Chelsea na son ɗauko Henderson, Arsenal na da ƙwarin gwiwa kan Aubameyang

Chelsea ta shirya bai wa golan Ingila Dean Henderson £170,000 duk mako a yunkurin da take yi na dauko dan wasan mai shekara 23, wanda ke zaman aro a Sheffield United, domin ya bar Manchester United. (Manchester Evening News)

Henderson zai sake tafiya zaman aro har sai ya samu tabbaci daga Manchester United cewa za a ba shi damar fafatawa da golan Sufaniya David de Gea, mai shekara 29, wanda shi ne zabin farko na kungiyar. (Times - subscription required)

Kazalika Chelsea za ta yi yunkurin dauko golan Barcelona da Jamus Germany Marc-Andre ter Stegen, mai shekara 28, kuma ta shirya bayar da dan wasan Sufaniya Kepa Arrizabalaga, mai shekara 25, a wani bangare na yarjejeniyar. (Mundo Deportivo, via Mail)

Kocin Arsenal Mikel Arteta yana da "kwarin gwiwa" cewa dan wasan Gabon Pierre-Emerick Aubameyang, mai shekara 31, zai sabunta zamansa a kungiyar. (Independent)

Mutumin da ya mallaki Leeds United Andrea Radrizzani ya ce "za mu ga yadda za a yi" a kan yiwuwar dauko dan wasan Uruguay mai shekara 33 Edinson Cavani bayan kungiyar ta samu ci gaba a gasar Firimiya. Cavani ya bar Paris St-Germain a bazarar nan bayan kwangilarsa ta kare. (Sky Sports Italia, via Football Italia)

Za a ci gaba da rike kocin Newcastle United Steve Bruce idan Henry Mauriss, wanda ke gogayya da kamfanin Saudiyya a yunkurin sayen kungiyar, ya yi nasarar mallakarta. (Telegraph - subscription required)

Mai yiwuwa dan wasan Aston Villa da Tanzania Mbwana Samatta, mai shekara 27, zai kama gabansa zuwa Fenerbahce bayan ya gaza taka rawar gani tun da ya koma Villa Park a watan Janairu. (Takvim via Sport Witness)

Everton na sha'awar dauko dan wasan Southampton dan kasar Denmark Pierre-Emile Hojbjerg, mai shekara 24, amma ya shaida wa kungiyar cewa ya gwammace tafiya Tottenham. (Liverpool Echo)

Golan Paris St-Germain Alphonse Areola, mai shekara 27, wanda ke zaman aro a Real Madrid, yana iya kama hanyarsa ta tafiya kungiyar da ke Ingila bayan iyalan dan wasan na Faransa sun sayi gida a London. (Marca)