na ta ƙirga asarar da suka tafka.
Bayanan hoto, Bayan kwanaki kaɗan da faruwar rikicin wasu har sun fara samun sukunin dafa abinci a sansanonin ƴan gudun hijira.